SHAFI NA BIYAR

936 62 0
                                    

*RUBUTACCIYAR K'ADDARA*

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
( *home of expert and perfect writers)*💡

*SOPHIE GALADANCHI* ✍🏼

(5)

Lokacin da indo taga har tara da Rabi ta kusa babu alamar Safiyyah zata dawo sai ta shiga wani tunanin a zuciyarta tace "anya babu hannun magajiya a wannan halin da muke ciki?" Sai kuma ta tuna da zato zunubi koda ya kasance gaskiya tayi saurin yin istigfari sannan ta juya ta shiga gida.

Tsayawa tayi tsakar gida tana tunanin mafita amma sai taji takon takalmi tayi na kafafu da yawa, juyawa tayi ta kalli kofar sai ganin magajiya tayi da gardawa su biyu, gabanta ya fadi ta zaro ido waje tana kallon su.

"Ku masu taurin kai keda y'arki ko? Dama na fada miki ba ayi mana gardama, nayi lallashinki na baki shawara amma duk a banza, wannan karon na shirya karawa dake" ta fada tana kallon cikin idon indo sannan ta kalli garadan tace "gatanan Ku tafi da ita sai na nemeku" sannan ta sake yin murmushi tace "au Ashe ban fada miki yarki na wurina ba ko? To ki kwantar da hankalin ki tana hannuna, sana'ar da kika kyamata aciki zan dulmiya ta domin nima na samu tawa biyan bukatar".

Tashin hankali ya bayyana karara a fuskar indo jikinta ya dauki rawa idonta ya kafe wurin kallon magajiya amma kalma daya ta kasa furtawa lallai duk abinda ake iya yiwa kuka to ba babba bane, idonta a kekashe yake batajin ma akwai alamar ruwan hawaye a ciki.

Juyawa magajiya tayi ta bar gidan, yayinda suka shiga kokarin fito da indo, ba karamar daga suka sha ba kafin suyi nasarar sakata a mota, kasancewar dare ne babu wanda ya lura da abinda yake faruwa sannan kuma unguwa ce ta masu zaman Kansu babu wanda ya damu da wani kowa harkar gabansa yake yi.

Fitar su da mintuna talatin aka dawo da Safiyyah gidan ta tarar babu indo a gidan.
Wannan kenan.

Kuka Safiyyah ta ci gaba da yi  a kofar gidan tana durkushe, ji tayi an dafa kafadunta an tada ita tsaye, dagowa tayi taga waye sai ta ci karo da fuskar magajiya, a hankali ta sauke idonta kasa.

Hannunta magajiya taja ta shigar da ita cikin gida sannan ta kalleta tace.

"Gaki kyakkyawa, ga ki da diri, komai naki mai kyau bakya tunanin wannan shine jarinki? An kaiki wurin hamshakin mai kudi kinki yarda dashi, first night kike tsoro? Na tabbatar zai mantar dake wannan zafin, kuma zafi ne na dan lokaci saga anyi na farkon akayi na biyu ke da kanki zaki nema a na ukun".

Kunya ta kama Safiyyah hadi da bakin ciki ta rasa me zata ce sai tayi kasa da idonta tana Jan majina.

Magajiya ta ci gaba da cewa " kindawo kinsamu Antynki bata nan, to zan yi amfani da ita domin na samu biyan bukatata, dan haka nasa aka dauketa" dariyar manya tayi sannan tace "kina mamaki ina fada miki duk ni nayi wayan nan abubuwan ko? Bana tsoron ki kaini police station, akwai wayanda nasa suke bibiyarki idan kikayi wannan kuskuren to zasu fadawa wanda Antynki take hannun su kuma na basu umurnin su kashe ta, haka zalika kema, idan har baki amince da wannan mutumin ba zakisha mamakin abin zai biyo baya, yanzu shawara ta rage gareki" ta kai karshen zancen tana tabe baki da daga kafada sannan ta fita daga gidan.

A fili Safiyyah ta furta " Anty saboda ni kike cikin wannan mummunar tashin hankalin, idan zan kubutar dake sai na sabawa mahaliccina, saina ba da kyautar abinda bazan taba sake samun sa daga baya ba, saina bada mutunci na a inda ya haramta, Allah gani gareka Allah ka bani mafita ka karemin uwata" ita dinma ta kasa yin kukan sai ji da tayi makoshin ta ya bushe sosai, samun wuri tayi ta zauna tana tunani fiye da Minti goma sannan ta tashi ta shiga daki, uniform din jikinta ta cire ta saka Riga doguwa ta atamfa da hijab ta fito ta kwashe abinci dake zube a kasa sannan ta fita hadi da rufe gidan.

Batada wata mafita illa tabi hanyar da zuciyarta ta nuna mata, dan bazata juri ana gallazawa uwarta ba, da wannan tunanin ta kama hanya saidai bata San sunan unguwar ba ga dare yayi, adaidai sahu ta tare bayan ta iso titi tayi masa kwatancen iya inda zata gane, a take ya fahimta domin shi dan gari ne bakin layin ya sauketa ta bashi kudin sa sannan ta taka da kafa zuwa gidan.

Wani irin tsoro ya risketa jin unguwar shuru ko kukan tsuntsaye babu, sauri kawai take tana ganin gidan ya mata nisa.
Ta kusa isa kenan taji an riko hannunta, tajuyo a firgice ta kalli wanda ya rike mata hannu, gabanta ya fadi ganin namiji yana tangadi da alamar yasha ya koshi, iya karfinta tasa ta kwace hannunta sannan ta falla da gudu sai kofar gidan, tana zuwa ta hau bugun kofar amma bataji alamar wani mutum a kusa ba takai Minti talatin a wurin amma shuru a hankali ta koma gefe ta tsuguna tana kuka.

A lokacin mai gadin gidan yasan babu wanda yake zuwa gidan irin wannan lokacin mai gida ya dawo yayi shigewarsa, shikuma mai gadin ya zaga wurin iyalinsa da dakinta yake bayan gidan kuma akwai tazara tsakanin gate da gidan dan haka acikinsu babu wanda yaji bugun gate din da take dama gata da siririn hannu.

Dan matsawa tayi ta shige rumfar gate din, danfa tayi alkawarin bazata koma gida ba saita tabbatar uwarta ta kubuta daga wannan mugun hannun na magajiya, ta zaune a wurin tayi tagumi wani wahalallen bacci ya dauketa har batasan lokacin data yi kwance ba a wurin, sanyin Safiya ne ya farkar da ita ta tashi tsaye tana rarraba ido, daga kofar wani gida ta hango randa gefen masallaci, ledar ruwa ta nemo pure water sannanntaje wurin randar ta daurayeta ta zuba ruwan aciki ta dawo kofar gidan tayi alwala, dankwalinta ta shimfita tayi salla, a wurin taci gaba da zama tana ta zancen zuci.

Mai gidanne ya fito karfe bakwai da Rabi zai tafi office mai gadi ya bude masa gate ya fito, yayi mamakin ganin mace ta juya baya tayi zaune a kasa tsaki yayi yana cewa "kaga mutum da lafiyarsa amma yana bara" shuru yayi yana tunanin sauri yake yanzu ma kuma baya tunanin dawowa da wuri saboda akwai aiki sosai a gabansa yau dinnan.

Ko da Safiyyah ta Ankara har motar tayi nisa ajiyar Zuciya ta sauke sannan ta koma tana kallon mai gadin zata masa magana, tsaki yayi yana girgiza kansa yace "Allah ya wadaran naka ya lalace yan Matan yanzu su suke bin maza da Kansu" daga haka ya karasa rufe gate din yabarta a tsaye.

A wurin ta wuni har dare tana jiran mai gidan yadawo domin shi take son gani, bata so takai yar yanzu bata San halin da Anty take ciki ba.

Indo kuwa tunda suka tafi da ita awani babban store suka kaita kamar ma an Dade ba ayi amfani dashi ba suka wurgata ciki, kayane a jibge sunyi kura yanar gizo duk ta baibayi su, ga hannunta a daure an kuma toshe bakinta, hawaye kawai take ta zauna a wurin tana addu'ar Neman tsari daga mugun mutum ko Aljani, da kuma muguwar dabba.

A daure ta kwana, kwanan wahala.

Yunwa ta soma galabaitar da Safiyyah dan har jiri take gani, ruwan randar da take alwala almajirai masu yawon bara sun karar dasu ma balle tasha, bakinta ya bushe sosai idonta sunyi zuru zuru.

Hadari ya hadu sai iska ake tana kwance a wurin, har a kwancen da take ma gani take duniya na jujjuyawa, mai gidan ya dawo tana kallo aka bude masa gate ya shige baima lura da ita ba sbd tayi lungu, jikinta ya soma rawa saboda yunwa amma batada karfin furta ko kalma guda, aka fara iska mai karfi dakyar ta juya fuskarta gefen bango ta kama jikinta sosai, tana haka aka fara tsuga ruwa dukda rumfar dake wurin hakan bai hana feshin ruwan tabota ba, tun yana tabata kadan har ya zama batada banbanci da wanda yake  afili ruwan na dukansa, atake sanyi ya kamata kafin wani lokaci bazata ce ga wanda yake kanta ba, a some ta kwana.

Da sassafe kamar jiya Deen ya fita danshi yama manta dayaga wata jiya a wurin, Yau ma din sauri yake karfe tara zasuyi meeting.

Mai gadin ya fito da niyyar share wurin saboda sharar da iska ta kwaso yayi turus yana kallonta, da sauri ya koma cikin gida yana kwalla kiran matarsa da yarsu. Da sauri suka fito yace "kuzo kugani wani ikon Allah" da sauri suka bi bayanshi hankali a tashe suke kallonta matarshi tayi karfin halin zuwa kusa da ita tana taba jikinta, ta kalli y'arta tace "Fad'imatu debo ruwa".

Mintuna kadan ta kawo ruwan aka yayyafa mata amma shuru bata motsa ba.

Matar mai gadin ta kalli fadimatu tace " zo ki kama min ita mu shiga da ita gida" da sauri yace " bakida hankali, wannan daga gani tana cikin yan iskan Matan nan na Alhaji, waya sani ma ko ciki yayi mata shine tazo wurinsa yaki saurarenta".

*Safiyyah Galadanchi ke muku fatan Alkhairi*

RUBUTACCIYAR K'ADDARAWhere stories live. Discover now