BABI NA TALATIN DA DAYA

765 46 2
                                        


*RUBUTACCIYAR KADDARA*

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
( *home of expert and perfect writers)*💡

*SOPHIE GALADANCHI* ✍🏼

31

Duk yadda yaso su hada ido kin yadda tayi har aka gama daukar hoton suka fita shida abokanansa, anan harabar gidan suka ci abinci sannan suka fita zuwa gidansa inda yake shirin angwancewa.

Halima ta zauna kusa da ita tana cewa "ki tashi kiyi wanka dan Allah kinga har ana batun sallar ishai, miko min waccen ledar kafin ki shiga wankan" batayi magana ba ta miko mata ledar tana mikewa da nufin shiga toilet, Halima ta katseta tana cewa "karbi wannan kisha kinji kanwata" sai taji kunyar kin karba tunda aka fara bikin nan Halima ke lallashinta akan abubuwa, karba tayi sai da ta dan lasa sannan ta shanye ta mika mata robar tana cewa "naga burinki dai kisa yayanki ya balla ni" dariya Halima tayi tana cewa "bakomai zai kuma hadaki ne ya gyara barnarshi ni tunda kin yadda da auren hankalina akwance yake" batayi magana ba ta shige bayin ta watsa ruwa, koda ta fito komai Halima ta hada mata ta kalleta yadda take aikin sauke numfashi tace "Yaya dan Allah karki sake yin komai bakya ganin yadda kike ne" kafin ta bata amsa ta jiyo hayaniya daga Palo sai ta mike ta fita, Safiyyah kam bata damu ba ta soma shirinta, ta kammala komai tana fesa turare Halima ta shigo tana share hawaye fuskarta. Tsaye Safiyyah tayi tana kallonta.

"Anty ce take cewa bata yadda da auren nan ba tunda Abba bai yadda da ita ba har yana tantama akanta ya jira sai sanda yagama binciken sa bazata aurawa yar ta fasiki ba" gaban Safiyyah yai wata irin faduwa sai kawai ta nemi wuri ta zauna. Tana cewa "ina anty take"?
"Tana ta amai Abba yayi fushi ya fita, Momy ce a wurinta tana bata hakuri, amma Momy tace abar zancen tarewarki har hankali ya kwanta nidai bance komai ba saboda banida abin cewa, wallahi matsalolin gidan nan sun fara isata, bari kiga ma na kira Muhammad yazo ya daukeni kar hawan jini ya kamani" shuru Safiyyah tayi basu kara yiwa juna magana ba har Muhammad din ya iso, saida sukayi sallama sannan Halima ta fita, bata nemi kowa daga cikin su ba tayi tafiyarta.

Tashi tayi tacire kayan jikinta tasaka na bacci ta kwanta bayan ta rufe dakinta tana sauraren yadda cikin ta ke kukan yunwa.
"Bata son taji komai, tun daga ranar dataji asalin zuwanta duniya ta daina takama da wannan rayuwar duk abinda sukaga dama suyi da ita" da irin wannan tunanin bacci ya dauketa.

"Shashashan banza da wofi, ka zubar min da mutunci wallahi, menene bakada shi, kayi amfani da dukiyar da Allah ya baka kana sabawa Allah, duk abinda ka Tara kamata yayi ace zuwa yanzu kanada iyali amma ka tsaya lalacewa da yayan mutane a waje, tun kafin Aisha tace bazata yadda da tarewar Safiyyah ba na yanke shawarar zaka zauna anan gidan to kuma yanzu tace bazata yadda ba nasan rigima ce ta dan lokaci inzaka gyara ka gyara wallahi ni na gaji da tashin hankali" gumi ta kowane gefe ya gama tsatstsafo masa wannan rana daya shiryawa duk abinda zai bashi lafiya babu Wanda bai ci ba amma da anty ta gama dashi, har Abba yagama surutunsa a tsaye kawai yake, jin baice komai ba Abba ya tafiyarsa.

Waya ya lalubo ya kira abubakar yana fada masa abinda ya faru " kai yanzu ya kake ganin zamuyi" Deen yace "kai wallahi sena dauko matata, sai da safe zamuyi magana" ya kashe wayar ya shiga part dinda Abba yace zasu zauna duka yaga keys din ajikin kofa an share shi sai kamshi yake.

Kulle gidan yayi ya fita babu dadewa ya yadawo, ya silla wanka yasaka kayan bacci ya fita, bayan gidan ya tafi yana kallon window din dakin Safiyyah a hankali ya Ciro na gefe mai net din ya ajiyeshi gefe, saida yagama kare mata kallo tana ta sharar bacci, akwatunanta ya kalla ya budesu a hankali yaciro kaya masu amfani sannan ya fito ta window din ya kai kayan part dinsu sannan ya dawo, kujera ya taka yasake haurawa, huci ya fitar yana tunanin babu yadda zaiyi ya fita da ita ba tareda ta farka ba, kuma koda ya baro part dinsu shadaya da mintuna basufi ashirinba, kwantawa yayi kusa da ita yana Shafa fuskarta ta bude idonta a hankali tasake rufewa, cigaba yayi da Shafa fuskarta harta bude idonta ta kalleshi dakyau, tsoro taji ta matsa baya tana kallon dakin, dukda babu haske sosai ta tabbatar dakinta ne wannan tace "Yaya Deeni mekakeyi anan"? Murmushi yayi yana cewa "zuwa nayi kibini mutafi bangarenmu" ta sake matsawa baya tana fito da ido waje tace "Yaya dan Allah kabari mana har dasafe ko bakaji rigimar da Anty tayi dazu bane" duk a hankali suke maganar ya marairaice fuska yana cewa "wallahi tallahi bance miki zan iya hakuri ba kizo mu tafi na bude window" acikin duhu ta harareshi tana cewa "babu inda zan bika" ya rike hannunta yana cewa "taimakona zakiyi kinsan fa nayi hakuri safiyyah, wallahi bazan iya ba yanzu na kwallafa rai" kwace hannun ta tayi tana cewa "bari na fadawa anty abinda kazo kakeyi" zata mike yayi saurin riketa yana cewa "to wallahi in baki bini ba zanyi abinda zanyi anan dakin, haba Safiyyah baki ko tausayina, sai kace bakisan ko wanene ni ba, ki dubi girman Allah ki taimakeni kizo mu tafi i promise to be gentle wallahi, anty bazata yadda kibini ba yanzu intaji, wurinki kawai nake samun sassauci a gidan nan kowa haushina yake ji" jikinta yayi sanyi taji tausayinsa tace "to yanzu ta window kake nufin zamu bi"? Yayi saurin gyada mata kai yana cewa " eh ni zan saukeki bazan bari kiji ciwo ba ta janyo hijabinta ta dauki wayarta tace "muje ingani" bai jirata ba ya dauketa a hankali ya saukar da ita kan kujerar ta matsa shima ya fito ya dauki net din ya mayar sannan suka tafi a hankali seya leka yaga ba kowa sannan ya dawo yaja hannun ta har suka Isa part din suka shiga ta tsaya tana cewa "ban dauko kayana ba, kuma da asuba zan koma can ko"? Ya kalli idon wautarta yace "eh ni zan maidake ma, kayan kuma na dauko tun kafin na tada ke" ta sauke ajiyar zuciya sannan suka karasa ciki.

Da hira yayita ribatar ta ta saki jiki har sukayi sallah suka ci nama dama tana jin yunwa taci sosai sannan suka sa sauran a fridge.

Sai da akazo kwanciya ido ya raina fata, gabanta ya soma faduwa, amma ta riga ta kawo kanta batada mafita.

RUBUTACCIYAR K'ADDARAStories to obsess over. Discover now