BABI NA Ashirin da daya

710 49 2
                                    

*RUBUTACCIYAR KADDARA*

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
( *home of expert and perfect writers)*💡

*SOPHIE GALADANCHI* ✍🏼

Page 21

Game takeyi da wayar da Abbanta ya bata Dan gaba daya yau sai taji bata jin bacci gashi dare ya soma yi, ta kalli Halima tayi shirin bacci cikin rigar baccin ta da kadan ta wuce gwiwa zata kwanta suka hada ido Halima tace "bakya jin magana ko? To bari yayanmu yazo sena fadamai kina kwana da brazier ajikin ki kuma bakya sauya kaya kisaka na bacci in zaki kwanta" Safiyyah ta rufe ido tana cewa "ni kunya nakeji irin kayan nan mutum fa kadan ne bai koma tsirara ba" tsaki Halima tayi tana cewa "nagodewa Allah da ba yanzu za a miki aure ba da mijinki yaga kauyanci, tashi maza ki wanka ko yanzu mu b'ata dake" ta fada bayan ta zauna bayan Safiyyah tana Harar ta.

Safiyyah kullum mamaki take yadda bata ma ganin abban nata gashi shi kadai ta sani, kullum sai dai ya kira waya yana tambayar su lafiya suke ita da Halima.

Deen kuwa saida ya shafe sati biyu sannan yace bari ya kira Abba yaji idan yana gida zai yi magana dashi akan zancen Muhammad.
Wayarsa ya daga yayi dialing numbern tayi ringing ba a daga ba sai ya sake kira.

Fitowarta daga toilet kenan taji ringin din wayar tayi mamaki Dan abbansu baya kira war haka bata damu da duba wayar ba taki dagawa, ganin yayi two miscalls ba adauka ba yasa ya hakura da kiran.

Abban Safiyyah bai gaji da yawon kauyensu ba duk sati sai ya ware rana daya yaje Dan yanzu bashida buri irin yaga hankalinsa ya dawo wuri daya.

Hajiyarsu ya sama da maganar ta rike haba tana kallon sannan tace "ba lallai yadda kayimin bayani Na fahimta sauran su fahimta ba, yanzu idan nayi magana konayi ruwa na yi tsaki zai iya zama jidali, idan kaje kamusu bayani idan sun fahimta to in basu fahimta ba sai kayi hakuri, sai kuma a kawo mana yarinyar muganta Allah ya tsare gaba ya karbi tuba"
Shuru yayi saida ta gama sannan ya mata godiya ya fita.

Wannan karon indo taji nasihar da Baffa ya mata har taji cewar ta amince da auren Abdullahi, koba komai zata zauna inuwa daya da yarta, taci gaba da bata tarbiya bayan shekaru kuma data dauka tana zaman kunci a rayuwarta zata samu yancin kanta cikin kwanciyar hankali a kuma karkashin inuwar aure.

Wannan karon da Abdullahi yazo ba karamin farin ciki yayi ba, ji yake kamar Wannan ne aurensa na farko, yayita jera mata godiya da Addu'o'i har sai da ta soma jin kunya, daya bar garin bai tsaya ko ina ba sai gwadabawa yaje domin jin ko sun gama bincikensu.

"Babban mutum dakai ace zaka auro matar data gama lalacewa a gidan karuwai, karuwa ce zaka auro fa, matar da akace har yarinya gareta wadda ba asan ubanta ba" kanin mahaifinsa ke maganar, autansu ma ya kama masa yana cewa "kuma bayan haka ma ace shekara fiye da goma tana zaune a gidan karuwai, haba ai abin yayi muni wallahi"

"Yauwa fada masa dai, tun wuri yadawo hankalinsa inba haka ba zai batawa kansa suna muma ya bata mana" Abdullahi ya sake yin kasa dakai yace "baba Malam bakwa tunanin yin hakan kamar jahadi ne? A gidan karuwan data zauna ba zaman zina ko karuwanci tayi ba, rashin mafaka ne yasa ta zauna can, nima kaina saida nayi bincike a unguwar data zauna Dan bata fadamin dakanta ba, amma babu Wanda ya taba cemin anganta da wani ko tana shashanci kamar sauran bayan haka kuma ga misali nan yarinyar data haifa, yarinyar ta samu tarbiyar da ko Wanda yakeda uwa da uba bazai fita ba"

Tsaki suka ja a tare sannan baba karami yace "to mudinma munyo bincike kuma anfada mana gaskiya Dan haka mun gama magana" zuciyar Abdullahi ta kasa hakuri yana kallon kasa yace "yarda ake cewa ta haifa shegiya tabbas ta haifeta kuma nine nan uban yarinyar yanzu haka tana gida na, Ku duba mana na cutar da uwarta inaso na gyara laifin dana aikata mata, dukanku bazaku so hakan ya faru akan yayanku ba, niba saurayiba, ba gauro ba haka kuma ba tuzuru ba sannan ba yaro bane ni nasan abinda nakeyi, inada dukiyar da zanje nayi auren Aisha batareda kunsani ba amma ina ganin girman Ku kune iyayena kune nake tutiya daku idan baku bani dama na gyara kuskurena ba wazai bani? Safiyyah itace yarda Aisha ta haifa kuma tana gidana, na karbo ta saboda inasonta kamar yadda nakeson uwarta".

Shuru sukayi kamar ruwa ya cisu baba Audu ya kalli baba karami yace "sai asaka ranar da zamuje Neman auren, magana ta kare babu Wani Kwana-kwana tunda abin ta haka yazo Allah ya yafe mana baki daya"

Sai a lokacin ya sake ajiyar zuciya yace "ko gobe ne, Bana so a dauki lokaci saboda yanzu mu ba yara bane daurin aure kawai yakamata ayi"

To suka amsa dashi kafin yayi musu sallama.

Indo tayi tagumi tana sauraren abinda inna ke fada wai garzali yace yana son Safiyyah, kuma inna lallashinta take su amince itada mahaifin Safiyyah saboda kar kuma ajanyo musu wani jidali daga gefen Baffa salihu dama zaman ga yadda ake yinsa babu jituwa.

Indo tace "innah nidai nasan Safiyyah bazata iya zama a garin nan ba,balle kuma aure da gazali, bance tafi karfinsa ba amma rayuwar da sukayi ba iri daya bane shiyasa kika ga har tabar gidan nan ta kasa sakewa, Dan Allah abashi hakuri kuce kawai babanta yace bazai aurar da ita anan ba yayi hakuri".

" hmm to idan Baffanku yazo sai kije kuyi magana bari na aika hafsatu ta siyowa bakin dazasu zo ruwa" gyada mata kai kawai Indo tayi tana tunamin yadda rigimar zata taso idansu Baffa salihu sukaji abinda zasuce gameda neman auren Safiyyah ga gazali.


Mikewa Deen yayi ya shirya yanata sauri duk da baya jin dadin jikinsa, ta tabbata dai mutanen nan bazasu dawo ba, amma ya tabbatar yarasa farin Cikinsa wallahi bai taba son mace kamar yadda yake son Safiyyah ba, yasan idan yaje wurin Abba sai yasha masifa bazai yuwu ace kana gari daya da iyayenka ba amma baka zuwa gaidasu, danma Abba yanada hakuri da ba haka ba.

Koda ya shiga gidan alokacin Aisha ta dawo daga makaranta ta rungumeshi, yaji dadin ganinta sannan yaji dadin ganin motar Abba a gidan.

Suna isa Palon ta sake shi tana cewa barin baka surprise dinda nace, da sauri ta shiga dakinsu, ta samu Safiyyah tana taje Gashin kanta duk ranta abace saboda rashin samun mai kitso a unguwar, ji tayi Aisha ta janyo hannunta tana cewa "Zo kanwarmu ga babban Yaya" jin yayansu ne yazo yasa Safiyyah binta saboda tana so taganshi yadda takejin labarin shi, sai da suka kai gabanshi sannan suka ja birki.

Wani irin faduwa gabansu yayi a tare suka kurawa juna ido.


_Ina Baku hakuri akan jin shuru da kuka yi kwana biyu, wasu daga cikinku sun San dalili wasu kuma basu sani ba, amma dai kuyimin uziri wallahi naso kafin yanzu na karasa shi nima na huta nagode sosai ina yi muku fatan alkhairi_

RUBUTACCIYAR K'ADDARAWhere stories live. Discover now