*RUBUTACCIYAR KADDARA*
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
( *home of expert and perfect writers)*💡
*SOPHIE GALADANCHI* ✍🏼
(20)
Maimakon tsugunawar da yayi sai yasamu Kansa da zaunawa kasan batareda ya damu da fararen kayan dake jikinsa ba, yana jin kunya, yana jin nauyin yadda zai daga ido ya kalli yarsa, babu yadda zaiyi tariga taji, fyade yayiwa uwarta aka samu cikinta, tabo yayiwa uwarta Wanda bazai goguba duk yadda yayi kuwa, shi namiji ne bazai yadda ya nuna cewar ya karaya ba, sai ya kalleta yace "kiyi hakuri, Abbanki yayi Safiyyah, kiyi hakuri karki rikeni da wannan laifin Dan girman Allah, nayi alkawari dake da mahaifiyarki bazaku sake shiga muguwar rayuwa ba indai ina raye" ita kanta ta kasa kallonshi wani iri take ji kamar bataga laifin shi ba amma kuma bata isa ta yanke wannan hukuncin ba.
Sai kawai ta gyada masa kai, yace "Nagode sosai Allah yayi miki albarka ya baki miji Na gari" ya fada yana kallonta sai yaga tayi murmushi yaji dadin hakan, sai ya sake cewa "kiyi wanka ki sauya kayan nan tun jiya suke a jikin ki, Na kawo miki kaya amma duka English wears ne atamfa Tela yace gobe nazo Na karba, sai dai ban saniba ko antynki zata iya saka irin wannan" ya fada yana janyo leda gabansa, doguwar riga ce ja tasha ado da stones sai kyalli take, karbar rigar Safiyyah tayi tana kallon indo, indo murmushi kawai tayi mata. Safiyyah tace "zata saka ai tana son doguwar Riga" ya daga mata kai se yace "kije dakin innah zanyi magana da Antynki" batareda tayi magana ba ta fita da ledar kayan a hannunta.
Deen yayi tsaki yafi a kirga. Ta ina ma zai fara Neman su Safiyyah, yasan bashida wani dalili Na Neman magajiya Dan yasan bazasu kara da kyau ba. Abubakar ya kalle shi yana cewa "kaifa mugun maye ne, yarinyar nan inaga idan ka aureta daina fitowa zakayi waje, bakada aiki sai mafarkinta kullum akan Abu daya to idan ka aure ta ai inaga awa ashirin da hudu duk akanta zasu kare" tsaki Deen ya sake yi yana cewa "kai banza ne wallahi, ana zancen yarinya ta bata bansan inda take ba kana zancen aure, Ka kawo shawarar kwarai kaji".
Abubakar yace " kawai kaje unguwarsu ka bincika ko sun San sunan garin nasu abun zai zo mana da sauki" shuru yayi yana kada kafa Dan gaba daya kansa ya kunce.
"Aisha wannan zancen da Abdullahi yazo dashi rufin asiri ne a garemu baki daya, ki duba ki gani wasu idan irin haka ta faru dasu mazajen basa son auren su, wasu kuma auren baya dadi ko anyi, meyasa zaki butulcewa Allah da irin rahamar da yayi miki" indo tana kuka tace "haba inna, Baku fa sanshi ba ya dawo ya Baku hakuri kun hakura nima na hakura, shikam ya tafi mana" inna ta sake yin kasa da murya tace "to Aisha kinji fa abinda yace, idan ba zaki aureshi ba ki bashi Safiyyah nasan kuma ba zaki iya ba, kinga tun yana lallashinmu idan an tunzura shi yana da karfi da dukiyar da zai karbi yarinya kota halin yaya, bayan haka kuma Baffanku yasan shi tun ba a ganoki ba ya danyi bincike akansa bai kuma ji wani mummunar tarihi nasa ba kiyi tunani dai zuwa gobe" indo ta goge hawayen idonta tana cewa "ba wani tunani inna inajin tsoron mutane yanzu ba abin yadda bane kai tsaye" haushinta ya kama inna tace "to sai ki zauna a gidan kina goga kafada dani, ki kuma yi kokari ki maimaita abinda kikayi tun farko ki gani idan zakici riba a karo na biyu" shuru tayi tana kallon inna ta kasa koda yin motsi ne bataso tana tuno rayuwar baya.
Bayan sati biyu ta warke sumul kamar batayi jinya ba, Abdullahi kuwa baya gajiya duk bayan kwana biyu yana hanya ko kuma yayo aike baida matsalar komai haka yake ji, yauma tana zaune a tsakar gida akayo sallama da ita a waje. Sai da ta saka hijabi sannan ta fito yana zaune a soron gidan kan tabarma, zama tayi suka gaisa fuskarta a sake kuma yaji dadin hakan, sai yake cewa "Dan Allah akan maganar Safiyyah ne, inaso ki bani ita naje na sakata makaranta kafin muga me lokaci yayi amma idan bakyaso wallahi ta zaunu senajira har ranar da nima kika amince dani Dan naga har yanzu baki kai ga matsaya ba" Dan gyara zamanta tayi sannan tace "duk abinda Baffa yace, kaima kanada iko akanta nasan bazaka cutar da ita ba sai dai ko zata bika kada ka manta amana ce Safiyyah a wurinmu" yaji dadin zancenta sai ya shiga yi mata godiya Dan yayi magana da Baffa yace ya nemi jin tabakinta.
Safiyyah kam kin yadda tayi ta bishi tace sai dai idan ummanta zata zo su tafi tare, dakyar inna tasa baki akan ita indonma zatazo su zauna tare wata rana sannan ta hakura tace ta yadda.
Maganar daya ce duk inda Deen yaje tambaya a unguwar sai ace ai ba asan sunan garin su ba, dansu sun zata ma yan uwan magajiya mai rasuwa ne, da ciwon kai ya dawo tun daga lokacin yake jin kansa sama-sama, wasa-wasa sai gashi ya kwanta zazzabi, sai da ya kwana biyu bai je aiki ba, koda yakoma aikinma baya sakewa jikinsa kullum a mace yake, haka kuma dare kawai yake jira sedai in be kwanta bacci ba sai yayi mafarkinta, sabon mafarkin dayake yi ma yanzu kullum sai yaganta taci kwalliya kamar amarya, tsoro ya kama shi indai ba aure tayi ba ta barshi.
Dogon tsaki hajiyar taja tana cewa "ko kunya bakaji ka dauko shegiyar yarinya ka kawo kana wani hura hanci kai ga mai y'a, to wallahi Dan kaji baka isa ba, sai ka zaba ko ni ko ita, nagaji da wulakancin da kake min acikin gidan nan, bayan waccen sauran rami ka ajiyemin yanzu kuma ka kawo min yar gaba da fatiha, ai wallahi bazan yadda ba" tunda take magana baiko dago ya kalleta ba, saima aikin gabansa daya ci gaba da yi ta sake daga murya tana cewa "dakai nake magana ka zaba ko ni ko ita" sai a lokacin yace "na zaba ko ke ko uwarta dai ko? Idan zaki iya ki zauna idan ba zaki iya ba kitafi tunda ke bakida lissafi" shuru tayi gabata na faduwa da jin kalamansa, shikam shareta yayi Dan bayason tashin hankali.
Halima dake kwashe kayanta gefe daya daga cikin wardrobe din tana dariya tace "haba koba komai yanzu na samu kawa, Abba yasan inada kanwa amma bai taba fada mana ba, ai wallahi bari yaya yazo sena fadamai, ya fadawa Abba bai kyauta mana ba, kanwa ta jini kinsan jiya su zulaiha cewa sukayi wai yatsun kafarmu iri daya, shine nikuma nace jini ai ba wasa bane, hmm nasan ma idan yaya yazo ya ganki dolema ze kaimu shopping sannan zamuje har har garinmu ki gano kakar mu tana nan zaki ganta ta tsufa taki mutuwa" sai a lokacin Safiyyah tayi dariya Dan bata sake da Halima har zuwa lokacin tace "wannan yaya yana shan kira zanso ganinshi kuwa" Halima tace "aiko zaki ganshi, Dan nasan shine zai bada aurenki kamar yadda yayi min, dakyar ya yadda da Muhammad dina, bari nayi Sauri na gama gyara miki wurin nan dukda nasan bazai dauki kayanki ba amma karki damu dakin nan bar miki shi ma zanyi duka, Dan Muhammad dina yace shi daga anyi babbar salla yakeso ayi aurenmu" Safiyyah ta zare ido tace "yaya Halima bakya jin kunya? Idan Antyna taji ina zancen aure ai se ta yimin Dan banzan duka" Halima ta kalleta da mamaki sai kuma tace "kinsan Fulani da kunya, shi take so kiyi" murmushi kawai Safiyyah tayi tana kallon yadda ake shirya kaya wai duk nata ne, Allah sarki ta tuno da antyn ta yadda take jera musu kayansu acikin jakar kayansu.
Wata irin kewar Safiyyah ta addabi indo ta kasa yin bacci ma yau, ko wane hali diyarta ta take ciki Allah masani.
Makaranta kuwa ta masu hali dai-dai gwargwado aka saka Safiyyah, kullum idan zataje idonta yana kan hanyar gidan oga Deen, da kamar yadda takeyi da ne, da wata rana sai tasan yadda tayi taje gidan amma yanzu an hadata da mai kaita ya daukota amma ko yayane watarana dole sai taje gidan nan.
YOU ARE READING
RUBUTACCIYAR K'ADDARA
FanfictionLABARIN UWA DA Y'AR TA WANDA YAKE CIKE DA TAUSAYI DA AL'AJABI, KUYI KUTSE A CIKI DOMIN GANIN ABINDA YAKE FARUWA.
