SHAFI NA HUD'U

1.1K 60 1
                                        

*RUBUTACCIYAR KADDARA*

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
( *home of expert and perfect writers)*💡

*SOPHIE GALADANCHI* ✍🏼

(4)

Sai kusan asuba bacci ya dauke indo Mara dadi, koda ta farka karfe bakwai da rabi Safiyyah na zaune gefe tana shan kunu ta gama shirin zuwa makaranta.

A hankali indo ta mike, jikinta duk yayi sanyi fita tayi waje dan dauro alwala tayi sallah taga igiya cike da kaya suna digar ruwa, juyawa tayi ta kalli kofar dakin. Tasan aikin Safiyyah ne sai tayi murmushi sannan ta dauki buta ta zuba ruwa.

Tana salla Safiyyah ta mata sallama dan ta Makara yau saukinta ma yau jumua ce.

Acikin weekend din nan ma duk jikin indo a sanyaye yake kamar Mara lafiya tunda abin nan ya faru take yawan jin faduwar gaba, sai dai bata mance da Allah ba kullum cikin addu'a akan ya kara karesu itada gudaliyar y'ar ta.

Ranar lahadi bayan azahar tace Safiyyah ta shirya zuje kasuwa, bayan sun tafi duk wani Abu da yake da muhimmanci ta siya mata sannan ta rage ta ta bukatar da sauran canjin, bangaren abinci ma duk wani Abu da suke siya saida ta dan taba wanda zai kwana musu biyu sannan suka wuce gida, dan a tunaninta yanzu wanki ya dauke kafa dan duk Matan gidan magajiya yanzu ta musu wanki a satin nan da guga sai kuma ya sake taruwa sannan, Matan unguwar ma suna kawowa sedai ba akai-akai ba.

Washe gari Monday da sassafe Safiyyah ta wuce makaranta indo tana ta nanata mata "ki kula da hanya banda rawar kai, sannan banda kula maza".

Murmushi tayi tace " kai Anty maza kuma? Ai kinsan kema babu ruwana da mazan" ta fada tana rufe fuska da tafin hannunta saboda kunya.

"To shikenan Allah ya kaiki lafiya ya dawo min dake lafiya" Safiyyah ta amsa da ameen tana gyara wuyan hijab dinta sannan ta fita.

Karfe biyar saura Minti ashirin aka tada su dan haka take ta sauri ta dawo gida domin bada haddarta a islamiyya  yauma sunci Sa'a an tada su da wuri sbd mai yi musu lesson last period baya jin dadin jikinsa, ta kamo hanya tana tafiya hijabinta sai cika yake da iska.

Tace "kai na manta bana son bi hanyar can bayan la'asar saboda mazan nan masu zaman majalisa mtsww" ta fada tana juyawa ta koma gefen titi, kawarta da suke tafiya tare tace, "Safiyyah nan fa yafi miki sauki".

Safiyyah ta kalleta tace " saboda gidanku kafin akai wannan majalisar ne? Nikam bazan bi ta can ba" tana gama fadar haka ta juya ta ci gaba da tafiya.

Tana tafiya tana kallon motocin dake wucewa bata Ankara ba taji kamar anyi sama da ita, tayi shuru kafin ta gama fahimtar abinda yake faruwa, a hankali ta dago ta kalli mutanen dake cikin motar, gabanta yai wata irin faduwa, ta runtse idonta sai kuma ta soma hawaye, tana kallo suna tafiya ta kasa furta komai sai tunani take, me suke nufi da ita? To ita inama tasansu? Bata taba yin fada da wani ba da har zai turo a saceta, ko dai masu garkuwa da mutane ne?.

A zuciyarta tace idan kuwa sune lallai kwana Na sun kare, daga haka ta soma kuka a hankali har suka iso gidan, tana kallo aka shigar da ita dakin nan dai aka kaita tana kallo suka rufe kofar suka barta a tsaye tsakiyar dakin.
Jikin kofar ta koma tasa iya karfinta tana dukan kofar har saida ta gaji ta tsugunna a kasa tana kuka.

Ta zaune bakin kofar aka turo kofar, Samuel ne dauke da katon tray da kala-kalar abinci, gefenta ya ajiye ba tare da ya furta ko wace kalma ba ya fita tareda kulle kofar da key.

Wani kukan ta kuma fashewa dashi tana dora hannu akai, mikewa tayi ta shiga zagaya dakin tana kuka.
  

Shuru babu labarin dawowar Safiyyah daga makaranta har karfe shida, hankalin indo yayi matukar tashi da sauri ta dauki hijabinta ta fita cike da tunanin inda Safiyyah ta tsaya bata dawo ba har karfe shida, bata taba yin haka ba, adaidata tahau zuwa makarantar su amma saita samu gate dinma a kulle, juyawa tayi da kafa taje islamiyyar su wai ko taga tayi letti tace bari ta tsaya islamiyyarsu, can ma malaminsu da yan ajinsu sukace yau bata zo ba, tun a wurin ta soma kuka ta kama hanyar zuwa gida zuciyarta nata yi mata sak'e-sak'e tana fatan ta sameta a gida idan ta koma yanzu.

Har akayi sallar magrib tana kuka haka ishai ma, sai lokacin ta tuna batayi ko sallar magrib sannan a hankali ta bude kofar dake dakin da alamar nan ne toilet, alwala tayi ta fito ta tsaya tunanin ina ne gabas daga baya dai ta yanke shawarar kallon gadon dake dakin wurin yafi kamada alkibla, ta fara sallar magrib sannan ta Dora da isha'i, ta fara shafa'i kenan aka bude kofar, yau kam dakin da wuta a kunne saboda ita ba da dare aka kawo ta ba, tsayawa yayi yana kallonta bayan ya rufe kofar ya jingina jikinsa da ita, kallonta yake tayi harta kammala sallolinta ta tsaya addu'a ta Shafa.

Kallon tray din abincin yayi ya tab'e bakinsa sannan ya matsa kusa da ita.

Babu zato tajishi kusa da ita cike da tashin hankali ta furta "innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un" sai kuka ya kwace mata ta durkusa a wurin tana kallon yadda ya zuba mata manyan idonsa.

Cikin kukan tace "meyasa ka tura aka dauko ni daga hanyar komawata gida? Kasan ni ne? Dan Allah kayi hakuri wallahi ko da zanje makaranta sai da Anty tacemin kar in kula maza" dan Allah ka barni na koma gida kar ka yimin komai", har lokacin kuka take tana kallon sa, shima dai ya saki baki kawai yana kallonta.

"Haba kai wane irin mutum ne? Ko zaka so ayiwa k'anwarka ko y'arka haka?".

Wani irin sarawa kansa yayi ya runtse idonsa yana fitar da numfashi da sauri-sauri, dagowa yayi yaci gaba da kallonta yana kokarin mayar da hawayen dake son zubowa daga idonsa.

Shuru tayi ta koma can lungun wardrobe tana kuka tana kiran Anty.

Sun jima a haka shi kansa bai San iya adadin lokacin daya dauka dafe da kansa ba, sannan ya mike ya fita daga dakin saida ya tsaya daga waje ya kulle kofar da key sannan ya fita.

Zuwa lokacin indo haukacewa ne kawai batayi ba, sai yanzu take ganin wautar kanta na rashin sanin gidan kawayen Safiyyah koba komai tasan akwai inda zata je domin jin ko taje makarantar bokon ma, kofar gidan tazo ta tsaya tana sauke ajiyar zuciya, wannan shine karo na shida tana zuwa titi ta dawo takalminta har ya tsinke amma bata damu ba, duk iskan da ake a gari saboda hadarin daya gama haduwa zufa take ta ko ina idonta duk sun kumbura, gashi babu wanda zata iya fadawa damuwarta dan yanzu bata da lokacin magajiya.

Bayan fitarsa safiyyah ta saka kanta tsakanin cinyoyinta tana mai ci gaba da kuka tana fadin "Allah ka kubutar dani, Allah ka tsare ni, Anty tace idan na yadda namiji ya taba ni ciki zanyi shikenan kowa zai daina sona aringa nuna ni" tana wurin taji an bude kofar, shine ya dawo ya sauya kaya zuwa shadda fara k'al sai daukar ido take a hankali yake tafiya har ya isa kusa da ita, tashi tsaye tayi ta jingina da bango numfashinta yasoma yi sama-sama saboda tsoro ta runtse idonta tana jira taji ya taba ta ta kwalla ihu sai taji yace.

"Ki fito Samuel ya maida ke gida, ki kuma yi min shuru tunda ko tabaki banyi ba", daga haka ya fice ya bar mata kofar bude, ganin haka yasa ta fita da sauri har tana tuntube amma bata Ganshi ba, ganin kofar ma abude yasa ta nufi fita, saura kadan suyi karo da samuel, ya juya tabi bayansa ta shiga motar, har kofar gida ya sauketa tana mamakin inda yasan gidansu amma ta share tunda dai ya dawo da ita gidan, ta shiga tana ihun kiran " Anty! Anty! Kina ina gani na dawo" duka dakunan gidan saida ta leka ta dawo ta tsaya tsakar gida sai taga kular abincin su a kife ga taliyar ciki ta zuba kasa, lekawa daki tayi ta kalli agogo karfe goma na dare gabanta yayi wata irin mummunar faduwa, da gudu ta fito ta ci karo da dan kwalin indo a kofar gidan ga takalminta daya tsinke da dankunnenta guda daya a kasa.

Hannu ta Dora akai tana kiran sunanta "ANTY!" Tareda sakin kuka da iya karfinta.

*Safiyyah Galadanchi ke muku fatan Alkhairi*

RUBUTACCIYAR K'ADDARAWhere stories live. Discover now