BABI NA ASHIRIN DA BAKWAI

758 55 2
                                    


*RUBUTACCIYAR KADDARA*

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
( *home of expert and perfect writers)*💡

*SOPHIE GALADANCHI* ✍🏼

27

Gefen wuyansa Abubakar ya taba yana cewa "jikinka fa da alamar zazzabi gara kakoma gida ka kwanta" karamin tsaki Deen yayi yace "kona koma gida maganar banza ce dan wahala ma zan kara yi, waccen yarinyar da take makaranta inaga bazata karasa karatun nan ba" Abubakar ya harare shi yana cewa "da dai kabari har ta karasa, wallahi ni gani nake ma kayi mata girma da yawa" shuru yayi dan yaji haushin maganar Abubakar.

Gyara zamansa yayi yana cewa "idan ka gama iskancin naka ka samo min abinci wurin matar ka" Abubakar ya kwashe da dariya yana cewa "bata karasa bane tuzuru, yanzu zaka ganta indai ta kammala" shuru Deen yayi yana sauraren yadda kansa ke sarawa, tunani ya shiga yi kuma har yaushe yarinyar nan zata gama makaranta.

Bata taba fadawa Abba abinda yake damunta ba, bala'in tsorace take, bata shirya jin tana dauke da abinda take tunani ba, tana wahala musamman da dare saboda ciwon kai da rashin karfin jiki da take fama dashi.

Daren sallah masu yi musu aikin salla sukazo, Hajiya Abba yace ta samo yan Togo guda biyu sai yan uwansa daga jega da suke zuwa duk shekara, ita dai tace a bangarenta zatayi nata, "Aisha nafa lura tun randa muka je jega baki jin dadi kuma zakice a kawo miki aiki" tana jera kaya acikin wardrobe tace "nidai nafiso ayi anan kawai dan bazan iya fita can ba, kuma kana ganin yadda Hajiya take min bana son fitina" gyada kansa yayi yana cewa "to shikenan, idan aka bata min gida sai kin wanke shi" bata kalle ba tace "Na yadda" mikewa yayi ya mata sallama dan yana son zuwa wurin Deen akan maganar gidan nan da yake ciki yanaso ya sake ganin gidan.

Washe gari da wuri ta tashi sukayi girki sannan suka shirya shiga suyar nama, tunda aka soma ta soma amai tun tanayi tana karfin hali har taji bata ma son ganin naman, dakinta ta shige ta rufe ko ina ta kwanta, lokacin da Abba ya shigo ya neme ta akace ai ta kwanta saboda tana ta amai hankalinshi ya tashi.

Koda ya shiga dakinta a kwance ya sameta ya karasa kusa da ita yana mata sannu dakai ta amsa mishi saboda bata jin karfi a jikinta, ya taba jikinta yana cewa "kona kira Dr asma'u ne"? Bata amsa mishi ba ya dauko wayarsa daga aljihu yakira wayarta, duk da tana aiki ne amma sai tace "to bari in fadawa mai gidan sai ka turo driver ya dauke ni" ya amsa yana godiya ya fita, Safiyyah ya aika ta fadawa driver, yana zaune har Dr din tazo, bayan ta duba ta tace "Hajiya tashi mu gwada wannan dan nasan irin ciwo wannan Na matan aure bai wuce ciki " gaban Anty ya fadi amma sai ta dake tana mikewa zaune, robar data bata ta karba ta shiga toilet, babu dadewa ta fito ta mika mata robar, gwajin farko ya nuna ciki, cike da farin ciki take fada musu, dadi sosai Abba yaji yakasa rufe bakinsa, karin ruwa ta sakawa Anty sannan ta rubuta maganin da za a bata Na amai sannan ta musu sallama, tana fita Anty ta saka kuka, Abba ya shiga aikin lallashi, yana farin ciki da wannan kyautar.

Kasancewar shi babban mutum ne shi mai hankali, yayiwa Allah godiya amma ya kama bakinsa, yana tunanin yadda Hajiya zataji, komai lalacewar ta yana sonta itama bai cire rai ace yau gata da ciki ba dukda ita bata wani nuna damuwa akan rashin haihuwarta.

Su Safiyyah duk basu San miyar da ake sha ba, ana gama hidimar salla suka shiga ta biki, kwana biyu bataga Deen ba duk da hankalinta yana kanshi amma batada karfin gwiwar kiransa.

Sai da aka fara biki gidansu ya Cika har Anty ta aika aka dauko yan gidansu daga kauyensu, basuyi wani bidi'a ba aka daura aure aka kai amarya dakinta, dan lokacin data zauna da Safiyyah sai taji kamar tare duka girma rana daya za a raba su, bayan umman ta babu Wanda tayi kusanci dashi kamar Safiyyah, dakyar aka bambareta jikin safiyyah da zasu tafi, Anty da dama bajin dadin jikinta takeyi ba har zata ce hafsatu ta tsaya ta kara kwanaki sai ta tuno hafsatun ma yanzu matar aure ce, duk sai taji babu dadi, dole duk suka watse aka barta daga ita sai Safiyyah mutanen jega da suka rage basu shiri da ita yan bin bayan Hajiya ne, bata iya kama aikin yadda ya kamata ba dole sai Safiyyah ce tayi iya kokarinta.

Ko hutawa bata yi ba sai ga kiran Halima tana rokonta tazo babu kowa ita kadai ce, shikuma Muhammad din duk da yana nan amma bata son shishshige masa dan ta gano in bata nesa dashi kwakwarta zata ci.

Dakyar Anty ta yadda Safiyyah taje amma karfe shida ta tabbatar ta dawo.
Tana can Deeni ya kira ta, jin tana gidan amarya ya saka shi Jan dogon tsaki yana cewa "kuna fa shiga hancin angon nan dayawa, ki shirya gani nan zan dauko ki" to kawai ta amsa dashi dan dama karfe shida ta kusa.
Halima tayi mitar wannan takurar daya kawo mata amma babu yadda zatayi dole Safiyyah ta tafi da alkawarin dawowa wani satin saboda sun koma makaranta.

Tana zaune gaban mota bayan ya daukota ya kalleta yana cewa "Safiyyah ki bani aron hankalinki nan magana zamuyi ta fahimta" sake baki tayi tana kallonsa, yaci gaba da cewa "Allah ya gani aure nake so, kuma ni ke nake so, gashi ke kuma makaranta kike bazan iya jiranki ba har shekara biyu, katse miki karatunki kuma kamar tauye miki hakki ne, Na yanke shawarar Neman wata matar kafin ki kammala karatunki zuwa lokacin ma kin kara girma" tunani ta shiga yi batareda ta amsa mishi ba, yana nufin tun kafin suyi aure kishiya zai mata, batasan Yaya kishi yake ba amma taji bala'in haushin abinda yace, bata bashi amsaba har suka iso gida sannan ta bude mota kawai ta fita.

Binta da kallo yayi har ta shiga gida tana bugo kofar karau! Bai San lokacin da ya kwashe da dariya ba, harga Allah ta bashi dariya, wai wannan yar ficiciyar yarinyar ta iya kishi. Sosa gemunsa yayi sannan ya fito daga motar yabi bayan ta.



_to nasan dai an gaji da hakuri dani amma sai ban barin bada hakuri_

RUBUTACCIYAR K'ADDARAWhere stories live. Discover now