3️⃣2️⃣

1.5K 134 5
                                    



A kofar gida nasauka,mai gadi yaban kudi nabiya,nashiga ciki nadauko masa,Anty nasamu parlor tana kallo,ta kalleni tace har kindawo sharp sharp haka,nai murmushi nace matarsace taketa nemansa shyasa yadawo dani,tace jarababbiya mtsww mata matsala garemu wlhy,haka kawae ayita takurawa namiji,na sosa kai kawae nawuce ciki,a raina nace wai ni xaaraina ma hankali,kwanciyata nayi ina shafa cikina nafara bacci.......

Washegari haka mukaje aiki,Ina fargabar kar Alhaji audi yaxo kuma har dare shiru bexoba,da daddare Anty tace mutuminnaki yau baxexo bane,nace qila matsalane a gidannasa,kuma ni gashi ba wayaba bare na kirasa,tace hakane amma xexo manasani,nace aikam,ban rufe baki ba kuwa se gashi yafado gidan ko sallama babu,anty tai sauri ta mike tace Alhaji lafiya?yace ni xaacima mutunci?wannan yarinyar ke kika koyamata abunda xataminko?anty ta kalleni duk hnkalina yatashi nace dan Allah kiyi hakuri dama wlhy bnjin dadine shyasa namasa hakan,ranta a bace tace mekikamasa maryam?nayi shiru,shikam yabata labari tas,sannan yace wlhy dakyr nashawo kan abun nabawa me gadina kudi da iyayenta sukaxo yace ae shi besan motar a bude takeba,yadaiga budurwar tashiga tadauko waya tashiga cikin gidanne,dakyr fa nasamu na lallabata da iyayenta komi yawuce.......

Ta kalleni tace kin kyauta,tace amma wlhy ni babu yarinyarda xataxqunamin a gida baxatabi abunda nikeso ba,in abunda kikeso xakiyi meyahanaki xama gaban iyayenki?ko kikama gida kixauna kiriqa abunda kikeso?wlhy dole kibi umarnina imdai xaki xauna gidana,ta kalla alhaji,ynxu ya kakeso ayi yace ni kudinakawae xaabiyani,da kudinda nasa akaturomaki jia da safe duk ki tattaramin kudina inkara gaba,tace Aaaah gskia Alhaji ae baxaae hakaba,kasan bamutaba samun matsala ba,dole tabika,ko shekara xatai gurinka nidai tabika Kurum,yace bayan taga gidana,wayasan mexatamin gobe?tace ae wlhy uban ta yayi kadan,bata isaba wlhy,se insa a batar da ita wlhy,ta juyo ya kalleni tace ke kuma tattaro kibishi,sannan inji ance kinyi wani abun kigani,wlh nidake ne,sanann Alhaji duk abunda tayi kakirani kawae,sannan kasa tsaro sosae a kanta,hnkalinane yatashi danni nasan nayi kuskure a rayuwata amma nayi nadama kuma baxan bari inkara aikata hakanba,nace to Anty kiyi hakuri,ciki nashiga nahada kaya a akwati duk abunda nasan nawa dawasu cikin wanda Alhaji yasiyamun nafito nace nashirya muje,tace yauwa kokefa......

Rike hannuna yayi,nayi sauri xan kwace naga tana kallona,haka nadaure muka mata sallama mukafita,tsayawa yai xebude mota,yasaki hannuna,nikam naja akwatina da gudu,biyoni yai da gudu dashi da mai gadinmu,gudu nike sosae naxo kwana naji wata mota tayi sama dani,dishi dishi nike gani,naga Alhaji da maigadi sunkoma a guje........

Bude idona nayi naganni cikin asibiti,kallon dakin nikeyi,naji kaina yamin wani irin nauyi,nadafe naji annannadamin bandage,so nike intashi amma nakasa naji gabadaya jikina namin ciwo especially cikina,dayake wani azaban ciwo,wata matace taxo kusadani tariqe hannuna tace ya jikin,kinajin wani abu?nace cikina ciwo tace sannu ko,sannu kinji,wata nurse ce ta matso tayi seaking permission wai xatamin wasu basic examinations,dagamata kai kawai nayi,don namakasa magana,idona harhaska da touch,tace kinajina?ya sunanki nace maryam....tace okay,tambayoyi tacigaba damun taga naki amsata,haka tawuce,rufe idona nayi se kawae naga hoton baby yai appearing a idona,cute,round face with black hair.........

Kwanana biyu a asibitin kullum suna kuladani,amma nabar ma kowa magana cikinsu,ranar matar datakawoni tadawo,tabani abinci naci,tace dan Allah kiyi hakuri maryam,bansan yaxanafara baki hakuri ba,shyasa naso kikiramin mijinki mu masa bayani,nace karkidamu ko ma miye kifadamin,tace kinyi miscarriage,gabanane yafadi don namarasa gane miye miscarriage,se a hnkali komi kedawomin,wato cikina yaxube kenan,haba no wonder,tace Dan Allah kiyi hakuri wllhy ranar kirana akai ciwon mamata yatashi shyasa nafito hankalina tashe,kawae naga kinfado titi,ga wasu mutane na biyoki,kiyi hakuri,tace suwaye su nace bansansuba,kayana fa?tace suna mota,nadaukarmaki,shafa cikina nayi Ina godewa Allah cikin raina,itakam wani tausayi nabata tace Dan Allah kiyi hakuri ba da gangan bane wlhy,nace karki damu bakomi.......

#vote
#comment
#share
    

                Your's arabiya🦋

ABINDA KA SHUKA(COMPLETED)Where stories live. Discover now