BABI NA GOMA SHA BIYAR

725 66 26
                                    

*RUBUTACCIYAR KADDARA*

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
( *home of expert and perfect writers)*💡

*SOPHIE GALADANCHI* ✍🏼

(15)

Komawa yayi ya zauna yana jin yadda ciwon kansa ke karuwa, Sam baya son jin kukan mace, yana tuna masa abubuwa da yawa.

Fitowa yayi ya zaga, sai da ya tsaya daga nesa yana kallon bayanta sannan ya karaso kusa da ita yace "me akai miki kike kuka haka kamar an kwakule miki ido?" A dan tsorace ta juyo tana kallonshi sai kuma ta mike tsaye tana goge fuskarta, batayi magana ba sai da ya sake cewa "dake nake, ina so inyi bacci kinzo nan kina min kuka kin hanani bacci" sai da ta Dan kalle shi ta kasan ido sannan tace "Anty ce ta tafi bata dawo ba kuma kwana biyar tace zatayi" sai da ya kara hade fuska yace "shine sai ki zauna kina kuka haka kamar wata karamar yarinya? Ko nan gidan babu mutane ne sai Anty ce kawai mutum" tayi shuru tana kara yi kasa da kai, ya sake cewa "Nima ai mutum ne kuma kin San ni, ko sai Anty kika sani?" Ta girgiza kai, ya zauna kujerar dake wurin yana cewa "to kiyi hakuri Anty zata dawo kinji" ya fada yana mikewa batare da ya jira jin mai zata ce ba yayi tafiyarsa, ita dinma juyawa tayi tana tafiya tana magana a zuciyarta.

Indo sai da duk ta zaga dangi daga cikinsu wasu sunyi matukar murna musamman dangin mahaifiyarta dangin mahaifinta wasu sunji dadin dawowarta wasu kuwa bakinsu ma bai fadi alkhairi ba, wannan yawon da tayi yasa ta zubar da hawaye, duk abinda take dannewa shekara da shekaru sai da ya dawo mata sabo, farin cikin dawowarta da iyayenta suka nuna kadai yasanyaya zuciyarta, kannenta kuwa mata uku dukansu sunyi aure da namiji guda daya Wanda shine yake binta, sai guda daya itama da ake shirin aurenta shekara mai zuwa, rana daya suka samu suka zo gida, wuni sukayi suna murnan ganin yayarsu, sai dai labarinta wasu daga cikinsu sukaji amma basu ganeta ba saboda dadewar da tayi bata nan.

Deen yau bashida niyyar zuwa aiki sai ma fitowa da yayi waje ya zauna tun bayan da yayi sallar asuba, yana mamakin rashin fitowar safiyyah taje makaranta har takwas saura, kira ya kwallawa malam buba yazo da sauri yace "meya hana waccen yarinyar zuwa makaranta yau?" Malam buba murya Na rawa yace "ranka ya Dade mahaifiyarta ce daga sunan kwana biyar sai da ta kwana goma bata dawo ba, shine tun jiya take kuka yauma kuka take tace bazata je ba" gyara zaman sa yayi yana cewa " jeka kiramin ita" wani irin juyawa cikin malam Buba yayi amma sai ya tafi da sauri dan Kiran Safiyyah.

Tana zaune a kofar dakinsu idonta sunyi zuru-zuru malam buba yazo ya tsaya kusa da ita yana cewa "mai gida yace a kiraki meya Hanaki zuwa makaranta to kiyi takatsantsan" gyada masa kai tayi tana turo baki tayi gaba, inda Deen yake zaune taje ta durkusa tana gaidashi, ya amsa yana fadin "bakya jin magana Ashe? Jeki maza ki shirya ki wuce makaranta banason naga ana wasa da karatu" ya fada yana danna wayarsa, kallon sa tayi idonta cike da hawaye tace "inajin tsoro kar su hanata dawowa saboda ta Dade bata je gida ba" kallonta yayi sosai yace "sun San tanada ke ai dole zata dawo, kije ki shirya da sauri Kinyi letti, Samuel zai kaiki" mikewa tayi ta koma gefensu gabanta Na faduwa, a tsorace ta zauna cikin motar bayan ta gama shiri hankalinta bai kwanta ba sai da taganta a gate din makarantar su, ta fito daga motar tana tunanin yanda akayi yasan makarantar da take.

Tun daga ranar baya fita sai yaga fitar ta wani lokacin ma Samuel yake turowa ya kaita, amma bai taba cewa ta shiga motarsa ba, baya so ya tsorata ta shiyasa yake dan yin abubuwan da zaisa ta saki jiki, da alama kuma ya soma cin ribar hakan.

Yau ma ya rigata dawowa, koda ta shigo Inda yake idonta ya soma sauka, bata San meyasa ba haka nan yau taji dadin samunsa a wurin, sai da taje kusa da shi ta gaida shi ya amsa da "lafiya lau matata" a razane ta dago ta kalle shi sai yayi murmushi yace "ko bakya sona?" Kasa tayi dakanta tana murmushi yayi magana yana cewa "dama akwai Maganar da nake so nayi dake ki nutsu ki saurareni" ya nuna mata kujerar dake kallon sa, ta zauna a dan tsorace, a hankali ya fara magana (bana jin abinda yake fada mata dan Na basu guri suyi sirri amma daga ina hango lokaci zuwa lokaci tana gyada masa kai sai kuma tayi murmushi.

Malam buba ne yake ta famar kumfar baki yana yarfa hannu, safiyya Na zaune tana sharar kwalla har ya gama bata ko dago kai ta kalle shi ba, bayan ya tafi ta soma magana ita kadai tana cewa "ni bazan masa rashin kunya ya koremu ba, ka barni da damuwar da take zuciyata".

______________________________________

Maganar komawarta tayi musu Dan yau ta kai sati biyu kenan, tasan akwai kallo idan ta koma nan gaba ko kofar gida zata sai safiyya ta bita.
Basu ki ta tafi ba amma da alkawarin zasu dawo nan suyi salla ko kuma bayan salla suzo, washe gari sai bayan sallar azahar sannan ta kamo hanya.

Ba karamar murna safiyyah tayi ba data dawo ta samu indo a gida, farin cikinta bazai misaltu ba abinci ma kasa ci tayi, ta zauna tana kallon yadda Anty ta murmure harda sabon kaya ajikinta tace "Anty shine kikaje kika yi kiba? Mantawa kika yi dani?" Indo ta kwashe da dariya tace "kin taba gani uwa ta manta da yar ta? Saboda ke inna tabarni Na dawo, nasan da babu ke banida hujjar da zan bayar ta dawowa garin nan" safiyya tayi murmushi ta sake tambayarta "to Anty ummanki bata ce ina nake ba" sai da ta kalleta sannan tace "Na bar gida kina ciki ai dole a tambayeni ina abinda na Haifa" rungumeta tayi tana murna sannan tace "Naji dadi lokaci na farko a rayuwata da wani daga cikin dangina yasan da zama na, Allah yasa suna son ganina ma" hannunta Indo ta rike tana jin dadin yadda yar ta take cikin walwala tace "sunce muje can muyi salla ko kuma bayan salla muje" tsalle safiyya tayi sannan ta janyo kwanon abincinta ta soma ci tana cewa "mun gama jarabawa, gobe Anty inna kwanta karki tasheni pls" gyada mata kai kawai tayi, ta dan kwanta saboda akwai gajiya a jikinta.

Saura kwana biyu a fara azumi Deen ya soma sadaka, basu wani sha mamaki ba sai da yayo aike na musamman yace Samuel yakaiwa Maman safiyyah, daganan ya kara hura wutar kiyayya tsakaninta da Indo, ga haushin malam buba na yadda yake zumudi, idan yaga Indo ya ringa washe baki kenan yana jera mata tambayoyi akan lafiyarta, safiyyah ma duk abinda ya siyawa fadimatu sai ya kawo mata, ita ma fadimatun saita daina kula safiyyah dama sama-sama suke dan ita bata koma makaranta ba tunda ta gama jss3 dakyar.

Deen ya shiga damuwa sosai dan rashin ganin wulgawar safiyyah duk da kuwa Sabon tsirin daya fito dashi na zama haraban gidan, bangaren safiyyah ma haka take har so take ta samu dalilin da zata bi hanyar suyi magana da Deen akwai abinda take son fada mishi.

Malam buba kuwa bai fadawa Indo yadda Safiyyah da Deen suka dinke ba so yake ya tsoratar da safiyyah dan yasan indai safiyyah da Deen suka yi aure to tabbas Indo ta wuce ajinsa.



*Safiyyah Galadanchi ke muku Fatan alkhairi*

RUBUTACCIYAR K'ADDARAWhere stories live. Discover now