BABI NA TALATIN DA BIYU

795 52 5
                                    

*RUBUTACCIYAR KADDARA*

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
( *home of expert and perfect writers)*💡

*SOPHIE GALADANCHI* ✍🏼

32

Momy data gama kallonsu ta window din dakin da take tayi murmushi tana jinjina karfin hali irin Na Deen, a fili tace "Aisha batasan yaran zamani sunfita iya duniyanci ba" ta sauke labule ta kwanta tana tunanin komawa Kaduna a goben.

Kafeshi tayi da ido tana kallonshi tace "Yaya Ashe tare mukazo lahira? Allah sarki nazata ni kadai naji abinda naje Ashe kaima kaji irin wannan azabar" aransa yace sambatu take, ruwan roba dake gefen gado ya dauko ya Shafa mata a fuska ta sauke ajiyar zuciya, ahankali ya dauketa suka shiga toilet.

Bayan sun gama shiri ya kalleta yadda ta kame zaune ta Cika tana batsewa yace "karfe uku fa yanzu lokacin salla bai yiba akwai saura ki kwanta kinji habibaty" saida masa wani irin kallo sannan tace "Allah ya tsareni in sake kwanciya nan dakin ka kash..." Kukan daya zo mata ya hanata karasa zancen, yana zaune yana aikin kallonta har tagaji tayi shuru sannan ya matsa kusa da ita, wata magana ya fada mata a kunnenta (nidai banji meyace ba) a hankali yakwantar da ita gefe ya kashe musu wuta.

Basu farka ba sai da haske ya fito shine ya soma farkawa motsinsa ya tada ita, ta tashi zaune tana zare ido tace "anty zatayi fushi idan tasan nazo nan ya zamuyi" toilet ya shiga batareda ya amsa mata ba sai da yayo alwala ya fito ya kalleta yadda take faman share hawaye yace "kiyi hakuri kibar kukan nan, ke matata ce Anty batada iko dake yanzu kuma kisani kofar gidan nan ban yadda kije ba" bata tanka masa ba ta tashi tsaye da niyyar zuwa alwala sai taji Ashe bazata iya ba komawa tayi ta zauna tana yamutsa fuska, Deen kuwa tada salla yayi har ya kammala tana zaune inda ya barta, kusa da ita yazo ya zauna yana Shafa fuskarta yace "Nagodewa Allah daya bani ke a matsayin mata, nayi alkawarin rike ki da amana zan nuna miki kalar soyayyar danake miki da zuciya daya, kiyimin alkawarin duk ajizancin dazanyi miki zakiyi hakuri ki jure batareda wani yaji ba, nasan ke karamar yarinya ce amma idan kinso zaki iya daukar nauyina da bukatuna Dan Allah ko sau daya Safiyyah kada ki gaji dani" wani irin tausayinsa taji batasan me zatace ba amma taji dadin irin yadda yake sonta gefen kafadarshi ta Dora kanta tana cewa "kasan yadda zakayi dani inaso nayi salla amma Na kasa dagawa daga nan" mikewa yayi tareda ita yace "dole ne kiji haka kiyi hakuri duk laifina ne, bari Na duba store ko akwai babbar robar da zaki iya zama aciki tunda Abba ya hanamu zama wancen gidan" gyada masa kai kawai tayi ya sake zaunar da ita, babu dadewa ya dawo sai da ya hada ruwan sannan ya dauketa, tanayin salla ta sake kwantawa saboda baccin da takeji.

Kallo daya zakayiwa fuskar Anty kasan kadan take jira, Momy ta kalleta tace "shiyasa jiya nayita baki hakuri, bakisan halin da yaran nan suke ciki ba, duk da nasan akwai matsala gefen Deen banyi tunanin zai kyale ba, ita dakanta ta bishi, Dan Allah tunda yaran nan suna son junansu ki kyale su kiji da jikin ki, kalli yadda duk kika firgice, magajiya ma dakike wannan fushin akanta tun jiya suke police station yau babansu yake fadamin sun tabbatar da karya suke shiri suka kulla Dan haka ya dauki mataki bawai Dan be yadda da abinda yake cikin ki bane, wata hikima ta manya yayi amfani da ita, gashi cikin ruwan sanyi sun fallasa kansu" dukda bata saki fuskarta ba amma taji sanyi sosai aranta, tasan matsalolinta sun ragu sosai.

Momy ta kwala kiran hafsatu, ta fito tana kallon yayarta dake zaune kan kujera duk tayi wani fayau da ita tace "ki kawo mata tuwon da su larai suka dumama, sannan dankalin nan asakashi a kula da ruwan shayi a flaks akaiwa su Safiyyah can bangarenta" amsawa tayi da to tayi yadda Momy tace.

Momy bata bar gidan ba sai da ta tabbatar komai ya zama normal sannan ta hada kayanta tashiga part din Safiyyah domin yi musu sallama, tamusu nasiha sosai da zata tafi Safiyyah tamike zata raka ta tayi saurin cewa "kiyi zamanki Allah ya kawo sauki" tun fitowar Safiya ta kalli yanayin tafiyarta shiyasa ta hanata tashi yanzun.

Bayan fitar Momy babu dadewa Halima tayi Kiran Safiyyah awaya saboda taga miss call dinta, tana dagawa halima tace "amarya yakika kwana" Safiyyah ta yamutsa fuska tace "babu dadi" dariya Halima tayi tace "karki cemin Kinyi missing yayana" "dama hakan ne zefi sauki, jiya ta window yayanki ya sato ni shine Na kira ki in fada miki ai a part dinmu Na kwana su Anty basu sani ba" dariya sosai Halima tayi tace "wallahi Yaya anyi dan duniya, to ya kikaji lamarin Dan nasan babu dagin kafa" tsaki kadan tayi tace "har yanzu bana iya tafiya yadda ya kamata, kuma wallahi ko da azahar din nan sai da Na zauna a ruwan zafi" halima tayi doguwar hamma tana cewa "shine dai mafita kici gaba dayi, bari inyi wanka insha Allahu da dare zamu shigo nida muhammad" daga haka sukayi sallama.

"Wallahi abubakar aure rahama ne bakaji yadda naji ba jiyan nan naga babu uban da nake tsoron yazo yaga abinda nayi, kuma yarinyar tayi ni yanzu ma rakani zakayi a duba mata mota sabuwa dal" Deen ya fada yana shafar gemu, abubakar ya kwashe da dariya yace "abinda nake fada maka kenan alaji kaki yadda yanzu gashi nan dai ka gano da kanka" dariya sukayi tare suka tafa.

Sai da aka kwana biyu ana kai musu abinci sannan Safiyyah ta soma shiga kitchen, hankalinsu a kwance sai wani gefe da Safiyyah take shan tumurmusa amma bata taba nuna damuwa ba, ta yadda kuma yazauna wuri daya daga wurin aiki sai gida baya zuwa ko ina yana manne da ita yana hutawa.

Sati biyu bayan biki yace tazo su gaisheda anty, tace "wallahi inajin kunyar Anty Yaya" yaita lallashinta yana cewa "ai anty tayi kamar ma ba abinda ya faru Kuma kinga bai kyautu ba ace muna gida daya sati biyu baki je kin gaishesu ba".

bayan sun shiga part din ta tsaya daga gefe har anty ta fito, ta kallesu tayi murmushi kawai, gaisawa sukayi Deen ya mike yana cewa "ki zauna nan zanje Na dawo ko" ta gyada kai tana kallon anty da gefen ido, ya fita anty tabi bayanshi da kallo tana mamakin wannan kamilin shine ya iya wannan abin ta kalli Safiyyah tayi magana da yarensu tace "meye kike wani yin kasa dakai mai miji?" Kasa ta sakeyi da kanta tace "anty yajiki Yaya Deeni yace bakida lafiya" anty ta kalleta yadda tayi fresh ta kawar da kanta tace "lafiya lau, mijin naki ya fada miki yayarki tana asibiti ko?" Safiyyah ta fito da ido waje tana cewa "wallahi bai fada min ba, ita ma mun kwana biyu bamuyi magana ba" anty ta mike tsaye tana sake boye cikinta a hijab tace "idan Abbanku yazo sai mutafi tare.

Sai da ta Sanar da Deen sannan suka tafi, koda suka je ta saukama ta samu baby boy tana ta bacci abinta, kallo daya Deen yayiwa babyn yaji kamar shi aka haifawa babyn ya kalli Safiyyah yana kanne mata ido daya.

RUBUTACCIYAR K'ADDARAWhere stories live. Discover now