*RUBUTACCIYAR KADDARA*
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
( *home of expert and perfect writers)*💡*SOPHIE GALADANCHI* ✍🏼
_Ina jin dadin comment dinku ina kuma fatan zaku kara himma wurin yin comment, kamar nafi tunanin shine zai kara bani karfin gwiwa Dan yafi kama da kuna tare dani, nagode_
(11)
Sosai suke jin dadin gidan, duk da kan indo yana daurewa akan sana'ar daya dace tayi, bataga amfanin zaman da take yi haka ba Dan tana takamar tana samun abinci, yau da gobe bata bar komai ba, akwai abubuwan da suke bukata, tunanin Neman mafita ya soma cin karfin zuciyarta da kwakwalwarta, Sam babu alamar wata karamar Sana'a zata yi kasuwa a wannan unguwar, duba da cewar unguwace irinta manya babu talakawa kamarsu a nan sannan batada jarin da zata yi babbar Sana'a.
Sallamar Safiyyah ce ta katse mata tunani, ta amsa sallamar tana kallonta, sai taga yarinyar ta kara girma yanzu, dole ne zatayiwa Allah godiya daya azurta ta da samun wannan y'a shine mafi sani akan abinda yafi dacewa da zama alkhairi a wurin bayinsa.
"Anty ina wuni, na sameki lafiya?" a hankali ta amsa da "lafiya lau Safiyyah, ya makaranta?" Gyara zamanta tayi tana fadin " lafiya lau Anty" sai kuma tayi kasa dakanta bakinta na motsi alamar akwai magana.
Indo tace "yanaga bakinki na motsi kinayin kasa dakai kamar kinga surukar ki" dago kai tayi idonta sunyi rau-rau suna kyallin ruwan hawaye, muryarta na rawa tace " Anty dan Allah kiyi hakuri, meyasa mu bama zuwa wurin danginmu suma basa zuwa wurin mu, kuma bakya bani labarin...su da kumaa babana, ban San komai akanshi ba sai sunan shi kawai dana sani" ta karasa maganar gabanta yana faduwa kafin ta sake kallon indo sai taga itama hawaye take tana kallonta.
Gabanta yaci gaba da faduwa sannan a hankali tana kuka take fadin "Banida amsa ko daya da zan baki, bansan mai zan ce miki ba, amma nayi miki alkawarin duk ranar da na tafi dake garinmu zaki ji komai, kinada dangi kamar kowa, sai dai banida masaniya ko babanki yana nan duba da lokacin Dana deba banje gida ba, karkisa wani tunani a zuciyarki kinji".
A hankali Safiyyah ta sauke ajiyar zuciya ta zauna kusa da indo tana cewa " kiyi hakuri Anty na saka ki yin kuka, wata magana naji a makaranta sai naji kamar dani ake kamar anyi min gori" Shafa fuskarta indo tayi tana murmushi dan yadda zuciyarta ke mata zafi bazai barta tayi magana ba.
A yanzu sun dauki kwanaki fiye da arba'in a gidan kuma komai lafiya lau dan mai gidan yana saki kamar bai San zafin kudi ba, Deen kuwa bashida damuwa dasu dan ko kadan basa takura masa, basuda hayaniya kamar babu kowa a gidan ma, Abu daya ne yanzu yake damunsa shine rashin sanin hanyar da zai sake ganin yarinyar nan, zuciyarshi taki yadda da kiran magajiya a lokacin sai daga baya yayi shahadar kiranta amma wayarta bata zuwa (abinda ya faru da magajiya kuwa shine) lokacin da Oga ya kirata akan zancen kudinsu ta bashi hakuri bayan sati biyu bata bullo da wata hanya ba domin Deen sananne ne kananan garadanta basuyi jarumtar zuwa su tunkareshi ba, tana jin tsoron akama su suyi zaman fursuna, wannan yasa bata dauki wani mataki ba, Oga Tiger kuwa bai yadda da asaraba danshi Neman abin duniya ne yasaka shi dulmiyar da Kansa cikin wannan sana'ar dan haka bazai dauki asara ba, kamar yadda suke dauke mutane haka suka dauke magajiya, sai da ta kwana biyu a wurin su sannan ya dawo da ita bayan ya gama morarta, ya kuma jaddada mata wannan bugun lamba ne dan haka yar yanzu suna jiran kudin aikin su, tsorata da tayi yasa ta kwanta ciwo na yan kwanaki sai dai Deen bashida labarin bayan ya daina kira magajiya ta dawo ta kuma ci gaba da sana'ar ta.
Tashi yayi ya janyo wayarsa dan duba lokaci yaga shabiyu da Rabi yanzu, mafarkin Safiyyah yayi, ya dafe Kansa yana tunani sai kuma yayi karamin murmushi ya tashi ya shiga toilet, washe gari da tunaninta ya tashi ya dauko wayarsa dan sake kiran layin magajiya ko zai dace ta shiga, a fili ya ce "dole na nemo yarinyar nan, saita karbi hukunci mai kyau tunda ta soma sakani wanka cikin dare" ya kuwa yi Sa'a yana kira ta shiga sai dai ba a daga ba sai da ya sake kira, bayan magajiya ta d'aga tayi shuru, shine ya fara magana "ranki ya Dade ina cigiyar wannan yarinyar ta karshe da kika kawo min nasa aka dawo da ita" ya fada cike da gadara.
Saida taja dogon tsaki sannan tace "ni wallahi har hanjinka ina gani, tunda ka samu yarinyar mutane ka kwasheta daga ita har uwarta ban sake ganin su ba kaima ka dauki wayata ka gagara dauka, kabarni na Shiga hannun mutanen dana sa suka yima aiki dan na faranta maka saboda ba a biya su ba, ka dawo min da mutanena ka kuma biya kudin aikin da aka yi maka" ta fada tana huci kamar wata zakanya.
Murmushi yayi yace " wayanda suka miki aiki dai, ni basu min aiki ba, kuma koda sunyi ni yanzu kudina ba kudin haram bane balle na aikita haram da su ba, kisan yadda zakiyi da mutanen ki, ni yanzu Allah ya shiryeni na gano gaskiya kema ina miki wannan fatan, ki bude baki kice bakisan inda suke ba kin tsaya kina Jan magana" daga fadin haka ya yanke wayar ya kuma yi blocking dinta, sai kuma ya shiga tunani, ko dai yaje unguwar yayi bincike akansu, wata Kila guduwa sukayi saboda yadda aka tsoratar dasu, lallai Allah shine Allah, ji yadda mutanen suka zauna kusa da masu aikata wannan masha'a amma basu afka ciki ba Allah ya kare su to.
Safiyyah na zaune a kofar dakinsu tana gyaran farce indo ta kalleta tace "ni duk kaina ya daure, za'a barki kuwa kije da abin siyarwa a makaranta?" Safiyya tace " ai dama waccen makarantar ce Anty nan kam sai dai a boye, dan idan aka ganka da sana'a ma kwacewa ake" indo tayi dariya tace "to nikam na gaji da wannan zaman inaga zan ringa fita da wata sana'ar amma dai sai nayi shawara tukunna" dariya Safiyyah tayi kawai indo ta harareta ta shige daki.
Tun ranar da indo ta gargadeta bata sake Barin gurinsu ba sai yau da haka kawai taji bazata iya hakuri ba sai taje ta sake ganin bawan Allahn nan mai kuka, saida ta kalli yadda indo ta kwanta tana sharar bacci ta lallaba ta fita daga dakin, kamar barauniya ta isa wurin window din, tana lekawa suka hada ido ta falfala da gudu saida ta shiga dakinsu sannan ta tsaya tana sauke numfashi.
Koda ya leko baiga kowa ba, "amma lokacin da muka hada ido kamar wannan yarinyar" sai kuma ya mari Kansa yace "meyake damuna data fara yimin gizo?" Tsaki yayi ya dauki wayarsa dake kan gado yana cewa aransa "Allah yasa karna haukace akan yarinyar nan".
*Safiyyah galadanchi ke muku fatan alkhairi*
![](https://img.wattpad.com/cover/210952048-288-k453654.jpg)
YOU ARE READING
RUBUTACCIYAR K'ADDARA
FanfictionLABARIN UWA DA Y'AR TA WANDA YAKE CIKE DA TAUSAYI DA AL'AJABI, KUYI KUTSE A CIKI DOMIN GANIN ABINDA YAKE FARUWA.