2️⃣1️⃣

1.5K 135 7
                                    



Baba yace maryam karkiyi judging mutum by the basis of his look,tace bawai looks bane kadai baba,dressing,choices,personality kuma kaga kanshi kuwa ko gashi fa babu...gashi yana magana da tsoro tsoro sekace ance xaa cinyeshi,yace maryam kawae kije kiyi tunani and then pray,kibashi lokaci

Babu wani lokacifa baba nidai banso baxanyiba kawae,tafadi tareda kunna data tashiga Twitter,tsayawa kallonta kawae baban yayi yarasa mexeyi,sega message yashigo wayanta daga mimi "xaki iya riqa tafiya gida da wuri har xuwa lkcinda kikeso,nafadama su BoBo cewa kunada some financial issues ne,duk sun tausayamaki,kiyi hakuri "tsaki tayi tace wlhy dole taci uwar mimi xatanunamata ita ba saar ta bace.....ynxu xatasa kowa ya rainata a skul,masu tsoron kallon idontama ynxu xasufara kallo,masu tsoron mata maganama ynxu suma xasu fara,sbda anga iyayenta xasu talauce,noooo baxanbari haka yafarubah,nice fa maryam usman who doesn't give up without a fight

Baba,tadago taga yanakokarin fita parlorn jikinshi duk yayi sanyi,setaga yabata tausayi tasakecewa baba yace ummm,tace nayarda xan aureshi........murmushi yai yace nagode,nagode diyata Allah yamaki Albarka tace Ameeen tareda wucewa ciki,murmushi yai yakoma kusada mummy yazauna...

Bayan sati daya sega iyayen muhsin sunxo sunkawo kudin gaisuwa da kayan sa rana,akasa rana wata biyu,baban muhsinne yabiya bashin da akebin babana gabadaya,ranar baba kwana yai farinciki,yau ce ranar da mukagama exams ana gamawa akasa date din graduation,next week Saturday munata shirye shirye,muhsin ya aikomin da kudi masu yawa nayi ordering rigar da xansa,naje saloon nasha lalle harda gyaran jiki akamin,sannan yamin sovereigners da xanraba gurin graduation seda ya tabbatar anmin komi ynda nikeso,ranar tunda safe narigasu tafiya so sudaga baya xasuxo,anyi angama lafiya anbamu gifts sannan mukai party,se ga call dinsa na shigowa wayana,yana kara tayani murna,sannan brothernshi xexo mugaisa shima xexo daga baya nace ba matsala

Mungama abunuwanmu har anfara watsewa sega call dinsa,namasa kwatance yaxo,Ina xaune kan wani kujera a can gefe namasa bayanin inda nike,daga nesa ta hangoshi yayi parking,ya fito yana kokarin cire sun glasses dinshi,idonta yakai kan silky black hair dinshi,dark brown eyes,red lips da kuma blue bottom up shirt dayai fitting muscular torso dinshi tace "wow"ya maida sun glasses din cikin pocket din jeans dinshi,yasa hannu yana burkita gashin kanshi yana duba ta Ina xeganta,idonshi ne yasauka kanta tamatso tanamasa wani friendly smile,se yakira numbernta yaga tana ringing a hannunta tana tahowa inda yake,shima murmushin yakeyi ta karaso tareda mai sallama,yace "BELLA"tace Aa sunana maryam,yace nasani amma ni bella xanriga cemaki tayi murmushi tace me hakan ke nufi yace bella means beautiful in italian tace ohhh tanata blushing,tace kaikuma fa yace bilal,bilal Abdulkarim tace ohh kai brothern muhsinne kenan?yace yes his one and only brother bah,it's nice meeting you tace nice to meet you too,ganin kawae muhsin mukai kusadamu yace soo kaga amaryartawa ko yace ey yaya she's stunning,tareda binta dawani irin kallo

Sun danyi fira kadan bilal yamusu sallama yawuce,muhsin yace muje yawo mana tace no kaina namin ciwo gida xantafi,yace olryt take care tace bye,tareda wucewa tashiga mota tatafi........


Yayi kadan ko? Sorry 😐 pls pray for my aunt Allah yamata rasuwa

#vote
#comment
#share
           
                                  Arabiya❤️

ABINDA KA SHUKA(COMPLETED)Where stories live. Discover now