SHAFI NA TAKWAS

895 60 2
                                        

*RUBUTACCIYAR KADDARA*

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
( *home of expert and perfect writers)*💡

*SOPHIE GALADANCHI* ✍🏼

(8)

Malam Buba bai koma cikin gida ba ya zauna kofar gida yana jiran dawowar mai gida Deen.

Deen kuwa yau ba shida niyyar dawowa da wuri dan yafi jin dadin zaman office din a yanzu, yana zaune yana kallon wani film a system dinsa
Abokinsa Abubakar ya shigo, kallon sa yayi yana dariya yace "mutumina ya naga kwana biyu kana wuni a office?"
Shima dariyar yayi sannan yace "Nafi jin dadin zaman office din ne tunda ko naje gidan babu kowa sai dai in yi bacci aikin danna waya watarana ma idan baccin yaki zuwa sai inyita tunani marasa kan gado, kaga nan ai ina jin motsin ku" Abubakar zama yayi kujerar dake kallon Deen yace "to ai duk laifinka ne, wane mutum mai hankali ne zai mallaki wannan babban gidan amma yabarshi bakowa a ciki, matsalar gauranci kenan dayanzu maimakon waya ba sai ka latsa matarka ba" ya fadi zancen yana dariya sannan yaci gaba "au ka jini nikuma sai kace bansan mutumin nawa ba, Ashe fa kai mai yan mata ne buhu-buhu".

Murmushi Deen yayi yasa Biro yana Sosa gemunsa sannan yace " kai wallahi maza sunyi hankali yanzu kamar anyimin asiri gaba daya abin baya gabana, nidai insha Allahu na tuba" ya fada yana kallon cikin iron Abubakar.

"To Alhamdulillahi abinda nake ta nuna maka kenan Nuruddeen, ni wallahi nafi kowa jin dadin wannan lamarin, yanzu sai zancen fito da mata kenan ko acikin wadanda aka murk'ushe ne a samo daya" a tare suka kwashe da dariya ganin yadda Abubakar yayi maganar, Deen ya ware hannayensa duka biyu yana tabe baki yace "ban taba forcing din mace ba, duk da amincewar su ne".

Abubakar yace "to Allah ya yafe maka dai yasa ka shiryu" amsawa yayi da ameen yana dariya kasa-kasa.

Indo koda ta koma gida ba zama tayi ba ci gaba tayi da hada musu kayansu,  tana zaune tana shan gari magajiya ta shigo gidan tana murmushi ta zauna kusa da ita tana cewa "ko kufa yanzu? Shuru nakeji tunda yarinya ta zama y'ar hannu shima dan banzan ko wayata baya dauka", shuru Indo ta mata dan batasan inda zancenta ya Dosa ba har ta Karasi surutun ta ta fita bata tanka ta ba.

Da yamma a ranar ta tafi tasha saboda taso taji a kalla idan zata je garinsu nawa zata kashe dan tasan ba mota daya zata hau ba.

Jiki a matukar sanyaye ta dawo jin ba kudin motar canjin hannunta ma bazasu kaita ba balle ayi maganar komawa gida, tanajin kunyar bayan duk wayannan shekaru da ta deba bata waiwayi gida ba taje musu a haka, ko kayan sawa na arziki babu, balle wata alama a jiki da zata nuna cewar ana cikin walwala, duk wanda ya ganta yasan ba dadin wurin da take zama take ji ba.
Lallai wannan tafiyar bazata yuwu ba, zataje ta dauko safiyyah suci gaba da addu'a da kuma hakuri idan ta hada kudin tafiyar sai ta tafi da Safiyyah gaba daya.

Yana zaune bakin gate kamar ko yaushe yajiyo horn din motar Deen da sauri ya tashi ya bude masa gate, bayan ya shigo ya rufe gate din ya isa wurinsa da sauri yana gaidashi. Deen ya tsaya suka gaisa yanata fara'a yace "malam ya aiki? Kwana biyu bamu gaisa ba kuma malam ana haka? Lokacin albashi yayi baka yi magana ba, wallahi nikuma abubuwa sun sha kaina shiyasa kajini shuru, dan Allah ayi hakuri" murmushi malam Buba yayi yana Sosa kai yace " ai wallahi Alhaji babu komai ko yanzu ma wata magana ce ta kawo ni" Deen ya dago ya kalle shi yace "to bisimillah malam mushiga daga ciki" yayi gaba malam Buba yabi bayan sa, suka shiga palon Deen ya zauna yana nunawa malam Buba kujera yace ya zauna duk da yasan ba zama zaiyi akai ba sai dai kasa.

Malam buba yace "wallahi Alhaji wata alfarma nake nema, wata y'ar uwata ce take Neman wurin zama amma abin ya gagara kuma ranka ya Dade suna cikin wani hali, shine data fadamin sai nace to tayi hakuri har in samu ganin ka in roki alfarma ko zata samu aron daki daya kafin ko mai ya daidaita sai su tashi Alhaji".

Sai da malam Buba ya dasa aya sannan Deen yayi magana yace " haba malam buba shine kake ta wannan kame-kame? Ai ko ba dan halinka na dattako ba saboda Allah ma zamuyi taimako muma ai Allah taimakom mu yayi, kuma idan munada iko bazamu bari dan uwan mu musulmi ya wulakanta ba, ni banida matsala kawai kazanta ce bana so kuma kuna kiyayewa dan haka yanzu idan na shiga na dan huta zan dubo maka keys din BQ din nan dake gefenku sai a basu, insha Allah wannan taimako bazai gagaremu ba" ya karasa maganar yana mikewa tsaye sai kuma yace " Au na manta malam Buba bari in shiga ciki in kawo maka kudinka dan satin nan gaskiya banida lokaci".

Tunda ya fara magana farin ciki ya lullube malam Buba bakinsa ya kira ruhuwa har sai da ya durkusa wajen yana yiwa Deen godiya.

Shiga yayi ya kirgo masa kudin albashinsa ya kawo masa, ya fita yana kara jaddada godiya ga Allah da kuma Deen.

Huraira data gama sauraren tatsuniyarsa ta buntsire baki tana hararansa tace "malam wai rawar jikin me kake akan wannan matar ni ina ganin zakewarka fa".

Nan take ya soma kame-kame yana cewa " ai taimako ne kuma ba kece mai gidan ba tunda mai gida ya amince banida matsala Allah ya ga zuciya".

Mikewa tayi ta karkade zanen ta tace "Allah ya kyauta" tsayawa tayi ta kalli su Safiya dake dan nesa dasu sannan ta shige daki.

Saida indo tayi shirinta tsaf na zuwa daukar safiyyah sannan ta nufi gidan zuciyarta na ta sake-sake, wata sana'ar zan tsiro da ita wannan bazata fiddani ba ga karatun safiyyah ya tsaya cak, har sai da aka wuce layin sannan ta Ankara.

Safiyyah na zaune kofar dakin su tana ta tunamin Antyn ta tajiyo sallamarta sun shigo gidan tare da malam Buba.


*Safiyyah Galadanchi ke muku fatan Alkhairi*

RUBUTACCIYAR K'ADDARAStories to obsess over. Discover now