page 12

779 58 16
                                        

*RUBUTACCIYAR KADDARA*

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
( *home of expert and perfect writers)*💡

*SOPHIE GALADANCHI* ✍🏼

(12)

"Wannan wace irin muguwar dabi'a ce Safiyyah?" Indo ta fada dan ta tsorata jin yadda Safiyyah ta shigo dakin da gudu.
"Anty kadangare n..." Tsakin da indo tayi ya katseta tayi shuru tana sauke ajiyar zuciya, bata zauna a dakin ba ta fito korido dinsu ta zauna tana tunanin abinda ya faru mintuna kadan da suka wuce, dariya tayi a fili ta dafa gefen zuciyarta tace " wallahi naji tsoro, idon mutumin nan kamar mujiya" ta sake kwashewa da dariya tana fadin "Ashe haka bakinsa yake kamar na mace, ko dai yana Shafa Jan baki ne?" Kiran sallar da akayi yasa ta tashi domin yin sallar.


"Yaya yace in bashi numbern ka kuyi magana, dan Allah yaya ka saurareshi" Halima ta fada cikin muryar kuka lokacin da take magana da Deen a waya, saida ta kai karshe sannan yace "sauwama ke kikeso ki wahalar da kanki akan wannan maganar, kinsan Muhammad dinnan ba shine farko a nemanki ba amma babu Wanda na yadda yazo kai tsaye wurin iyayenmu dan haka shima sai yayi yadda nace, idan yayi ya dawo to wallahi na bashi ke halak malak Halima" sai da taja majina sannan tace "to yaya zan kara fada mishi" daga haka sukayi sallama, amma ita sai ta dasa kuka,yayanta gani yake kamar hakan shine gata awurinta bayan bai san tana matukar cutuwa ba.

Deen kuwa zama yayi tunanin Safiyyah yau da asuba ma duk uban sanyin nan sai da ta saka shi yin wanka sannan yayi sallah, sai da yaja iska da bakin sa kafin yace " hmm wannan yarinyar ranar da duk ta shigo hannu zamu raba raini da ita" sai kuma ya zare ido yana kallon kansa ta madubi yace "ji yadda mutum yake magana shi Kadai saboda wannan yarinyar "hannu ya Dora a kai yace "ban San sunanta ba, dole zan mata suna Wanda ya dace da ita" tsaki yayi ya sake cewa "to ko dai haukacewa nayi akanta? Allah gani gareka, Allah kasan niyyata ka bayyanamin wannan yarinyar" ya amsa da ameen shi kadai sannan ya kwashi tarkacensa ya bar gidan.


Malam buba yana fitowa ya hango indo tana wanki yayi saurin zuwa wurin yana washe bakin nan as usual yana cewa " Maman safiyya wanki a cikin sanyin nan" bata kalle shi ba tace " babu komai zan iya ne" ganin yadda ta murtuke fuska yasa shi cewa " to nima bari na koma can gate Allah ya taimaka" sai da taga tafiyarsa sannan ta amsa tana sake tsuke fuska, shishshiginsa ya soma yawa, haka jiya yazo yana damunta akan zancen zuwa gida.

Safiyyah na gyaran farce ta kalli indo tace " Anty jiya naji kin cewa baban fadimatu zaki je gida wani satin" yadda tayi maganar ya nuna cewa taji dadin zuwa gidan da indo zatayi " Eh ran laraba zan tafi bana so na wuce kwana biyar, idan Na Dade sati daya" Safiyyah tayi murmushi tace " da ba saboda makaranta ba Anty dana biki" harararta indo tayi sannan tace " Gara da kikasan akwai makaranta, kuna kusa da yin Hutu yanzu dan nasan bazaku yi azumi a makaranta ba" safiyya ta karkata kai tace " sau sati daya mu fara jarabawa, azumi kuma saura kwana ashirin da bakwai" indo tace "to kinji dai, ki tsaya har bayan salla idan zan koma sai mu tafi tare" gyada kai kawai Safiyyah tayi.

Ranar alhamis karfe biyar da rabi Deen ya nufo gida saboda kansa dake masa tsananin ciwo, dole ya koma gida ya kwanta, yasan rashin samun ishashshen Hutu ne yasa masa ciwon kai.

Tana kwankwasa kofar gidan malam buba ya bude mata zata shiga taji horn din mota a bayanta, tana juyawa suka hada ido ta sauri ta shige gidan.

Deen ya saki baki yana kallon wurin har malam buba ya gama bude masa gate a fili ya furta "amma wallahi ina cutuwa, ji yadda yar mai gadi kemin kama da yarinyar nan" tsaki yayi sannan ya shiga gidan danshi harga Allah bai san akwai wata yarinya budurwa gidan bayan diyar malam buba ba, kuma idan za a kashe shi bazai ce ga fuskarta ba dan babu ruwanshi da ita har uwarta, parking yayi ya zauna amotar yana fadin "idan ma ta kama naje amin rukiyya ne zanje dan inaga yarinyar nan aljana ce, haka kawai bazan zauna ta zautar dani ba" daga haka ya fito ya shiga gida ko kayan Jikinsa bai cireba ya kwanta, a gida yai sallar magrib da ishai sannan ya kwanta.

Ranakun zuwan indo gida na matsowa yayinda Safiyyah ke shiga fargaba, dan yanzu bata samun sakin fuska daga wurin su huraira da fadimatu kamar da, yanzu ma idan ta zauna sai su sauya harshe suna magana da yarensu na buzaye, wata rana sai dai tayi murmushi tace aranta "Allah yasa dai muma muna da yaren" amma a fili bata nuna yana damunta, dan ita dinma ba surutu ne da ita ba, ko tarkacen kawaye bata da.

Yau laraba ta kama ranar da indo zata je gida, tunda asuba safiyya take zubar da hawaye, tanajin kamar ta hada kayanta tabi indo amma babu hali, saboda makaranta da kuma dalilinda indo kadai ta sanshi.

Sai da ta gama shirinta gaba daya na tafiya ta zaunar da safiyya kusa da ita ta kalleta cike da tausayi sannan cikin muryar lallashi tace "bakyaso na je na gano miki danginki? Idan fa na gano su safiyya mun daina rabe-rabe, abinda yasa bazan je dake ba wahala zakiyi Safiyyah, kinsan saboda me? Saboda nasan ko da zan je ansamu sauye-sauye da yawa a garin nima sai na sha wahala zan gane dan haka kiyi hakuri kwana hudu ma zanyi in dawo da yardar Allah, nasan kinajin magana dan haka ki kama kanki kamar yadda kikeyi koda yaushe" Safiyyah ta sauke ajiyar zuciya sannan ta amsa da to, indo ta mika mata jakar makarantar ta tace "ki tafi Allah ya bada sa'a" saida ta amsa sannan ta fita.

Indo kuwa gefen huraira taje ta sake yi musu sallama hadi da barin amanar safiyya a wurin su sannan ta bata key din dakinsu idan safiyya ta dawo sai dai kwana a dakin ne bata yadda safiyya tayi ba ita kadai, huraira ta Dan saki fuska tace "ba komai zamu kwana anan", Godiya Indo tayi sannan ta dauki jakar kayanta ta bar gidan.

Magajiya kuwa cikinta ba kadan ya duri ruwa ba, duk ta firgice ta shiga tunanin inda zata samu kudin sallamar mutanenta, daga nan ta yanke shawarar kiran alhazawan ta domin su moreta su kuma biyata shine kawai mafita, dama ta kwana biyu babu harka.

Tafiyar awa daya da rabi takai ta kauyen da ake hawa mashin daga bakin titi zuwa kauyensu, sai dai kanta ya daure ganin inda aka saukesu yanzu titi ne, tayi shuru sannan ta matsa kusa da wasu mutane ta tambaye su ko nan ake hawa mashin zuwa kauyen Nasu suka ce eh amma yanzu mota ake hawa saboda an shimfida musu titi, godiya tayi sannan taje wurin motocin tun kafin ta isa wani yazo yana tambayarta, ta daga masa kai ya nuna mata motar ta shiga bayan ta biya kudin, tana nan zaune kusan awa daya kafin motar ta Cika aka gama Lodi sannan suka kama hata.

Duk kusanci da sukeyi da kauyen yana kara bugun zuciyarta, faduwar gabanta na karuwa, tana jin tsoro, anya batayi kuskuren dawowa wannan kauyen Nasu ba? Anya za a karbe ta, to su iyayenta ma suna raye, mutanen garin zasu ganeta ko kuwa? Tambayoyin da take ta nanatawa zuciyarta kenan, ba su yi tafiya mai nisa ba suka iso, kowa ya sauka ya kama gabansa aka barta tsaye tana saka wasikar jaki, gani take kamar tana kusantar gida tashin hankali na kusantar ta, hawaye taji sun zubo daga idonta, Sam bata son tuno abubuwan dake yawo a kwakwalwa da zuciyarta.


*Safiyyah Galadanchi ke muku fatan alkhairi*

RUBUTACCIYAR K'ADDARAWhere stories live. Discover now