BABI NA ASHIRIN DA TAKWAS

677 45 1
                                    

*RUBUTACCIYAR KADDARA*

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
( *home of expert and perfect writers)*💡

*SOPHIE GALADANCHI* ✍🏼

28

"Deeni bawai bana son aurenku bane amma Safiyyah tayi kankanta da aure Sannan kana gani yanzu ss2 zasu shiga, roko daya zan maka idan zaka iya tunda bansan halin da kake ciki ba, sai kaje skul dinsu kayi magana idan final year students dinsu zasuyi waec sai ta shiga cikinsu, kaga sai tayi a ss2 kenan".

Gyada kansa yayi yana tunanin ya zaiyi da kansa, Sannan ya kalli Abba yace "kafin lokacin dama akwai course dinda muke so muje tare da Abubakar na wata shida da dai har nace ba zanje ba amma yanzu zan kirashi sai ayi process din, may be kafin lokacin tayi nisa" Abba ya amsa masa cike da gamsuwa Sannan yayi masa sallama ya fito, lokacin Safiyyah ta dawo daga islamiyya bata kalleshi ba ta shige gida, tun ranar da yace zai auri wata kafin ita take jin haushin shi, yi yayi kamar bai ganta ba badan yana son hakan ba kawai dai yanayin da yake ciki baya son yana kusanci da ita.

_zamu danyi agurguce saboda lokaci_

Duk shirin da ake bata saka kanta, fushi sosai take yi dashi, Dan ta nuna damuwa akanshi shine har zai daga yabar kasar gaba daya bai fada mata ba, ko kiranta ma bayayi karewarta ma yanzu shirin auren sa ake Dan ya kusa dawowa.

Tsaki a karo na babu adadi tayi tana ture littafin dake gabanta.
Dafe kanta tayi ta shiga tunani, wayarta tayi kara ta daga da sauri Dan ganin Halima ce.

Kafin tayi magana Halima tace "kanwata, baki bani labarin za a fito da lefen yayanmu ba gobe"  gabanta taji ya fadi amma ta daure tana cewa "nima dazu Anty take fadamin" Halima taji muryar Safiyyah wani iri amma batayi zancen ba sai tace "gobe insha Allahu zan shigo kafin lokacin kin dawo daga makaranta ko"?
Da ummm Safiyyah ta amsa mata sukayi sallama, Halima kam tayi mamakin sauyawar Safiyyah to kodai bata son Deen ne, amma gobe idan tazo dole ta tambayeta meyake damunta.

Mommy daga Kaduna tazo ita da yayanta, sunata murnar ganin juna, kuma da labarin zasu dade Dan sai anyi auren zasu koma, bangaren Anty su Momy suka sauko, duk yadda Anty take jin jiki amma dole ta daure saboda bazata yi kwance ga baki agidan b, batada Matsala da Momy Dan itama momyn batada matsala, kullum sukan zauna suyi hira, indai Momy nason tayi doguwar hira da Anty to bazatayi maganar cikin dake jikin Anty ba, daga zarar tayi to Anty zatayi gum da bakinta.

A gajiye ta dawo daga makaranta Dan yau registration suka tsaya yi na waec Dan haka yawo sukayi tayi, Allah ma ya taimaketa kawarta ma salma zatayi jarabawar shiyasa ta kara samun karfin gwiwa.

Tana shigowa gidan ta hango shi zaune cikin mota yana waya, kiba taga yayi ya kara girma, saurin dauke idonta tayi shikuma daya hangota sai hankalinsa ya koma kanta, horn ya mata ta juyo ya mata alamar tazo da hannu, sai da ta turo baki sannan ta karasa kusa dashi, ya rike hannunta kawai yana ci gaba da wayarsa.

Sai da ya gama wayar sannan ya kura mata ido har sai da ta tsargu, yace "yaushe raini ya shiga tsakanina dake"? Kallonshi tayi taga babu alamar wasa atare da shi a hankali tace " kayi hakuri" ya gyada kai yana cewa "jeki kawo min ruwa" ya fada bayan ya sake hannunta har ta shiga gida yana kallonta, ta kara girma sosai, da gangan ya tura ta dauko ruwan, managing kansa kawai yake shiyasa duk tsawon lokacin nan yayi kokarin shareta, yasan yadda suka fara haduwa a yanayinsa na yanzu baida tabbacin zai hana hannunsa kaiwa jikinta idan kuma hakan ya faru zatayi wani tunani na daban.

Shi da kanshi ya dauko Tela yazo har gida ya auna ta, daga lokacin ta gano abinda suke nufi, babu dadewa Abba ya aika kiranta, a dakinsa ta sameshi ta zauna daga gefe bayan ta gaidashi ya kalleta yana cewa "nasan kun gama dinkewa da yayan naki shiyasa kawai muka saka rana, amma dai lokacin naga yayi kusa tunda baku ma fara exam ba amma dai kiyi hakuri haka Allah ya kaddara, duk da yayanki bai fada min ba nasan akwai matsala ta gefensa idan anyi auren zai miki bayani, sai maganar zuwa dubo kayan daki nace abarki ki zaba dakanki, Halima tace zatayi kokari tazo Ku tafi tare, ya mika mata jaka mai girma yace invitation cards ne aciki sai kuje Ku raba"
Da faduwar gaba ta baro sashen, kenan koda zasuyi exams da aure akanta, wannan wace irin rayuwa ce, kamar a film.

Momy ta kalli Halima dake zaune tace, "Ku banga kuna gyaran yar kanwar taku ba" cikeda kunya Halima tace "na zata kune zakuyi ai momy, da har zan kira wacce tamin" tsaki momy tayi tana kallon Hindu tace "Hindu kuje kuyi magana Ku kai yarinyar can kinga dai mahaifiyarta ba lafiya gareta ba kuma koba komai ba ita ya kamata tayi ba tunda kuna nan" mikewa sukayi suna dariyar shakiyanci suka fita.

Kallon abin tayi a Kofi tana yamutsa fuska, Halima tace "ke munafuka, duk can takalminmu ya tsinke, kisha abinki Dan munsan babu abinda baki sani ba".

Kawaayenta sai mamakin wannan lamari suke ranar kunshi duk sun zo suna zaune ana zana musu lalle bayan an gama mata, Deen ya kira ta yana waje, sai da ta kare musu kallo taga duk hankalinsu baya kanta ta sulale ta fita.

Ya kasa dauke idonsa akan lallenta a hankali yace "jibi zan nunawa lallen nan Kaduna, zan kuma biya kudin lallen" kasa tayi da kanta tana murmushi.

"Alhmdllh munyi Sara daidai da gab'a" magajiya ta fada da karfi, jin muryarta yasa Safiyyah dagowa da sauri gabanta na matsanancin faduwa.

Deen mamakin ganin su yayi har ya soma tunanin kalar rashin mutuncin da zai musu sai yaji magajiya na cewa.

"Yauwa ke lubabatu mika masa y'arsa".

_ina ci gaba da muku fatan alkhairi_

RUBUTACCIYAR K'ADDARAWhere stories live. Discover now