SHAFI NA GOMA

787 53 21
                                    

*RUBUTACCIYAR KADDARA*

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
( *home of expert and perfect writers)*💡

*SOPHIE GALADANCHI* ✍🏼

(10)

Dafe kansa yayi yana kallon wayarsa dake ringing, gaba daya week din nan be yi tunanin zuwa gida ba, to yanzu ma idan ya daga wayar mai zai cewa Abba? Tashi yayi daga kwancen da yake ya shiga toilet ya Dan watsa ruwa.

Shirinsa a cikin sauri ya yishi Dan haka yana fita ya shiga mota yabar gidan, zuciyarsa tana tsa yi masa sakar abinda zai fadawa Abba domin kare Kansa.

A palon sa ya sameshi ya shiga da sallama yana Sosa k'eya da key din mota ya durk'usa yana gaidashi, kallonsa yayi da kasan ido yace "Nuruddeen Ashe ana ganinka? Lallai inaga za a rufe gidan can kadawo nan gaba daya tunda iyayenka ma sai sun nemeka"  dagowa Deen yayi yana kallon Abba yace " Abba kayi hakuri wallahi aiki ne yayi mana yawa tunda baka nan yanzu a wurin sai ya zama dagani sai abubakar Muke tsaye shiyasa koda nake komawa can gidan nagaji sosai, ko jiya asabar ma wallahi muna office dinnan".

Abba gyada Kansa yayi alamar ya gamsu da zancen sannan yace "ka shiga part din Hajiya kanwarka Na Neman ka" lokaci daya annurin fuskarsa ya dauke, ya murtuke fuska kamar bai taba dariya ba, Abba yi yayi kamar be lura yanayin sa ba, mikewa yayi ya nufi part din.

Sama-sama suka gaisa da Hajiyar sannan ya nufi dakin Halima, kofar ya tura ya shiga da sallama.
Tana zaune gefen gado ta amsa sallamar tana yi masa murmushi, sai yaga ta kara ramewa tayi baki kamar ba gida take ba, idonsa suka fara kyallin ruwa, kauda fuskarsa yayi sannan ya zauna kan gadon kusa da ita.
"Yayana kwana biyu ban ganka ba, yau Abba yace ya kira baka daga ba" Shafa gashin kanta yayi yace "kiyi hakuri kinji sauwama, aiki ne yayi min yawa amma kuna raina keda Abba"
Kwantar da kanta tayi gefen kafarsa muryarta Na rawa tace " Muhammad yace in fada muku yana so ya turo iyayensa" wani kallo ya mata yace "waye Muhammad?"
Jikinta yayi sanyi jin yadda yayi tambayar  a hankali tace "lecturer dinmu ne, Baku taba haduwa ba saboda ba a nan kake ba".

Tabe baki yayi ya tada ita daga zaunen da take a kasa yana cewa "babu kyau mace na zama kasan tile haka saboda sanyi, kiringa shimfida sallaya kafin ki zauna ko ki koka can gefen center carpet" gyada kai tayi alamar gamsuwa sannan ta rikon hannunsa tace "Yaya baka ce fa komai ba" wayarsa ya dauko daga aljihu yana cewa "kinsan me zance ai sauwama, zaki iya kiransa ki fada masa, idan yayi yadda nakeso sai yazo muyi magana kafin aje ga zancen iyaye" cike da rashin kwarin jiki tace "to yaya" ganin kamar zatayi kuka yasa shi mikewa ya nufi wardrobe dinta ya dauko mata hijab yana fadin "yau dai dole nakai kanwata shopping" murmushi tayi koba komai taji dadi Dan duk abubuwan da take bukata sun dauko hanyar karewa, haka kuwa akayi komai da take bukata yana tare da ita saida ya siya mata sannan suka dawo gida ya shigar mata da kayan sukayi sallama.

Koda ya dawo gida yamma tayi sosai, daki ya shiga ya zauna yana zubar da hawaye, wannan karon kukan da gaske yakeyi yana dunkule hannunsa yana dukan katifa da bango.

Safiyyah zaman guri daya ya isheta, bata son zuwa bangaren su fadimatu yanzu sai suyita yare kuma ita bata ganewa, Dan haka ta zaga bayan gidan ko zata Dan rage kewa, kamar kuka, kukan mutumin nan, Dan matsawa tayi kusa da window din a ranta tace "sau biyu kenan ina jin kukansa"  samun kanta ta sakeyi da matsawa kusa da window din sosai tana lekawa, sai da tayi dagyal sannan ta hango cikin dakin ta tsakanin labule, gocewa tayi da yasa saida ta dafa wurin gudun kar ta fadi, karar da window din tayi yasa taja baya da Sauri tana toshe bakinta da hannu, da gudu ta bar wajen.
Deen kuwa motsin da yaji yasa shi lekowa amma bai hango ta ba, hakan yasa shi saurin fitowa ya zaga ta dayan gefen Dan ganin waye, amma sai ya samu wurin babu alamar mutum, dawowa yayi yakoma daki ya shiga aikin danna waya, yana tunanin abinda abubakar ya fada masa ranar " kaga da yanzu maimakon waya sai ka latsa matarka" murmushi yayi yana hango kanshi rungume da yarinyar da ko sunanta bai sani ba yana shirya mata kalaman kauna, samun Kansa yayi da daukar key ya nufi gidan Abubakar ko zai yi masa hira mai dadi irinta ranar.

Magajiya na zaune oga daga cikin garadan ta ya kirawo wayarta, tsaki tayi a fili ta furta "tun jiya yake damuna da kira, bari in daga inji mai zai ce" tana dagawa yace "mu bafa kayi mana haka, ya zaki shanyamu fiye da sati daya baki bamu ladan aikinmu ba" wani tsakin ta kuma yi tace "to har yanzu ni kaina jira nake banji komai ba kuma da alama wayan nan mutanen sunyi wasa da hankalinmu, Alhaji Deen ko wayata baya dauka tun ranar jiya da yau ne kawai ban kirashi ba, Dan haka ni yanzu wata hanya nake tunanin mu bullo musu amma Ku kara bani lokaci kunsan tunda Muke aiki daku bamu taba samun matsala ba sai wannan karon" , "mu ba gane hakan zamuyi ba kawai ki nemo mafita in ba so kike mu Cika miki aiki ba" kafin tayi magana ya katse wayar, shuru tayi tana tunanin abinda su indo suke shirin ja mata.

Safiyyah kuwa dakinsu ta shiga tana zare ido, ta samu Indo ta jika tsumma da ruwa tana goge tile din dakin, karba tayi ta karasa, indo ta kalleta tace "me kika fita yi waje?" Dagowa tayi zata bata amsa ta katseta "kimin shuru, kinsan kar in sake gani? Bakiga fadimatu bata zuwa ko ina ba? Iya kacinta nan gefen, tunda kika ga su malam buba sun kama Kansu muma abinda yakamata muyi kenan, wata kila yana daga cikin sharudan mai gidan, kina kina ko?" Ta fada a tsawace, da sauri Safiyyah taja baya tana gyada kai kafin ta saki kuka tana fadin " Dan Allah Anty kiyi hakuri bazan sake ba" saboda bata taba ganin fushin mamanta akanta irin yau ba.

Kyaleta indo tayi tacigaba da kukan Dan tanaso ta gane laifinta, bata son shishshigi, sun samu Allah ya taimakesu dole ne su kiyaye duk abinda zai janyo musu Barin gidan batareda sun shirya ba.

Fitowa indo tayi tana tuk'a tuwo a kofar kitchen din ta jiyo sallamar malam buba ya tsaya daga gefe, ta kwalla kiran sunan Safiyyah bayan ta amsa masa sallamar tana fadin "miko min hijabi na idan kin gama kukan" jikinta a sanyaye ta fito ta bata hijabin ta koma ciki, bayan ta saka ta nufi wurin malam buba suka gaisa.

" dama abinda ya kawo ni akan zancen makarantar Safiyyah ne, nace ko sai dai a canza mata saboda wannan tafi kusa ga kuma saukin kashe kudin tafiya makarantar" tana kallon kasa take amsa masa "to malam nagode sosai gobe insha Allah sai mu tafi tare da ita naji yadda za ayi ko zasu dauketa" gyada Kansa yayi sannan yaci gaba da fadin "sai magana ta biyu mai kamada shawara, ki ringa rakata zuwa makarantar sannan mai gidan nan yana fita karfe bakwai da rabi, ita sai dai ta fita kafin bakwai da rabi ko kuma bayan shi ya fita, yana dawowa karfe biyar, baya dawowa kafin biyar ko bayan biyar idan bai dawo karfe biyar ba sai bayan isha'i ,bana so ta hadu da shi saboda wani dalili, Dan haka sai a kiyaye" kallonsa tayi sai kuma ta sauke kanta kasa ganin irin kallon da yake mata, a hankali ta masa godiya ta koma wurin tuwonta, sai tunanin maganganun sa take, daga baya ta share bayan ta tabe bakinta tayi magana kasa-kasa "kila baya son yaga ana yawan kaida kawo shi mai gidan".

Safiyyah kuwa hankalinta yafi karkata ga tunanin dalilin kukansa, daga tace Abu kaza aranta saitace kaza kamar wacce aka tusa a gaba sai ta kawo dalilin dan dole.

*Safiyyah Galadanchi Ke muku fatan Alkhairi*


RUBUTACCIYAR K'ADDARAWhere stories live. Discover now