*RUBUTACCIYAR KADDARA*
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
( *home of expert and perfect writers)*💡
*SOPHIE GALADANCHI* ✍🏼
(16)
Sosa kansa yayi da biron dake hannun sa bayan ya gama sauraren Muhammad yace "Ni banida matsala Muhammad indai kaji ka gani, bayan haka kuma..." Ya dauko takarda daga cikin drawer din table dinsa ya ajiye a gaban Muhammad yana cewa " wannan dole sai ka saka hannu domin na kafa hujja indai ka sab'a to gaskiya zuciyata bazata iya dauka ba".
Muhammad yayi murmushi bayan ya gama karantawa ya kalli Deen yace "yace wallahi ni Nuruddeen bana daya daga cikin mutanen da kake tunani, bance kar kayi shakku akaina ba amma ina baka tabbacin gani a aikace sai dai kasan halin rayuwa Wanda itama akanta zai iya faruwa" murmushi Deen yayi yace "babu Matsala, takardar nan zaku sake haduwa idan magana taje gaba saboda kafa shaida, nagode sosai" ya fada yana mika Masa hannu suka yi sallama.
Muhammad sai da ya zauna cikin motar sa sannan ya sauke ajiyar zuciya yana tunani, zuciyarsa cike da tausayin Halima, sai yake ganin kamar bata jin dadin rayuwarta, shuru-shurunta har yayi yawa, alkawari a dauka a zuciyarsa na bata kulawa da sakata farin ciki da yardar Allah, wayarsa ya dauka ya kirata, lokacin Tana kwance cikinta na faman ciwo, dagawa tayi amma sai taki magana.
Yace "baki fadamin haka yayan mu yake sonki ba? To ina miki albishir Halimatu sauwama kin kusa amarcewa" dariya kadan tayi tana cewa " yanzu da taku ta hadaku ai kaji kuma kaga yadda yake ji dani" jikinsa yayi sanyi jin muryarta kamar tayi kuka yace "meya faru dake muryarki ta koma haka" saida ta runtse idonta tadanyi huci kadan tace "kadan cikina yake ciwo yau" gyara zamansa yayi yana cewa "ciwon cikin daya maidake haka Halima ba kadan bane, bari na kawo Pampers ko" ya fada cikin sigar tsokana, a hankali tace "Eh" , "dagaske?" Ya tamabayeta ta sake cewa "umm" yayi dariya yace "to zan hado da panadol kafin na iso kisha Lipton mara sugar gani nan zuwa" bai jira jin mai zata ce ba ya kashe wayar.
Dadi taji aranta, dama pad dinta ta akare dama yau da sauran biyu ta tashi kuma saboda tana yawan canjawa duk tayi amfani dasu na jikinta ma ya a takure take jinshi, mikewa tayi tana tafiya a dudduke ta fito, a zaune taga Hajiya Palo ta gaida ita, amsawa tayi murya ciki-ciki sannan tace "yau kinga damar fitowa kenan? Wai har yanzu Halima ba zaki hankali ba? Duk musulmin kwarai ana son shi da tawakkali, ya kasance mai yadda da kaddara amma ke duk kinbi kin kuntata rayuwarki, to ni wallahi bazan ringa lallashinki ba tunda ke ba jaririya bace daga yau kuma kar ciwon ki ya tashi a nemeni tunda ke kike jawowa kanki, sai kiyi ta zama da yunwar har tayi ajalinki" ta maida idonta kan TV da ake news.
Ci gaba da tafiya Halima tayi, ita har yanzu maganganun Hajiya basa mata ciwo, Lipton din ta hado tazo ta koma daki tana sha a hankali harta shanye, dan kwantawa tayi sai kiran Muhammad ya shigo, bata daga ba ta saka hijab din ta ta fita bayan ta fadawa Hajiya zata je wurin Muhammad.
Kamar yadda Deen ya saba daga karfe biyar tayi yake aiko da kularsa dan azuba masa kosai, rana daya ya soma yin haka dan tsirfa da iyayi sai yaji kosan ya masa dadi sai ya waske da aika nasa mazubin kullum, bakaramin dadi hakan yayiwa Indo da safiyyah ba koda zai kawo kular jikinsu na rawa za a zuba masa nasa a aika masa.
Abinda ya sake k'ular da huraira kenan dan tunda take wannan aikin bai taba koda son yaji kamshin kosan bane balle yace zaici, gashi malam buba ma kullum yana cikin yabon Indo akan dadin kosan, huraira kuwa tanaso amma saboda bakin kishi da hassada ko kallon kosan bata yi, sai dai tayi nata daban, idan malam buba yayi magana sai tace ita idan kosai yacika laushi bata iya cin shi.
Ranar jumu' azumi yakai goma sha biyu Safiyyah ta fito zata je siyo zogala, tana fitowa harabar gidan shikuma ya dawo daga aiki sai da yayi parking ya fito daga mota yana cewa " ina zaki je bada izini na ba?" Kanta a kasa tace "Abu zanje siyowa can wurin da ake tafsir din mata", " shi abin bashida suna ne ranki ya Dade?" Ya sake tambayarta, "zogala" ta fada murya kasa-kasa, yana danna wayarsa yace "saboda ke zan shuka zogala, amma yanzu kije Allah ya kiyaye" yana gama fadar haka ya juya itama tafiya tayi batareda taso kara yin wata Maganar ba, dan daga inda suke Indo zata iya hango su tasan kuma zata yi mata fada.
Bayan kwana biyu tafiya mai muhimmanci ta kama Deen wacce bazata wuce kwana biyar ba, suna bukatar kayan aiki a kamfanin su dan haka sai dole yaje China da kansa ya turo kayan sannan ya dawo.
Kasuwa sukaje kamar yadda suka saba shida Abubakar suka siyo kayan da suke rabawa lokacin sallah na yan uwa da kuma ma'aikatan dake company dinsu, zama sukayi suka ware duka kowanne da sunan shi.
Abubakar sai kallon wasu kayan da aka ware gefe yake yana murmushi yasan Bazai wuce na safiyyah bane amma bai yi magana ba.
Bayan sun gama sun dan huta sai Deen ya tura masa kayan gefe yace "dan Allah ka zagaya baya ka bawa Maman su safiyya badan Halina ba" daukar kayan Abubakar yayi yana cewa "dole na tayaka kamun kafa tunda ina so kayi aure" dariya sukayi su duka sannan suka fita bayan Deen ya dauki kayan malam buba da iyalinsa kamar yadda ya saba.
Indo ta zube kayan a daki tana kallon su cike da mamaki ita bata taba ganin kaya mai kyau irin wannan ba, dinkin sallama ai basu taba saka irin wannan ba, sai saka masa albarka take tana kara yi masa godiya.
Bai samu damar yiwa safiyyah sallama saboda washe garin ranar suka tafi, kuma jirgin karfe bakwai da rabi suka bi.
A bakin malam buba suka ji yayi tafiya, safiyyah dake zaune tayi murmushi tana adduar Allah ya dawo dashi lafiya dukda bai fada mata zaiyi tafiya ba amma idan ya dawo sai ta masa korafin haka.
Wasa-wasa Deen sun kusa cinye azumin a can saboda matsalar shipping kaya da suka samu dole zasu k'ara kwanaki a can, bai wani damu ba dan shi dama ba wani dokin salla yake ba, dan bai damu da zumunci ba.
Safiyyah kam tun ranar da aka Cika kwana biyar da tafiyarsa take zuba ido amma taji shuru har ta kasa hakuri tacewa indo "Anty kila mai gidan nan ba anan yake salla ba" indo ta harareta tace "me kuma ya shafe ki da sanin inda yake salla? Kinsan bana son tsegumi ko?" Shuru safiyyah tayi dan dama subutar baki ne.
Sallah saura kwana biyu indo ta tarkata sauran kayan abincin da suka rage bayan ta debi wanda zatayi tafiya dashi ta kaiwa huraira tace "Maman fadimatu, ga kaya nan kiyi hakuri insha Allahu gobe zamuje gida muyi sallah, kwana bakwai nakeso muyi duk da sai na taba makarantar safiyyah, ayi mana gafara" sai da ta yamutsa fuska sannan tace "angode" Indo bata damu ba dan tasan akan mijinta take wannan halin ita kuwa Allah ya gani bala'in k'azantar malam buba take ji, bakinsa duk ya dafe hakorinsa sun koma coffee brown, ga gashin fuksa baya gyarawa, ga faso kafarsa kamar hwadama, ita yaushe zata iya hada shimfida da wannan kazantar.
Washe gari da wuri suka fita suka kama hanya, mai makon safiyyah taji dadin tafiyar sai duk taji bata jin dadi bata dokin tafiyar, hankalin ta duk ya koma kan Deen dinta, a ranta tace "wata kila ma yau zai dawo", indo kuwa faduwar gaba ne ya risketa bayan sun sauka inda zasu hau mortar da zata karasa dasu can garin, har sai taji kamar faduwar gaban tafi wacce tayi lokacin datazo ita kadai.
Murna inna tayi ba kadan ba ta rasa inda zata Dora kanta, kallon safiyyah take kamar zata cinyeta, itace da wannan jikar masha Allah kamar balarabiya, wannan ai duk garin nan ba macen da zata goga da ita wurin kyau.
Baffa salihu kuwa da matarsa sai bakin ciki suke ganin kayan da indo ta kawo, babu Wanda ya nuna alamar ko yaganta, gari ma ya dauka kus-kus kawai ake ai yarinyar nan da ake gani kamar yar indiya da yar gidan Gidado tazo da ita, itace yarinyar data tafi da cikinta, wasu su fadi alkhairi wasu kuma sabanin haka.
Baffa gidado ya kalli indo yace " Aisha kunzo kenan ko babu Maganar komawa? Dan naga kamar kun debo kaya kadan" indo tayi kasa dakai tace "Baffa sati daya zamuyi mu koma dan makarantar safiyyah" kafin yayi magana inna ta karbe da cewa "to ai ko nan garin yanzu akwai makaranta dan haka babu inda zakuje kima bar wannan zancen".
Wannan karon gaban safiyyah ne yayi mummunar faduwa har sai da ta dago ido tana kallon inna ko kiftawa batayi, zuciyarta ta shiga bugawa da sauri.
_Kuyi hakuri kwana biyu kuna jina shuru saboda wani uzurin daya kama. ina muku fatan alkhairi_
YOU ARE READING
RUBUTACCIYAR K'ADDARA
FanfictionLABARIN UWA DA Y'AR TA WANDA YAKE CIKE DA TAUSAYI DA AL'AJABI, KUYI KUTSE A CIKI DOMIN GANIN ABINDA YAKE FARUWA.
