BABI NA ASHIRIN DA UKU

642 49 0
                                    

*RUBUTACCIYAR KADDARA*

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
( *home of expert and perfect writers)*💡

*SOPHIE GALADANCHI* ✍🏼

Page 23

Bayan sunyi sallar asuba suna zaune sunyi shuru su dukansu Halima ta kalli Safiyyah tace "nayi tunanin koda bakya hannun Abba yana kula dake amma, sai naji kince kuna neman gidan da zaku zauna"?

Safiyyah ta tabe baki sannan tace " Abba bai dade da Sanin ina rayuwa a duniya ba, nima nayi tunanin ko ya fada muku labarina nida Anty ai" Halima ta girgiza mata kai kanta Na kullewa, Safiyyah taci gaba da cewa "A labarin da naji wurin kanwar Anty cewa tayi a kauyen mu ba'a bari mace ta wuce shekara goma sha daya ba a mata aure ba, sai aka samu akasi ta gefen Anty Dan ita sai da ta shekara goma sha biyar ko mijin aure batada shi, Baffan mu ya zaba mata miji daga baya amma sai ta turje ta nuna bata sonshi sai aka fasa auren dukda baya daga cikin al'adunsu, innarsu Anty taji haushin abinda Anty tayi sai ta ringa Dora mata tallar fura da nono, lallai bazata zauna gida ba bamijin aure sannan ba a morarta, Baffa yayi kokarin hanawa amma inna taki ji, gori a gari Anty tana shanshi amma bata damu ba, wasu har suna cewa Anty bazata iya zaman aure ba Dan ta saba da iskanci, shikuma Abba gidan gonar su a can kauyensu anty yake, tana kaimasa fura saboda yanaso shine sai Abba yaji yana sonta yaje yai magana da Baffa, Baffa yace zaiyi magana da kaninsa Baffa salihu, dama zaman kawai sukeyi a tsakanin su babu jituwa, Baffa salihu yaji haushi Anty Zata auri mai kudi kuma Dan birni sai ya soma surutu a gari yana cewa Baffa Gidado zai siyarda yarsa ga maimota Na gidan gona, a lokacin kakansu Anty yana da rai amma tsufa ya kamashi yaje har wurinsa ya fadi maganganu marasa dadi shine sai kakansu yace ya kashe maganar kar a kuma yinta, haka nan aka fasa zancen auren, to bayan wani lokaci Anty taje tallar fura sai ta kai masa, a lokacin sai...." Ta kasa karasawa saboda kuka ga zancen ya mata nauyi a abaki, taci gaba da cewa "a lokacin aka sameni, ranar kuma inna ta gane abinda ya faru da Anty bayan ta dawo gida amma sai suka boye saboda macen da duk irin wannan kaddarar ta afkawa a garin bazata taba aure ba saboda ko an auresu ana wulakanta su, bayan wani Dan lokaci sai ciki ya bayyana ajikin Anty Wanda shine yayi sanadiyyar Baffa ya koreta daga gidan, duk irin hakurin da take bashi bai saurareta ba kuma yace baya bukatar sake ganinta saboda ta wulakanta shi ta zubar mai da daraja, daga nan ta baro gida shine bata koma ba sai kafin wannan azumin".

" data fito sai ta sauka anan batada kowa sai wata magajiyar gidan karuwai ce ta dauketa aikin wanke wanke a wurin siyar da abincinta, a gidan karuwan Anty ta haifeni, duk da magajiya taso dorata akan wannan sana'ar amma data nuna bata so sai takkyaleta, har Na girma a wurin ta muke anty tana yiwa matan gidan guga da wanki suna biyanta, komai nawa Anty ce takeyi min bantaba sanin cewa bada aure aka haifeni ba bantaba ganin danginmu ba kullum idan Na tambaya anty sai ta daina kulani Nikuma bana son ganin bacin ranta sai Na daina tambaya nasan komai Daren dadewa sai naji ko waye mahaifina da dangina, ciwo ya kama magajiya har sai da yayi ajalinta, daga nan muka soma Shiga matsin rayuwa Dan sabuwar magajiya tanace se anty ta yadda tayi karuwanci anty taki, nidai bansan ya akayi ba Anty ta fita ta dade bata dawo ba, sai ta dawo a firgice bayan kwana biyu nima daga makaranta aka daukeni sai gidan yayanki......" Daga nan ta karasa bata labarin abinda ya faru har suka zauna a gidan sa sannan kuma har yanzu anty batasan abinda ya faru ba da aka sato Safiyyah.

Halima tayi saurin matsawa kusa da ita tace "Dan Allah kuma ki rufa masa asiri kinji" Safiyyah tayi murmushi tace "ko ina ko bana so rufa masa asiri tamkar wajibi ne a gareni, nasan yayanmu bai San koni wacece ba bayan diyar Abba, tun ranar da aka kai masa ni bai kara bin wata mace ba sannan kuma yana sona da aure tsakani da Allah idan na tona masa tamkar na tonawa kaina asiri ne"

Halima tayi murmushi tace "Ashe tun daga can kun gama kullowa shine ranar kukayi kamar dacan Baku San juna ba Ashe dai masoyane" kunya Safiya taji ta tashi tsaye tana cewa "bari nayi wanka akwai makaranta yau" Halima tace "nima haka amma ni zan kaiki makaranta yau" daga haka suka soma shiri.

"Ki ajiye tsintsiyar nan Aisha kizo ki huta"  kallonsa tayi tun jiya da tazo se yau suka hada ido saboda tsananin kunyar sa dake dawainiya da ita tace "nariga na saba ne bazan iya zama ina ganin aiki banyi ba, tu da ka hanani wanki to ja barni na share Palon nan sannan na dafa mana abin kari" murmushi yayi yace "Ashe zanga haka a rayuwata? Nikam bansan wannan ba harda su wanki da guga"?

Dariya kawai tayi taci gaba da shararta, sai da ta gama sannan ta shiga kitchen, tsayawa tayi tana kallon kitchen din, ita ko wannan murhun bata iya kunnawa ba, sai da ta kirashi ya kunna mata, saiga Alhaji na fere Irish,lol.

Wanka sukayi suka kwanta abinsu saboda gajiya, Abba kam ji yayi kamar bai taba aure ba sai yanzu, hankalinsa ya kwanta sosai yana fatan wannan jin dadi ya dore.

*kuyi hakuri babu yawa*

RUBUTACCIYAR K'ADDARAWhere stories live. Discover now