3️⃣1️⃣

1.8K 125 4
                                    


Tafiya nike narasa Ina zandosa naga mai napep natara nace muje muna tafiya,mukashiga wata unguwa naga wani restaurant cike da mutane anashige da fita,nace yatsaya nabiyasa,nashiga ciki nace inason magana da mai gurin akamin iso da ita,nafadamata aiki nike bukata,tace ita ae maaikata basumata yawa,so xatarika biyana 10 thousand per month nace to nagode,tace a gidanta xanriqa kwana sbda ita duk masu mata aiki gidanta suke kwana nace ba matsala,takirawo wata mai suna karime tace takaini gida inhuta,gobe se infara fitowa aikin,tadaukarmin ledan kayana kam mukatafi gidan......

Gidane madai daici babban falo,da dakuna kwara uku,daki daya na mai gidanne,biyu kuma namune,ma'aikatanta,kayan tajeramin cikin wadrobe sannan tabani abinci naci,nayi wanka nayi sallah nayi kwanciyata.......

Se 8 din dare sukadawo,Ina falo muna kallo nida karime,yanmata kusan takwas duk suka shigo mukagaisa,suka shiga cikin daki,bayan hour daya naga sunfito duk sunci kwalliya kamar basu ba,a raina nace ko biki xasuje ne?se naga sunama anty sallama daya bayan daya,itakuma tanacewa akawo mai tsoka,ashe samarinsune ke jiransu waje,nikam dai inata kallon ikon Allah,natashi namasu seda safe naje daki nayi shafai da wutiri nayi kwanciyata.......

Washegari
Tun asuba mukatashi mukai sallah,mukafara shirin tafiya gidan abincin,yanmatan naga suna kwalliya kamar ba aiki xasuba,nidai nasaka dogon hijabina,Ina jira sugama mutafi,karime ce takaraso kusadani tace ke baxaki shiryabane?nace mata na shirya ae,duk suka juyo suka kalleni suka kwashe da dariya,nikam takaici sukabani don banga abin dariya a jikina ba......

Fitowa mukai mukasami anty a parlor,tace oya mutafi,wata a cikinsu tace anty bakiga abinda ke jikintabane,Anty ta harareta tace wannan ba matsalarki bace,ta rikemin hannu tace muje kinji diyata,nayi murmushi nabita,haka mukaje mukai aiki mukadawo,kamar jia naga yauma sunyi kwalliyarsu sunfice,nace su kam ko yaushe xasudawo oho,fira muke da anty har naji bacci natashi natafi daki,Ina mamakin kirkin matar....

Bayan kwana uku

Haka muke zuwa aiki kullum mudawo nikadai akebari a gida da daddare se anty,washegari natashi nashirya,nafito se anty ta shigardani dakinta,tabani wasu riga da skirt na atamfa sababbi da mayafi tace nasa,nacemata Aa nafijin dadin hijab,tace ae kawae tabarni insabane amma ita gskia baasamata hijab gurin aiki,ba don nasoba na karba,naje nasa,akabani powder nashafa sunata yabon kyau na,nikam gabadaya I'm not comfortable,haka mukaje aikin,washegari haka takara bani wasu kayan nasa,mukaje,muna tsaka da aiki wani customernta Alhaji audi yazo tanata murnar ganinsa,shikuma se kallona yake,kallon ya isheni na tashi na shige ciki,yace hajja wannan fa,tace sabon hannu ce,kafin inbaka ita sekabiya kudi masu yawan gaske,yace na sati ma zakiban,ko na wata kinga se intafi dubai da ita in shana,tace bakada matsala inji alert kawae yace angama,wayarsa yadauki yakira yaron shagonsa yace aje asama acct din hajian kudi,sega alert kuwa,guda tayi tafara rawa tace lallai Alhaji dagaske kake,babbar harka,to kabani xuwa gobe insamu in lallabata yace angama kardai a wuce kwana biyu don baxan iya hakuri ba tace toh.......

Ranar anty yini tayi cikin farinciki,don tadade batasamu makudan kudi hakaba,muka koma gida tun yamma tafara bani wasu magunguna wai na basir ne talura basir na damuna,haka nasha ba don naso ba,Ina shiga daki kam na amayar dashi......ranar da daddare tace inshirya xanyi bako,nace wani irin bako kuma,tacemin wani kaninta kesona,itakuma tanaso nayi aure inda xanji dadi shyasa ma ta amince masa yaxo mu daidaita wai amma in bemun ba infadamata kawae,nace to haka nashirya yaxo naje,Ina zuwa naga Alhajin daxu takaici yakamani,nace amma matarnan ya tarainani,muka gaisa yace shopping xamuje nace to nabisa mukatafi wani mall,yaita lodarmin kaya,su jaka ,takalma da kayan makeup,kayan hargani nayi sunyi yawa,yasiyamun su chocolates kuma kala kala,nikam nagaji bacci ma naikeji nacemasa,mukatafi gida,haka yasaukeni yasa mai gadinmu yashigarmin da kayan,sannan yabanu kudi inriqe a hannuna,kin karba nayi,ya ajiye yatafi,haka nadauka nashiga ciki,anty taita santin kayan,tace maryam kinga harkar arziki ko nace ey ga kudi ma yabani,tace inriqe abuna,nace na ajiye cikin kayana kam,itakuma ta dauki kayan ya tayani jerawa a dakinmu........

Washegari haka yaxo yadaukeni,tace xamufita nace toh,hotel naga munje,ya kama daki,segashi ankirasa a waya yacewai emergency ne xeje yadawo,nacemasa baxan iya xama nikadai ba,sede mutafi tare yace to,haka mukatafi wani gida,lura nayi gidansane,yace ko anyi knocking glass karnabude,xe bama matarsa sako ne,nace to,yana shiga gidan nafito nabi bayansa,Ina shiga naga ya marairaice yanama matar magana,na shiga na zauna,ta kalleni tace kekumafa?daga Ina?shikam iya tashin hnkali,hnkalinsa yatashi nace daukoni yai wai muje hotel,tace hotel kuyime?nace abinda akeyi mana,aiko tasa salati,shikuma yafara masifa kee,a ina kikasanni,uban wa ya aikoki kimin sharri,wlhy my love makiya ne,wanda basusan ganina taredake,yajuyo kaina yace kekuma xanci ubanki yau,inga ubanda yatsaya maki,wayarsa na mika masa nace ga wayarka Ina mota,matar kasa magana tayi tabini da kallo kawai,tace wlhy yau seka sakeni,ashe abunda akefadi gskiane,karfe ya dauko yabiyoni,nikam nasa gudu a titin,na tare me napep na hau..........

#vote
#comment
#share
    

                Your's arabiya🦋

ABINDA KA SHUKA(COMPLETED)Where stories live. Discover now