*RUBUTACCIYAR KADDARA*
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
( *home of expert and perfect writers)*💡*SOPHIE GALADANCHI* ✍🏼
(13)
Sai da aka yi mata kwatancen gidan sannan ta kama hanya, ita da gidan ubanta amma ace sai ta yi tambaya amma kam akwai kunya.
Bugun zuciyarta ya karu lokacin da ta isa kofar gidan, tana tuno abinda ya faru ranar data bar gidan, a hankali ta yi sallama sannan ta shiga, tsaye tayi tana kallon Inna dake gaban murhu tana dafa madarar shanu, hawaye suka zubo daga idonta.
Inna ma wani irin faduwar gaba ya riske ta, sai taga kamar tunanin da take faman yi ne yake sata ganin ba daidai ba, har ta juya kuma sai taga indo ta durkusa, da sauri ta matsa kusa da ita ta riko fuskarta da dukkan hannanyenta.A hankali indo tace "Inna Ashe zan sake ganinku?" Batare da inna ta amsa ba ta kwalla kiran Baffa Gid'ad'o wanda ya janyo hankalin mutanen gidan, duk suka fito suna kallon su, inna ta kalle shi tana fadin "Baffa Aishatu ce ta dawo, Aisha ce a gabana, Ashe bata mutu ba" murmushi yayi yana kallonta yace "Alhamdulillahi, Allah na gode maka daka dawomin da y'ata gida, Allah na gode maka daka tsaremin Aisha badan halin mu ba" hannun indo ya ja ya zaunar da ita kan tabarma, suka zagayeta suna kallonta.
Inna tace "haba Aisha sai ki manta da iyayenki saboda abinda ya faru? Baki mana adalci ba, munshiga cikin tashin hankali indo" indo ta share majina sannan tace "inna nayi tunanin kona dawo bazaku karbe ni ba shiyasa" shuru inna tayi kafin
Ta tashi ta kawo mata abinci takai mata jakar ta daki sai nan-nan ake da ita, Baffa ma sai kallonta yake bakinsa yaki ruhuwa.Ranar data tafi safiyyah kasa bacci tayi, ta kwana tunanin yadda indo ta isa gida, sai kuma zuciyarta ta tuno mata da yadda suka hada ido da mutumin nan jiya, murmushi tayi tana gyara kwanciyarta.
Washe gari ma da sassafe ta shirya zuwa makaranta tana ta sauri a tsaitsaye tasha kunu ta fita.Deen yau sai takwas ya fita jikinsa duk a sanyaye, yauma mafarkin Safiyyah yayi sai duk yaji yana muradin abin dan haka ya dauki azumi dan baya so ya koma ruwa," Allah yagani har addua nake in zan kwanta amma wannan aljanar sai tasan yadda tayi ta hada shimfida da ni a mafarki" ya fada bayan yayi parking a ma'aikatarsu.
Bayan azahar ya wuce office din abubakar ko zai samo masa malamin da zai masa rukiya.Wata irin dariya abubakar yayi har saida ya fadi kasa yana fadin "wallahi Deen ka kusa haukacewa" Deen yaja dogon tsaki yace "nazo Neman Abu ka tsaya kana yimin dariya wallahi zan tafiya ta" abubakar ya tsagaita da dariyar sannan yace "kodai itace a gidanka? inaga ka saka ido dai tunda har sau biyu kana ganinta wata Kila a dace".
Gyada kai kawai Deen yayi sannan ya masa sallama ya koma office dinsa.
Indo na zaune gaban Inna da Baffa, Inna tace " Indo to ina labarin cikin da kika tafi dashi?" Indo tayi kasa da kai a hankali tace "Safiyyah ce, tana can na baro ta, bansan ya zaku karbe ta ba shiyasa banzo da ita ba" hawaye suka zubo daga idon Inna muryarta na rawa take fadin "bamu da dabara, bamu isa mu hana abinda Allah ya rubuta sai ya faru ba amma muka kasa gano hakan a wancen lokacin" Baffa ya dubeta yace " hakane saudatu ki kuma fada mata abinda ya biyo baya, bayan tafiyarta" inna ta riko hannun indo ta sake cewa " tun bayan tafiyarki indo Maimota ya zo garin nan yana Neman ki, ya yadda da kuskuren dayayi yayi kukan rashin sanin inda kike, cikin da kika tafi dashi ya kwallafa rai akansa duk burinsa ya kare akan abinda kika haifa, bai daga kafa daga zuwa garin nan ba indo sai shekaru uku da suka wuce, rashin sanin inda za a fara neman ki shine babban abinda yafi daga hankalin mu, tun muna kukan ido har muka koma yin na zuciya, Maimota bai taba haihuwa ba sai akan cikinsa da yake jikin ki gashi lokacin da kika dawo ya dauke kafa shikuma" tunda aka ambaci sunan sa take kuka har inna ta dasa aya, sannan ta dago tace "inna inajin tsoro Safiyyah tasan komai, inajin tsoro na manta ko wacece ni na kuma manta ko wacece Safiyyah, bayan abinda ya faru, na bar garin nan ba tare da nasan inda na nufa ba, babu wani kauye a kusa damu inda zan zauna koda zanji labarin kuna nema na, ban taba cire rai da cewar zaku kirani na dawo ba sai da na ganni a inda banida kowa banida komai, bayan na hau mashin din naje inda zan hau mota, na Shiga motar batareda nasan kudin mota koma inada su ba, sai da aka soma tafiya sannan aka ce kowa ya kawo kudinsa, sai tunanin ya fado min dan bayan kudin dana hau mashin naira goma ta ragemin sai da wani bawan Allah ya taimaka ya biyamin, a tasha da muka sauka kowa ya kama gabansa aka barni ni kadai a wurin ga dare yayi dan har sallar magriba anyi, wata rumfa naje na zauna Ashe wurin wata mata ne mai siyar da abinci, har ta gama tattara kayanta zata wuce ban motsa ba, ta tambaya ni me nakeyi kowa ya watse, anan na fada mata ni bakuwa ce bansan kowa ba, sai da tayi tunani sannan tace inzo mu tafi, banyi tunanin zata cutar dani ba saboda zuciyata a bushe take, koda mukaje gidan Ashe ita magajiyar karuwai ce ban damu ba, domin munyi da ita cewar zan ringa yi mata aikin gida da wurin siyarda abincinta bayan haka kuma domin na tsayu da kaina zan ringa yi musu wanki da guga, dukda ba iya gugar nayi ba amma wanki bazai gagareni ba, rayuwarmu lafiya lafiya har nayi sati biyu sai ta hango alamar ciki a jikina, anan ta shiga yimin tambayoyi ban Boye mata komai ba domin itace komai da kowa nawa, ta bani shawarar a zubar da cikin jikina sannan na afkawa sana'ar karuwanci, batareda nayi wani tunani ba naki amincewa, bata takurani ba ta barni da rayuwata inda bazan cutar da ita ba, babu aikin dana gagara yimata ina Tara kudi a wurin ta har cikin jikina ya shiga wata Tara, a lokacin makocinmu Wanda gidan sa yake hade da gidanmu yaji bazai iya makotaka da gidan da Muke ciki ba dan haka ya saka gidan a kasuwa, magajiya ita ta siya gidan sai muka koma ciki, naji dadin hakan domin bana fatan abinda zan Haifa yayi shaawar irin wannan rayuwar, hankali na ya tashi ganin mace na Haifa har ina jin tsoro ina ganin kamar bazan iya riketa ba, magajiya ita ta siya ragon da aka radawa Safiyyah suna da kudina da suke hannunta, duk abinda akeyiwa jariri aka yi mata, bamuda wata matsala har safiyya takai shekara goma sha hudu da yan watanni, asirinmu ya tonu saboda ciwon magajiya har takai ina Allah-Allah in samu wanki da guga domin siyan mata kudin magani amma Allah bai yadda ta rayu bayan lokacin daya debar mata ba, haka ta rasu ta barmu, bayan kwanaki da mutuwarta aka nada sabuwar magajiya, itace silar shigarmu tashin hankali domin ta dauki alwashin saka ni karuwanci har tana yi mana barazana da rayuwarmu, abinda ya tsorata mu kenan muka tarkata muka bar gidan batareda munada wurin zama ba, a wani gida muka samu taimako inda mai gidan ya bamu wurin zama, nayi niyyar zuwa kafin lokacin amma kudin mota ya gagareni, sai bayan mun samu nutsuwa, safiyyah taso nazo da ita amma bansan ya zaku karbe ta ba shiyasa nace ta bari har suyi hutun makaranta zan zo da ita". Koda takai karshen labarin inna da Baffa hawaye suke, rayuwar yar su a gidan karuwai, wannan yana daya daga cikin babban kuskuren da suka tafka.
Deen washe gari karfe bakwai da rabi ya fito da niyyar zuwa office amma sai ya tsaya yana amsa waya a mota, a lokacin Safiyyah ta fito cikin uniform dinta zata je makaranta bata lura da motarsa a wurin ba sai da ta iso kusa da ita, waya a kunnensa amma bayajin abinda mai maganar yake cewa, ido, baki da hanci duk safiyya suke kallo, itama tsayawa tayi jikinta na rawa kafin daga baya tayi sauri barin wurin, baiyi azamar binta ba sai da ta fita, sannan yayi horn malam buba ya fito da sauri ya bude masa gate ya fita, gabansa yayi wata irin faduwa hango safiyya dake tafiya a ransa yana adduar Allah yasa basu hadu da mai gidan ba.
YOU ARE READING
RUBUTACCIYAR K'ADDARA
FanfictionLABARIN UWA DA Y'AR TA WANDA YAKE CIKE DA TAUSAYI DA AL'AJABI, KUYI KUTSE A CIKI DOMIN GANIN ABINDA YAKE FARUWA.