*RUBUTACCIYAR KADDARA**HASKE WRITERS ASSOCIATION*
( *home of expert and perfect writers)*💡*SOPHIE GALADANCHI* ✍🏼
Page 22
Sai ya boye faduwar gabansa, da ba a hannun Halima ya ganta ba seya ruga da gudu dan ya tsorata da ganinta.
Kujera ya nema ya zauna yana murmushi, Halima tace "ka ganta yaya kalli gashinta" kallon Safiyyah yayi yace "masha Allah, kanwar mu sannu da zuwa, da kin daura dankwali da munyi hira amma idan kika zauna kusa dani ba dankwali sena rankwashe ki" kasa tayi da idonta tana murmushi sannan tajuya ta shiga daki, dafe gefen zuciyarta tayi sai kuma taji babu dadi, tana sonshi gashi kuma Ashe yayanta ne.Hijabinta ta saka sannan ta fita Palon kusa da Aisha ta zauna tana gaidashi, amsawa yayi yana kallonta Halima tace "yaya bari inje inyi wanka na kwaso ranar makaranta" gyada mata kai kawai sannan ya maida dubansa ga Safiyyah yace "haka akeyi? Sai Ku tafi baku yiwa mutane sallama ba, kin kuwa San halin da na shiga" tana wasa da yatsun hannunta tace "Kaine baka dawo ba da kayi tafiya, dama zamuje salla gida, da mukaje sai su Baffa suka hanamu dawowa sai kuma mota ta kade Anty har ta samu karaya a hannu shiyasa duk muka daina maganar dawowa, Wanda ya kade anty Ashe abokin Abba ne shine yakai shi kauyenmu daga baya sai Abba yace zan dawo nan da zama inkoma makaranta" gyada kansa yayi yace "Allah sarki, Allah ya kara kiyayewa, yanzu sai maganar aurenmu ko"? Da sauri ta dago tana kallonshi.
Dariya kadan yayi yace " Abba bai taba haihuwa ba sai a kanki, ki tambayi Halima naga kin zuba min wannan idon naki kamar na mujiya" duk yadda takai ga kawaici sai da ya jiyo ajiyar zuciyarta wallahi taji tsoro da farko, tana tunanin duk yadda take sonshi sedai su kalli juna daga nesa.
Hajiyar gidan kullum ta yafa mayafi bata dawowa sai dare, Abba kuwa babu ruwanshi da ita tunda ta tsiri tijara ya zuba mata ido, babu abinda yasa gaba yanzu irin gyaran part dinda Indo zata zauna, daki uku ne da palo biyu, sai kitchen da tsakar gida, duk hankalinsa yana kan auren da zai kara.
Sai yau da zata fita ta lura da gyaran part dinda yake taja dogon tsaki tace "wahalalle kawai, dakai da ita duk zaku sani".Duk bidirin da ake na daurin aure bai fadawa su Safiyyah ba, ranar da aka daura aure sai dare ya shigo ya kirata ita da Halima ya shiga bangaren daya gyara tare dasu, lokacin da Safiyyah tayi ido hudu da Anty da sauri ta karasa kusa da ita ta rungumeta.
Kunyar duniya ta kama Indo ta kasa magana sedai ta janye jikinta dama tunda suka zo batayi magana ba dan kunya yadda Abbansu yaje ya daukota ya hana azo da kowa wai sai an kwana biyu zai turo azo a daukesu.
Anan ya barsu yashiga dakin dayake nasa, kadan Indo ta saki jikinta sukayi magana Halima sai kallonsu take kamar ta sace su, aranta tace " Duk Wanda ya rayu tareda iyayensa shine dan gata, ita yanzu data fi bukatar wannan soyayyar sai Allah ya karbi ran uwarta" hawayen da suka zubo tayi saurin gogewa, ta riko hannun Safiyyah tana cewa "kanwata mubar Anty tayi bacci ta huta, muje mukwanta muma" binta Safiyya tayi tana yiwa Anty bye-bye.
Daga bakin kofa yatsaya yana kallonta sannan yace "idan kingama tunanin zamu kwanta ko" wayyo inama kasa zata stage ta shige ciki, tunda suka kamo hanya yake mata zantukan da suka girmeta, itafa batada banbanci da Safiyyah yanzu saboda bata taba zaman aure ba sai wannan karon idan yayi wani abin sai taji duniyarta na juyawa, mikewa tayi a hankali taje kofar dakin, matsawa yayi ya bata hanya ta shiga ya rufa mata baya, to daga nan nidai ban karasa ciki ba saboda abin na manya ne na dai tsaya daga waje koda wani taimakon inzasu nema.
Sun gama shirin kwanciya sai Safiyyah ta kalli Halima tace "yaya halima, nikam inaso na tambayeki, meyasa yayanmu duk lokacin daya zauna shi kadai yake kuka ne? Nasha ganinsa yana kuka kamar wani Abu na damunshi" Halima ta kalleta bayan ta tashi zaune tace "kafin kizo nan gidan kinsan yayanmu ne"? Zaro ido Safiyyah tayi sai kuma ta dawo normal tace "nasanshi, lokacin da muke Neman gidan da zamu zauna kafin mu koma kauyensu Anty yaya ne ya bamu daki a gidansa ta sanadin mai gadinshi" ajiyar zuciya Halima ta sauke tana cewa "Allah sarki, hmm Safiyyah abinda ya faru da rayuwarmu ne yake ta ba yayanmu, Abba kanin mahaifinmu ne, kusan tare suka girma sannan duka kasuwancinsu a tare sukeyi, duka iyayenmu yan nan garin ne mamanmu tanada yaya dake aure a kaduna, wani lokacin mukan ziyarce ta musamman lokacin Hutu Abbanmu shi yake kaimu ya kuma koma ya dauko mu tareda yaya saboda yaya daya fara girma sai ya daina binmu sedai su kaimu tare ko su dauko mu, zuwan mu na karshe kaddara ta afka kan mu, saboda mota ta lalace mana bayan mun baro zaria, kafin a gama gyara magriba ta gabato, dan haka mukayi dare a hanya, muna tafiya yan fashi suka tare mu, bayan sun karbi duk abinda yakeda muhimmanci a wurinmu sai suka nemi yin lalata dani hankalin Umma ya tashi sai ta rikeni tana rokonsu har suka soma ja-inja da ita babbansu a take ya harbeta a kai tafadi kasa babu rai, nikuma daya daga cikinsu ya kwantar dani a kasan yake ta min haddi a gaban Abba da yayanmu, bansan halin da ake ciki ba sai farfadowa nayi naga yayanmu akaina yayi kuka kamar zai mutu, Ashe har an kwana biyu, bayan sun sakemu su Abba suka dauko gawar Umma da tawa suka kamo hanya duk a zatonsu Nima na mutu, koda muka iso sokoto dare yayi sosai, abiti aka wuce damu sai aka samu inada rai shikuma Abba dama yanada hawan jini ciwon da yayi ajalinsa kenan bamubar asibitin ba sai da aka fita da gawarsa, munyi kuka sosai saboda babu Wanda ya taba kawowa su umma mutuwa sai gashi a rana daya sun tafi sun barmu, nikuma sunyi min illar da har duniya ta nade bazan taba warkewa ba, haka ma yayan, bayan mun dawo gida ni sai aka kawo ni nan gidan Abba shikuma yayanmu sai yaci gaba da zama a gidan mu, idan kin lura banbancinsu kadan ne da wannan gidan, yayanmu na lura ya soma bin mata duk da bamu taba zama dashi ko mun gani da idonmu ba amma yanayinsa ya nuna, sai naga kamar iyayenmu basuyi dacen yaya nagari ba, kema da kikace kinsan shi sai naji gabana ya fadi idan ba zuwa yayi ya lalata ki ba, kamar alkawari ya dauka, mai gadin gidan sa ya taba zuwa ya kawo kararshi wurin Abba dai abban ya masa fada sosai yace ya daina duk da bansan anyi ba Hajiya tazo ta fadamin, tun daga lokacin baya yadda da namiji yazo Neman aurena sai yace seyaje yayi bincike yasan koni wacece idan yaji zai iya to zai nashi aurena amma sai ya saka hannu akan takarda kan Cewar bazai taba wulakanta ni ba, dayawa sun tafi saboda bazasu iya auren macen da ba budurwa ba amma Muhammad shiga dage ya kuma yadda da duk sharadin, wannan shine sanadin kukan da yaya yake yi kullum kuma naga canji a tare dashi kasancewar yakan bata lokaci awurin aiki sannan yana shigowa nan gidan ba kamar da ba, Safiyyah tunda nazo gidan nan Hajiya ji take kamar ta kasheni, bata taba fadar kalma mai dadi akaina ba, inada cutar ulcer haka zanyi ciwo har na warke bata taba zuwa ta duba ni ba sannan kuma ga kadaici har sai da yaso ya taba min zuciya, sai Abba yayi tunanin maida ni makaranta, wannan shine abinda ya faru" haka nan sai taga Safiyyah ta Dora kanta kan cinyoyinta tana kuka sai suka soma kukan dukansu babu Wanda ya sake magana har bacci ya dauke su.
Lallai rayuwarsu abin tausayi ce.
_ina ci gaba da yimuku fata na alkhairi_
YOU ARE READING
RUBUTACCIYAR K'ADDARA
FanficLABARIN UWA DA Y'AR TA WANDA YAKE CIKE DA TAUSAYI DA AL'AJABI, KUYI KUTSE A CIKI DOMIN GANIN ABINDA YAKE FARUWA.