SHAFI NA GOMA SHA HUDU

729 55 6
                                    

*RUBUTACCIYAR KADDARA*

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
( *home of expert and perfect writers)*💡

*SOPHIE GALADANCHI* ✍🏼

(14)

A tsorace take tafiya jin alamar mota a bayanta, Deen kuwa basarwa yayi kamar bai ganta ba yana danna waya yana driving har yazo ya wuce ta, tsayawa tayi ta sauke ajiyar zuciya sannan taci gaba da tafiya, tana mamakin abinda ya hanashi yi mata magana duk da ya ganta kuma ta tabbatar da ya gane ta.

Sai da yayi nisa sannan ya tsaya yana murmushi a fili ya furta "wallahi itace, kai amma Allah ya sakawa abubakar" cike da nishadi ya shiga inda yake aiki, tun daga gate ya soma sadaka, fara'ar fuskarsa kawai zata nuna yana cikin tsananin farin ciki, securities din wurin da cleaners sun yi murnar zuwan wannan rana, dama ya kwana biyu bai saka hannu a aljihu ba.

Abubakar ya sameshi a office dinsa yana cewa "Ranka ya Dade yau naji kamfanin nan ya hargitse da zancen ka sai addua ake maka" murmurshi Deen yayi sannan yace "kaima kanada taka kyautar saboda yau idona tar acikin idon masoyiyata" ya fada yana dafe gefen zuciyarsa, abubakar ya bashi hannu suka tafa yace "hankalin mu ya kwanta kenan yanzu? Sai magana ta furta mata Kalmar so" shuru Deen yayi sannan yace "ina wani tunanin ne, idan Naje mata da wannan maganar zata tsorata yanzu saboda kasan abin da ya faru tun farko" kallon sa abubakar yayi yana gyada sannan yace "kayi magana gaskiya, Allah ya taimaka" murmushi Deen yayi ya amsa da ameen.


Magajiya na zaune a dakinta tana kwalliya, gefenta Kofi ne babba cike da tsimi, murmushi kawai take zata hadu da Alhajinta dan yau ya dawo daga tafiyar da yayi, ya kama musu daki a babban hotel dan haka yau akwai more rayuwa, ta gama yan zizare-zizaren ta ta dauki kofin ta shanye abinda ke cike ta gincira tana tunanin yadda zasu murje juna yau idan sun hadu, agogo ta duba taga biyu da rabi yace karfe uku zai aiko a dauketa, sai ganin mutum tayi akanta yana murmushi, zaro ido tayi muryarta na rawa tace "Oga mai kuma ya kawo ka yanzu babu labari?" Dariya yayi sannan yace "ladan aikina nazo deba" daga haka bai jira tayi wata magana ba ya afka mata, duk sai da ya kwashe zumar da aka tanadarwa Alhaji, yabar magajiya kwance tana jinyar jiki, gaba daya ta gama tsorata da lamarin nan, koda ta duba wayarta miss call na Alhaji da wanda ya turo sunkai goma, wata irin gajiya takeji amma dole zata kaiwa Alhaji wannan ziyarar.

Gaba daya gari ya gama dauka indon Gid'ad'o ta dawo bayan shekaru goma sha biyar.
Hajjo na zaune a dakin ta mijinta ya shigo Baffa salihu, sai da ta tabe baki tace "kaji mutanen can wai murna suke yarsu ta dawo bayan ta gama lalacewa a gidan karuwai" Baffa salihu ma tabe bakin yayi cike da hassada yace " su suka jiyo" daga haka ta kawo masa fura ya shiga sha yana tunani.
Hira suka dasa irin ta y'a da uwa anan indo take fadawa Inna gobe zata wuce, inna tace "duka yaushe kika zo ma da zakice ki tafi?" Indo tayi murmushi da irin kunyar su tace "Inna kinsan na baro Safiyyah sannan kum..." Inna ta katseta da cewa "ita Safiyyah din ba hannun mutane kika barota ba? Ko jaririyace ita zaki je ki bata Nono?" Shuru indo tayi tana wasa da yatsun hannunta sannan tace "inna yanzu ba daya da baya ba, wayanda na baro ta wurinsu basuda karfi sannan kuma tunda Muke bamu taba daukar lokaci bama tare ba dole zata ji daban" Inna tayi murmushi tace "hakane amma idan kinga kin bar garin nan to kin gama zaga dangi nan da sati biyu tukunna" gabanta ya ringa faduwa tana tunanin halin da yarta take ciki yanzu gashi bazata iya yiwa Inna musu ba sai ta kama bakinta ta tsuke.

Karfe uku Deen yadawo gida, malam buba yanata mamakin dawowarsa da wuri yau, wanka ya shiga yayi ya shirya cikin kaya marasa nauyi yafito harabar gidan ya zauna kan kujera yana danna waya, malam buba yace " hmmm wata sabuwa inji yan caca", deen kuwa ya kasa ya tsare yau gefen BQ yake kallo saidai dayake can baya ne baya hango komai, yana zaune yaji ana buga gate amma bai damu daya kalli gefen ba.

Safiyyah data shigo bayan malam buba ya bude mata kofa gabanta ya fadi, yau da tunanin Deen ta wuni a makaranta gashi ta dawo kuma ta sameshi zaune a harabar gidan abinda bai taba yi ba, kawar da kanta gefe tayi taci gaba da tafiya, duk da tana dan nesa dashi hakan bai hanashi kare mata kallo ba, yana lumshe ido kamar mai jin bacci, shi kadai yasan abinda yakeji game da yarinyar nan.

Bayan sallar magrib Deen ya shirya domin zuwa gida, bayan yaje sun gaisa da Abba ya nufi dakin Halima ya sameta a kwance kamar mai bacci ta shiga da sallama, tashi zaune tayi suka gaisa yace " ya labarin Muhammad?" Ya tambayeta yana dariya itama dariyar tayi sannan tace "yana nan yaya yanzu daka shigo dashi ma nake waya ganin ka yasa na katse, yace zai zo office ya sameka ina ganin yayi yadda kace ne" fuskarsa dauke da murmushi yace "to ina jiransa, bakya bukatar komai? Naga kin fara yin kiba kin daina wasa da abinci kenan?" Fuskarta ta rufe da tafin hannunta tace "bana bukatar komai yaya jiya da Muhammad ya dawo dani daga makaranta ya kaini shopping" zaro ido yayi yana cewa "kudinsa kika soma ci? To ki rubuta ki ajiye kar balli ya tashi nidai ina gefe, sannan kuma ina motarki?" Dariya tayi tace " ai Muhammad ba haka yake ba, kuma motar ce muntari ya wanketa bata bushe ba shine taketa wari sai na barta a bude" ya jinjina kai sannan yace "to shikenan bari in wuce idan da wani Abu ki kirani awaya" amsawa tayi da to tanajin dadin yadda yake kulawa da ita.

Ranar da indo ta Cika kwana biyar da tafiya a ranar Safiyyah zumudin dawowar Anty yacika zuciyarta, ta shiga dakinsu ta gyara ta goge ta zauna zaman jiran Antynta amma shuru har akayi sallar magriba, tana zaune taga dare sai yi yake amma babu alamar zata dawo, sai a lokacin take tunanin dama sunada waya da yanzu takira Anty taji ko lafiya, haka ta kwana cike da zullumi, washe gari ma tasa ranta da dawowar indo, a makaranta ma bata tsaya lesson ba ta dawo amma sai ta Tarar yadda ta bar dakin haka ta dawo ta sameshi, zama tayi ta ringa kuka ko abinci taki ci.
Kwana biyu tayi tana zuba ido daganan tacire rai, tashi tayi ta zaga baya inda Anty take hanata zuwa tayi zaman kuka tana cewa "dama wannan Anty take yiwa gudu tasan idan taje bazasu barta ta dawo ba, idan Anty bata dawo ba Na tabbatar mutuwa zanyi" ta kara sautin kukanta, Deen yana zaune a dakin yajiyo alamar kukan mace yataso ya tsaya kusa da window din yana hanngota, a hankali ya bude glass din window yana kallonta, atake kansa ya shiga Sara masa yana jiyo kukan nata har cikin kwakwalwarsa.

*Safiyyah Galadanchi ke muku fatan alkhairi*






RUBUTACCIYAR K'ADDARAWhere stories live. Discover now