*RUBUTACCIYAR KADDARA*
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
( *home of expert and perfect writers)*💡*SOPHIE GALADANCHI* ✍🏼
_Assalamu alaikum_
_ina bawa masoya littafin baya da kura da labarin zara'u hakuri akan rashin karasa su da banyi ba hakan ya faru ne saboda wani dalili kuma ina muku albishir na samun wannan labarin daga farko har zuwa karshen idan kun bani hadin kai, nagode__Da sunan Allah mai rahama mai jink'ai_
(1)
shuru tayi tana kallon magajiya dake kwance tayi wani irin bak'i da rama, addua take tana rokon Allah a zuciyarta ya bawa wannan baiwa tasa lafiya ya tashi kafad'unta.
Motsin shigowa dakin yasa ta daga kanta tana kallon kofar, y'ar fara ce ta shiga tana yatsina fuska ta kalli Indo dake zaune a gefen magajiya da mafici a hannunta tace, "jikin dai har yanzu? To Allah ya kawo sauki".
" ameen" indo ta amsa tana kallon magajiya cike da tausayi.
"Nace wankin dana kawo sai yaushe zan samu? naga kayan sun kwana biyu". Maganar yar fara ta katse mata tunani.
Ajiyar Zuciya ta sauke sannan tace " Safiyyah nake jira ta dawo, taje siyan sabulu insha Allahu gobe zata kawo miki idan an goge".
Labulen dakin ta saki ta wuce ba tareda ta kuma yin magana ba.
Ta nanan zaune Safiyyah ta shigo da sallama ta zauna a gaban indo tace "Anty ga sabulun, shagon lado a rufe sai da na kai titi na samu".
Indo ta karbi ledar ta ajiye gefenta tana cewa " shikenan nagode, amma dai Bana so kina tsallaka titin nan".
Murmushi kawai Safiyyah tayi sannan ta kalli magajiya tace "Anty Dan Allah mana ki maida goggo asibiti mana, kalli fa yau ko idonta bata bude ba" ta karasa maganar cikeda tausayi.
Murmushi indo tayi tace "Safiyyah kenan, asibitin ai su suka ce mu dawo gida koda mun koma ma ba karbarta zasu yi ba kedai kiyi mata addu'a insha Allahu tunda tana shan magunguna zata samu lafiya".
A hankali Safiyyah tace " to Allah ya bata lafiya, Anty kuma wankin can fa yayi yawa ki tashi mu fara".
Kallonta tayi tana yaba kokarin ta sannan tace " kije dai ki Dan taba karatu tunda kun kusa fara jarrabawa ni zanyi kokari na kammala wankin".
Tashi tayi ta nufi dakin su tana amsawa da to.
Tunda ta fara wanki sai karfe biyu ta gama, shima dan Safiyyah ta kama mata shanya ne data ga wankin yayi yawa.
Kwana uku kenan jikin magajiya yaki yin sauki, abin ma ya fara tsorata indo Dan jikinta duk wasu kuraje sun feso itama kanta seta kai Zuciya nesa take iya kallonta, tana mamakin ace magajiya batada kowa ko wasu dangi da zasu taimaka da jinyarta, ita dai bazata manta alkhairin magajiya ba agareta Dan haka bazata bari ta wulakanta ba, zatayi duk iya kokarinta da yardar Allah.
Kudin hannunta take kallo, lokacin biyan haya baiyi ba wannan kudin ma bazai isa siyan maganin ba domin wasu daga cikin magungunan ma tun shekaranjiya sun kare Dan haka take tunanin karasawa Suby wankinta a yau din nan.
Sauke ajiyar Zuciya tayi tana karara ganin girman ubangiji, duk dukiyar da magajiya ta Tara ta kare wajen Neman magani amma ciwo sai karuwa yake.
Daga waje take jiyo tarin magajiya da sauri ta shiga dakin, ta dauko ruwa ta bata a baki tana jera mata sannu, tana sauke kofin daga bakinta ruwan suka dawo, daga nan kuma sai shak'uwa tayi yakai sau goma sai kuma taji shuru, ido ta fiddo waje tana fadin, "innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un", ganin idon magajiya ya kafe asama hakan ya tabbatar mata da rai yayi halinsa, kuka ta fashe dashi tana fadin, " Allah yajikanki, Allah ya yafe miki", Safiyyah ta fito sakamakon jin kukan mahaifiyarta taga abin da yake faruwa itama ta sa kuka, dakyar indo ta yi karfin hali ta fita zuwa Inda su yar fara ta fada mata halin da ake ciki, a take gidan ya karad'e da kukan matan gidan, kafin azahar an kaita makwancinta.
Kwana uku da rasuwar magajiya, yar fara ta maye gurbinta, su a wurinsu Wanda ya mutu shi ya jiyo bazasu Fasa business dinsu ba, Dan haka sai gidan ya koma kamar ba ayi mutuwa ba.
Yar fara yanzu itace magajiya domin duk karuwar data zo gidan anan ta sameta, ta fi sauran Sanin ciki da wajen sana'ar, itace tasan manyan maza masu kudi manyan mutane dake garin wayanda ake harka dasu kamar margayiya magajiya, itace tasan macen datafi kawo customers, tasan wacce takeda farin jini, haka kuma tasan macen datafi dacewa da namiji idan yazo yana Neman ta zabo mai zazzafa.
Wannan kenan.Indo da safiyyah na zaune tsakar gida suna cin abinci magajiya yarfara tayi sallama ta shigo, suka amsa ta suna kallonta, zama tai a kusa dasu ta kalli Safiyyah tace "yan mata dauki abincin ki kishiga daki kici zanyi magana da mamanki kinji".
Kwanon ta dauka batareda tayi magana ba ta shiga daki.
Yarfara ta maida kallonta wurin indo tace " kindai San tatsuniyar gizo bata wuce k'ok'i, kamar dai yadda na kwadaita miki wannan Sana'a tamu abaya ki ka k'i amincewa ban gaji ba shiyasa na sake dawowa Dan in tabbatar miki da zance na, haba Aisha kalle ki fa, da sauran kuruciyarki, shekarunki basu nunu ko kadan a fuskarki ba, wa zai yadda ke kika haifi Safiyyah,kinfi karfin wanki da guga, ga ki da babban jari mai tsoka a hannunki amma kin tsaya kina wahalar da rayuwarki , yanzu magajiya bata nan Dan haka nazo na miki tuni na baki lokaci ki Debi iya adadin kwanakin da kike so kiyi tunani.
Murmushi Indo tayi tace "yar fara kenan, nidai wannan Sana'a taku bata burgeni, kuma nayi alkawari bazan taba bari shaidan ya rudeni na afka ciki ba, kuma addua nake muku Allah ya ganar daku Ku daina".
" yanzu sai ki fara yimin wa'azi, ni dai na fada miki ya kamata ki tsaya kiyi tunani, na barki lafiya".
Daga fadin haka ta mike ta fita tabar indo zaune tana tunanin wannan rayuwa.Safiyyah ta katse mata tunani tana cewa "Anty zan tafi makaranta ki kawo kudin idan zan dawo sena siyo miki sabulun".
Sai da ta kalleta na sakan goma sannan ta shiga daki, kudin ta mika mata tana cewa " idan babu a shagon dake kan layi ki dawo Bana son kina kaiwa titin nan ke kadai, kisiyo abin da zaki dafa da safe na zuwa makaranta karkuma ki tsaya shiririta".
Karb'ar kudin tayi tana gyada kai sannan ta fita.
Indo komawa tayi ta zauna ta dafe kanta daya soma yi mata ciwo saboda tunani, ita tsoro ma takeji kar yarfara tazo da wata rigima akan gidan da suke ciki dalilin kin amincewa da bukatar ta.Washe gari bayan Safiyyah ta dawo daga makaranta, suna zaune a daki saboda ruwan da aka gama shekawa sanyi ya sauka, zee baby tayi sallama tana yamutsa fuska, kallon gidan take kamar taga kashi, amsawa Safiyyah tayi tana lekowa ta Dan rusuna ta gaida ita.
"Lafiya" ta amsa a takaice sannan ta sake kallonta tace "kizo ki kwaso min wankin can dan ni bazan iya daukar su ba" ta kai karshen maganar tana bintsire baki da harare-harare.
Jin abinda take cewa yasa indo fitowa da sauri da hijabi a hannunta tana cewa, "Safiyyah shiga ciki ki karasa goge sauran kayan nan" sannan ta maida kallonta ga zee tace "muje in dauko kayan sun mata nauyi amma ni zan iya dauka".
Zee tana karairaya ganin wata mota a kofar gidan tace " Ku kuka jiyo, muradina awanke min kayana" ta fada tana yarfa hannunta sama.
Shuru indo ta mata, dan ita kome za ayi saidai ayi bazata bar karamar yarinya kamar Safiyyah tana shiga irin gidan ba, gara ita batada sauran zabi daya wuce wannan.
Da shigarta gidan magajiya yarfara ta soma washe mata baki, indo sai takaita gaisuwar take yi.
"Mu shiga daga ciki sai muyi maganar ko" magajiya ta fada tana kokarin cire takalmin kafarta.
A sanyaye indo ta kalleta sannan tace "kayan wanki nazo dauka, ban kuma San maganar da kike nufi ba" daga haka ta dauki kayan da zee ta nuna mata tayi ficewarta.
Magajiya ta rike baki tana kallon bayan indo harta bace mata sanna tace "inkin San wata baki San wata ba wallahi, mune muka San duniya kuma duniya ta sanmu".
Zee dake kofar dakinta tana kallonta a boye ta tabe baki tana sakin gajeren tsaki sannan ta shige dakin.
*Safiyyah galadanchi ke muku fatan alkhairi.*
YOU ARE READING
RUBUTACCIYAR K'ADDARA
FanfictionLABARIN UWA DA Y'AR TA WANDA YAKE CIKE DA TAUSAYI DA AL'AJABI, KUYI KUTSE A CIKI DOMIN GANIN ABINDA YAKE FARUWA.