BABI NA GOMA SHA BAKWAI

758 59 10
                                    

*RUBUTACCIYAR KADDARA*

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
( *home of expert and perfect writers)*💡

*SOPHIE GALADANCHI* ✍🏼

(17)

Zaune kawai take tana kallonsu suna aiki tayi shuru, sai tunanin yadda zata koma take.

Innah da duk hankalinta yana kan Safiyyah, kallon kanwar indo Maisuna hafsatu tayi cikin Harshen su tace " hafsatu a lari bingel do sali yoftugo be Amin ko o yida jodugo be Amin on" (Hafsatu kinga yarinyar nan taki sakewa kodai bata son zama damu)?

Hafsatu tace "Inna soinde vowugo on o fertai" (inna rashin sabo ne, zata ware).

Indo dake kusa da Safiyyah haushi ya kamata saboda halin Safiyyah ta kalleta cikin tsawa tace "Saitoh mi feti ma be maraje ndan a fertata"? (sai na kwada miki mari tukunna zaki saki ranki)? tayi maganar itama cikin harshensu, juyowa inna da Hafsatu sukayi suna kallon Indo, basu yi tunanin har yanzu indo ta iya yaren ba balle yarta ta iya.

Safiyyah ma dake gefe zabura tayi ta matsa gefe tana cewa da yaren fillo "Aunty wadu muyal" (Anty kiyi hakuri), tsaki indo tayi tana cewa "do irin buslogo hali toi on do,a hoti sera a hauti yeso yoftu" (wannan wane irin mugun hali ne, kin koma gefe kin hade fuska) sake matsawa tayi kusa da inna ta karbi wukar dake hannunta tana gyara kayan miya, sakar mata inna tayi tana murmushi.
Ajiyar zuciya indo ta sauke tana ci gaba da gyaran alayyahu.

Washe gari da wuri suka tashi aka Dora girki kamar yadda akeyi akowane gida, lafiyayyan tuwon jar dawa sukayi da miyar kubewa sannan sukayi tuwon shinkafa da miyar alayyahu Wanda za'a aika gidajen makota dana dangi, sai da suka Gama sannan suka shirya zuwa sallar idi, Safiyyah sai mamaki take Dan ita bata taba zuwa ba, bata sha mamaki ba sai da sukaje taga mutane kamar kwari, mata da maza, Hafsatu ce take janta duk Inda zata idan an tambayeta wacece sai tace diyar yayarta ce tana ta murna saboda duk garin babu wacce ta iya kwalliya kamar Safiyyah.

Bayan sun dawo suka ci abinci sannan aka sassamusu sukaiwa dangi, duk Inda sukaje sai Safiyyah taga ana hararta ko kuma ana nunata hadi da yin magana kasa-kasa, dakyar taga sun gama yawon sun dawo.

Tunda suka dawo take son yiwa indo magana amma ta kasa ganin harda matar Baffa salihu acikin masu harararta ana mata wani kallo.

Bayan kwana biyu hankalin kowa ya kwanta angama bikin salla indo tajewa Baffa gidado da zancen komawarsu, kallonta yayi sannan ya dauke kansa yana cewa "Aysha bazaku koma ba kunzo kenan, can din wa kuke dashi da zaku koma, idan makarantar Safiyyah ne nan ma akwai Dan haka ki bar wannan maganr" kallonsa tayi sannan ta sauke idonta kasa tana cewa " Baffa aduba mana, kayan mu duka suna can idan nakoma ko kyauta nayi da wasu wasu kuma sai na taho dasu nan" karkace kai yayi yana cewa "kije sai nayi tunani" mikewa tayi tana godiya sannan ta koma dakin inna.

Washe garin sallah Deen ya dawo daga china, sai zumudi yake ko gidansu bai je ba ya nufi gidansa, yana burin yi tozali da Safiyyah, jiya mafarkin da yayi ya masa dari bisa Dari, yana adduar idan Safiyyah ta kasance mata awurinsa Allah yasa yadda yake ji da ganinta a mafarki ta kasance haka, Dan murmushi yayi tunowa da ruwan da yayi wanka da su jiya da dare.

Malam buba yakai masa kayansa Palo yanata jera masa sannu da zuwa, Seen yayi godiya ya shige dakinsa, bai tambayi Malam buba ba Dan baya son yayi wani tunanin, wasa-wasa har dare baiga gilmawar ko dayansu ba, hankalinsa bai tashi ba sai Washe gari da yayi ta maza cikin dabara yace "Malam buba Kunyi salla lafiya ko? Kuma kowa lafiya, kuda wannan yar uwar taku?" Malam buba ya bata rai yace "ai ranka ya Dade sunje gida salla amma ban tunanin zasu dawo ma Dan naga ta kyautar da wasu daga cikin kayanta" hankalin Deen ya sake tashi cikeda gigicewa yace "tafiya babu sallama? Ai zaman tare bai ce haka ba" Malam buba dai shuru yayi yana jin kamar ya kamo wuyan Deen ya shakareshi sai ya daina numfashi, Deen ya sake cewa "babu matsala ai tunda garinku daya" da sauri Malam buba yace "ba garinmu daya ba ranka yadade nima bansan su ba wallahi kayimin aikin gafara gani nayi gani nayi suna Neman taimako" dagowa Deen yayi yana kallonshi, ba wai zancen ba yan uwansa bane ya daga masa hankali, cewar da yayi ba gari daya suke ba, ma'ana dai bai san garinsu ba.

Juyawa yayi ya koma cikin gida, zama yayi kan kujera yana tunani aransa yace "ai tace salla da sati daya zata dawo Dan haka nan zan jira nagani", daga haka yaci gaba da lamuransa yana saka ran zasu dawo baya tunanin zasu tafi ba tare da sunyi masa sallama ba, ba alfahari ba yasan ya taimaka musu yakuma yi musu alfarma, bai cancanci wannan sakayya daga garesu ba.

Gidansu yaje ya samu Abba baya nan bayan ya gaida Hajiya ya wuce dakin Aisha tana salla yajira sai da kammala sannan tazo kusa dashi ta zauna tana cewa "yayana sannu da zuwa" daga mata kai yayi yana cewa "yauwa sannu, nazo Abba baya nan naso muyi maganar Muhammad dinki dashi Dan asaka musu ranar turowa" kunya taji ta rufe fuskarta da tafin hannunta tana dariya, Deen yaji dadin ganin farin cikinta ya riko hannayenta yana cewa "su kunya manya, ai ke kika nuna kina son auren, nidai bari na tafi inaso naje gidan Abubakar bashida lafiya tun da muka dawo" Allah ya kiyaye ta masa yafita.

Yau indo tunda ta tashi gabanta yake faduwa, amma sai ta dauki carbi ta kuma yi addu'a, sai bayan la'asar sannan ta tashi tana cewa Safiyyah, ko zauna ki taya inna aiki, zanje gidan haula na dubo jikinta dazu hafsatu da tazo tace kwana tayi tana amai" Safiyyah ta gyada mata kai duk da bataso tafiyar bada ita ba.
Tunda ta fito takejin kamar an karo mata faduwar gaba amma ta daure taci gaba da tafiya, ita sam bataga mota na zuciyarta nacan wani wurin, sai karar wani Abu taji, daganan kuma bata kara sanin abinda yake faruwa ba.

Wanda yake cikin motar ya fito da sauri yana fadin "Innalillahi wa'inna ilaihiraji'un" mutane suka taru, acikinsu aka samu Wanda ya zura da gudu zuwa gidansu ya fadi abinda yake faruwa, safiyya na tsugune tana gyara itacen murhu taji yadda yaron ke haki yana bawa inna labari, kafin ya rufe bakinsa har takai waje, kanta babu dankwali kafarta da takalmi daya Dan tuni dayan ya cire.

Inna ma cike da tashin hankali ta saka mayafi ta fita, bata hango Safiyyah ba, koda Safiyyah ta isa ana kokarin saka indo mota, jikinta duk Jini, hannu ta dora akai ta fara kuka, sannan ta karasa Inda suke ta rungume ta, dole aka tafi da ita da inna, Baffa gidado yana zaune kofar gidan mai gari labari ya riskesu, anan mai gari yabada mota Dan abi bayansu, hankalin Baffa duk a tashe kansa har ya soma ciwo.

Inna ta cire dankwalinta ta yafawa safiyyah tana lallashinta, sai bayan magrib suka isa asibitin, Sam inna ta manta da wani Abu wai kunyar yar fari, hankali ta yakai kololuwar tashi suna tsaye a kofar dakin da aka shiga da ita, Baffa gidado ma yakasa zaune ya kasa tsaye.

Hankalinsu bai kwanta ba sai da doctor ya fito daga dakin yana fada musu karaya guda ce a kafa sai kananan ciwuka wasu an dinke wasu kuma basai an dinke ba, ajiyar zuciya suka sauke a tare, mutumin daya kade ta duk shi ya biya kudin aikin da aka mata sannan ya siyo magunguna, akace tana bacci idan sai zuwa gobe zata farka.

Sai a lokacin suka hango Safiyyah datayi kuka duk fuskarta ta kumbura, mutumin ya kura mata ido kamar ya santa sai kuma ya share amma abin yana ransa.

Juyin duniya inna tayi akan Safiyyah tabi Baffa gidado su koma amma taki yadda dole Baffa yace a kyaleta.

*Dan Allah Ku saka yar uwata a addu'a Billy galadanchi Allah ya bata lafiya*

RUBUTACCIYAR K'ADDARAWhere stories live. Discover now