*RUBUTACCIYAR KADDARA*
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
( *home of expert and perfect writers)*💡*SOPHIE GALADANCHI* ✍🏼
(6)
Kallon sa tayi tana mikewa tsaye tace "ka dauki fadimatu ka daura ta akan mizanin da yarinyar nan take, zakaso a barta anan a yashe? Kabari ta farfado muji menene".
Shuru yayi jikinsa yayi sanyi sannan yace "Ku daukota" daga fadin haka ya bude kofar gidan bin bayansa suka yi suka shigar da ita har dakin huraira( maman fadimatu).
Dakyar suka samu ta farfado, kallon dakin take kafin ta sauke idonta kan fadimatu, hawaye suka zubo daga idonta.
Tada ta zaune sukayi fadimatu ta bata ruwa masu dumi tasha domin cikinta ya warware, ga duk kan alamu yunwa na daya daga cikin abubuwan dake dawainiya da ita.
Magajiya na zaune tana hutawa sai dariya take ta kira wayar daya daga cikin garadanta, bayan ya daga tace "gaishe Ku dai mazajen fama, tofa Abu yayi dan yarinyar ma bata kwana a gidan ba, abinda nake so kawai Ku dawo da uwarta".
Dariya yayi irin tasu ta yan Daba yace " haka muke so ranki yadade zamu maido ta anjima, amma matar ta jigata fa kwana biyu a daure, mudai fatanmu ki yago mana rabon mu mai tsoka".
"Kar ka damu indai naku Rabon ne daga na samu Deen ya daga wayata mukayi magana nima dakaina zan kiraku" ta fada tana gyara kwanciyarta, sai hango kanta take ta siyo man bleaching dinta tana cin kaji da sauran ababen more rayuwa.
Sai dare suka kawo indo wacce take fitar da numfashi dakyar saboda wahala, kuka take kamar ranta zai fita.
A lokacin tunanin inda Safiyyah take ya dawo mata ta sake sakin kuka, kenan Safiyyah ta zubar da mutuncin ta, yadda wani da ya haramta ya kutsa cikin mutuncin ta? Lallai tana cikin tashin hankali.Kulawa sosai Safiyyah take samu ba tare da Deen yasan tana gidan ba, Safiyyah bata boye musu abinda yake faruwa ba saboda ta rasa mafita dole tana bukatar shawara a wurin wani.
Zuwan da tayi gidan da niyyar rokon Deen alfarma take akan yabawa magajiya hakuri ta dawo mata da uwarta ba zuwa tayi saboda ta tafka babban kuskure ba arayuwarta.
Buba mai gadi ya jinjina lamarin sannan yace bayan kwana biyu idan kin kara warwarewa zansa huraira ta raka ki gida.
Huraira tace wannan shi ya kamata amma bamu sani ba ko sun maida ita sai dai ko a asirce zamu bincika, wannan masifar dame tayi kama? Mutum a yarasa y'ancin kansa? Dubi yadda ake bibiyar yarinya karama haka, shiyasa wallahi mu hankalin mu ya kasa kwanciya a gidan nan ko fadimatu bama kaunar abinda zai aka Alhaji ya daura idonsa a kanta,Allah dai ya kara karemu mu duka".
Suka amsa da ameen.
Deen yau da wuri ya dawo gida, sai yanzu abin yake damunsa, wannan fa shine karo na uku ya kasa samun macen da zata rage masa damuwa, anya wannan ba gargadi Allah ya ke masa ba, anya ba Allah ne yake son shi da rahama ba domin ya daina aikata wannan mummunar dabi'ar, a take ya tuna da wannan matar da aka kawo mai da kalaman data furta masa " idan ka taimaka wurin kare mutunci na nikuma nayi maka alkawarin addu'ar neman shiriya a koda yaushe, Allah ya shirye ka" , sai kuma maganar y'arta da aka kawo masa a maimakonta "shin kai wane irin mutum ne? idan kanwarka ce ko yarka zaka so ayi mata haka?".
Kukan da yake rikewa ne ya subuce masa ya zauna akan kujerar palonsa yana yin kukan kamar Allah ya aiko shi.
Saida yaji zuciyar shi ta rage zafi sannan ya yi shuru yana tunanin fuskar Safiyyah. Gashin kanta da ya kwanta har goshinta yana Neman hadewa da girarta, sai lips dinta Dana kasan yayi pink sosai na saman kuma yayi duhu, yadda manyan idonta suke zubar da hawaye, tana fada masa magana kamar bata son yin maganar, a hankali yayi murmushin da bai San yayi ba.Jikin Safiyyah yayi kyau Alhmdllh kuma har zuwa lokacin Deen bai san tana cikin gidan ba domin ko yar malam buba mai gadi bata fita ko ina balle Safiyyah data samu wurin fakewa na kwana biyu.
Indo kuwa jikinta yayi kamar ba komai amma sai ciwon ya tattare ya koma zuciyarta, bata kaunar ganin fuskar magajiya dan haka ta kasa tunkararta da Neman Safiyyah ko kuma son jin inda take, amma fa zuciya na azabtuwa.
sun yanke shawarar zuwa gidan su Safiyyah domin jin ko indo ta samu kubuta daga hannun garadan magajiya, sai dai Safiyyah zata nunawa inna huraira gidan kawai amma ita bazata Shiga ba saboda gudun ko ta b'aci haka kuma bata so wata daga cikin Matan gidan magajiya su ganta.
Sai da aka yi sallar magrib sannan suka fito daga gidansu bayan sun tabbtar da mai gidan baya nan, daga dan nesa da gidan Safiyyah ta tsaya ta nuna musu gidan, koda suka shiga a kwance suka samu Indo, lokacin babu wuta sai fiti dake kunne gefenta, tashi zaune tayi tana kallon su bayan ta amsa musu sallama muryarta kamar mai mura saboda yadda ta dashe tace "ga wuri Ku zauna" zama sukayi daga dan nesa da ita kan tabarmar suka gaisa sannan ta sake cewa "sai dai kuma ban gane Ku ba", murmushi huraira tayi tace " gaskiya ne baki sanmu ba, ni sunana huraira wannan y'ata ce fadimatu, shekaranjiya mai gidana malam buba yaga wata yarinya a kofar gida a some, muka dauketa babu lafiya dakyar muka samu ta farfado ta bamu labarin abinda ya faru, ta fada mana nan ne gidansu shine muka zo mugani ko mahaifiyarta ta dawo domin mu maida ita gida, sunan yarinyar Safiyyah " da sauri Indo da matsa kusa da huraira ta riko hannayenta duka sannan tace "Naji dadi da y'ata ta fada hannu mai kyau nakuma gode muku na godewa Allah, amma ina rokon alfarma a wurin ku, kuyimin kwatancen gidanku zan zo idan na gama yanke shawara, saboda a yanzu rayuwarmu daga ni har ita tana cikin had'ari, na yadda daku dan da zaku cutar damu da Baku zo Neman gidan nan ba, dan Allah Kuyi wannan alfarmar" ta karasa maganar tana zubar da hawayen tausayin Kansu.
Huraira tayi murmushi sannan tace "indan wannan bamuda matsala da yardar Allah zamu rike amana kafin lokacin da zaki zo, sannan gidanmu yana nan layi na uku bayan masallacin jumu'a dake unguwar mai dawaki, gidan shine na tara a layin yanada bakin gate da fenti ruwan toka".
" duk kwanakin da nayi bayan batan safiyyah, nayi su ne a kwance saboda jimamin rashin sanin inda safiyyah take, yanzu Dana gano inda take dole zamu bar gidan nan koma garin gaba daya".
Huraira tace "Allah shine abin godiya mu zamu tafi sai kinzo".
Godiya Indo ta sake yi musu sannan suka fito daga gidan, suka barta tana ci gaba da tunanin shawarar da zuciyarta ta bata.
A tsugunne suka samu safiyyah ta gaji da tsayuwa ta nufi wurin su da sauri huraira ta katse mata hanzari da cewa " mamanki ta dawo safiyyah sai dai tace mu koma dake saboda zamanku nan gidan akwai hadari, muje gida zan kara miki sauran bayani kafin wani ya ganmu anan kuma".
Juyawa sukayi da sauri suka karasa titi suka hau adaidaita sahu.
Jikin safiyyah a mace bata taba share kwana daya bata ga Antyn ta ba amma yau ga shi har kusan kwana biyar bata ganta ba, koda suka isa gidan duk hankalinta naga maganar da suka fara a can, lura da haka huraira ta zauna tayi mata bayani yadda zata gane sannan tace "kuma ina baki shawara koda Antynki ta zo nan karki fada mata abinda ya faru saboda kara tatar mata da hankali zakiyi kuma naga alamar bata da lafiya".
Shuru safiyyah tayi tana tunanin duk akanta mahaifiyarta take cikin wannan hali.
Indo kuwa niyyarta ta samu karamin gida koda mai daki daya ne ta kama musu haya amma me? Batada kudin da zasu kama koda kofar gida ne balle gida dan haka ta yanke shawarar zuwa ta dubo safiyyah gidan da take daganan zata nemi shawarar yar tata taji meya kamata suyi, sai dai tana tsoron kada wannan dalilin yasa Allura ta tono garma.
*safiyyah Galadanchi ke muku fatan Alkhairi*
![](https://img.wattpad.com/cover/210952048-288-k453654.jpg)
YOU ARE READING
RUBUTACCIYAR K'ADDARA
Fiksi PenggemarLABARIN UWA DA Y'AR TA WANDA YAKE CIKE DA TAUSAYI DA AL'AJABI, KUYI KUTSE A CIKI DOMIN GANIN ABINDA YAKE FARUWA.