*RUBUTACCIYAR KADDARA*
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
( *home of expert and perfect writers)*💡
*SOPHIE GALADANCHI* ✍🏼
35
Jiki a sanyaye ta shiga part dinta, daga kitchen taji motsin Deen ta lek'a sai ta samu kanta da tsayawa kallonsa, ya gama soya kwai ya juyo sai ganinta yayi a tsaye idonta nata kyalli ya ajiye plate din hannunsa yazo kusa da ita tareda riko hannunta.
"Yaya yanzu su Abba sunfi son y'an biyun can akaina ko? Sunfi farin cikin haihuwar su akaina ko"? Hawaye suka zubo daga idonta jikinta har rawa yake.
Sai da ya janyota suka dawo Palo ya dorata kan kafafuwansa yace "haba sweety wannan wane irin tunani ne? Kannen naki da zaki taya mu farin cikin samunsu? Kar in sake ganin hawayen nan daga yanzu idan akan wannan maganar ne, kinsan ko mahaukaciya idan ta haifi Dan dabatasan ubansa ba to ko kuda bata kaunar ya taba mata shi, balle ke da kaddara ce ta saka zuwanki duniya a lokacin da Anty ta haife ki babu wanda takeson gani kuma babu Wanda take sonji kusa da ita kamar ke, duk wahalar da tayi saboda ke ne, yan biyu da kike gani bazasu taba samun gata da soyayyar da kika samu ba daga wurin Anty har Abba, kinsan saboda me?" Ta goge fuskarta tana girgiza masa kai alamar a'a yaci gaba da cewa "saboda a lokacin Anty bata tareda kowa sai ke Dan haka tafi duk Wanda yake tare da ita sonki, Abba kuwa bai taba haihuwa ba sai gashi yaji labarin abinda ya faru Anty nada ciki duk da a lokacin bansan wahalar da yake ta meye ba amma tabbas yasha wahalar Neman Anty saboda ke tun bai San mai aka Haifa ba yake matukar son cikin nan Dan haka ki kwantar da hankalinki abinda yakeda banbanci a tsakaninku kadan ne kuma tunda gani ai bakida damuwa" ya karasa maganar yana Neman bakinta, tayi saurin matsawa tana murmushi tace "banfa wanke baki ba" ya riketa sosai yana cewa "ko jikin ai ba a wanke ba balle bakin kuma haka nakeson abina yanzu" tayi shuru tana sauraren abinda yake mata Halima ta kwankwasa kofa, ta Dan motsa tana kokarin barin jikinsa ya sake riketa duk mai kwankwasa kofar nan sedai ya shigo ya gansu ko kuma ya hakura.
Tana fitowa daga wanka a dakinta taga Halima a zaune gefen gado ta juyo suka hada ido, Safiyya tayi saurin dauke idonta Halima tayi murmushi tana cewa "abinda kika dawo Kuyi kenan nazo inata kwankwasa kofa bakwama jina, ko yanzu ma banjira ba ina murdawa naga ta bude".
Safiyyah ta zauna tana cewa "Aiko banji buga kofarki ba Dan koda Na dawo bacci yake nikuma sena gyara kayan guga da aka kawo jiya" Halima ta kwada mata harara tace "munafuka yaushe kika iya sharara karya haka? Yi maza ki saka kayanki ni zaki rakani unguwa ne" tayi dariya kadan sannan ta fara shiri.
Tana saka Riga Deen ya shigo dakin yana cewa "zanje wurin abubakar Akwai kayan da suka iso jiya da dare" ta amsa da to tana cewa "Yaya Halima tace zan rakata unguwa" yana tafiya da alama Sauri yake yace "to Allah ya kiyaye hanya" baima lura da Halima dake kwance ba.
Halima tabi bayansa da kallo tana cewa "lallai Safiyyah kin iya kiwo kinga kibar da yayana yayi" tana janyo mayafi daga wardrobe tace "shima shekaranjiya haka yace wai nasa ya zama kato harda naman wuya yayi" sukayi dariya a tare sannan suka fito.
Part din Anty suka shiga bata palon sai babyn daketa tsala ihu a daki, dasauri suka shiga Safiyyah Na cewa "ina Anty ta tafi tabar yaro haka yanata kuka" Anty ta dago daga gefen gado da fitila a hannunta tana cewa "Ruwan zam-zam nake Neman Na manta inda Na ajiye duk ya tsotseni ruwa zan bashi tunda yaki yayi shuru" Halima tayi dariya tace "Anty tun yanzu?" Murmushi kawai tayi ta dago bayan ta dauko ruwan, ta karbe shi suna shirin fita sai ga Hajiya ta shigo suka gaisa ta zauna a Palo, Halima ta koma daki ta kira Anty sannan suka wuce.
Anty tayi mamakin ganin Hajiya amma ta daure suka gaisa Hajiya tace "ni banma San kin haihu ba sai shine ya kirani yanzu Dan yashiga wurina nikuma ina wanka lokacin, sannu Allah ya raya mana, Anty tayi murmushi tana amsawa cikeda rashin sabo, tana kallon Na hannunta tace " naga kamar yana ciwon ido?" Anty tace "nima se yanzu Na lura amma yace zai turo Dr danni dai lafiyata qlw nace ba zanje ba" Hajiya ta mike tana cewa "zan kirashi yanzu naji idan bai kiraba sena kira Dr din Dan yanzun haka hankalinsa ya dauku".
Anty ta amsa da to kawai, tana ta mamaki, babu dadewa ko sai gata ta dawo suna hira da Dr din suka shigo ta rubuta magani suka fita.
Ranar suna ko gida ya Cika yan jega da yan garinsu Anty sai kai kawo ake da abinci. Wanda duk Hajiya ta dauki nauyi komai a part dinta akayi.
Washe gari kowa ya watse ana hutun gajiya.
Koda akayi arba'in umar da usman sunyi b'ulb'ul abinsu idan ko Hajiya Na nan dayansu yana wurinta, bata taba jin tanason haihuwa aduniya kamar yanzu ba amma tasan tunda har Abba ya haihu da Anty to matsalar daga wurinta ne amma dai bata cire rai ba.
Bayan shekaru biyar twins din Anty sun girma har an saka su makaranta halima ma ta haifi mace mai suna Aisha tana dauke da ciki Na uku.
Shekara biyar harda watanni da Auren su Deen amma Safiyyah ko bari bata taba yi ba, bai taba nuna mata ya damu ba amma tabbas tasan ya damu saboda tana ganin yadda yake masifar son yara duk weekend a gidansu Duke yi dayake sun koma gidansu, hakama yaran Halima, Aisha har ta zama yar gidan, shekara daya da aurensu ya samawa Safiyyah admission ta shiga jamia har ta gama yanzu tana final year.
Daga makaranta ta wuce gidan Halima zata dauko Aisha, Halima ta kalleta tace "kanwata wannan karon Na hango babynmu wallahi" Safiyyah tana shan ruwa ta ajiye cup tace "ki daina saka mini rai mana" Halima ta mike tana cewa "tashi mu shiga gidan makociyaya kiji idan karya nake" dariya kawai Safiyyah tayi tabi bayanta suka fita kamar wasa tana tambayarta irin abubuwan da takeji tana bata amsa, kadan ne bataji daga cikinsu sai dai bata alakanta su da ciki ba ta dauka wahalar jarabawar makaranta ce. Matar tace "Halima gobe da safe ki kaimin ita, itace kanwarki da kikace aure shekara biyar bata haihu ba ko" Halima ta amsa da eh sannan suka fito.
Safiyyah tana tunanin yadda Deen zai ji inyaji tanada ciki, tayi shuru aranta tana cewa bazata fada masa ba sai ta dawo daga asibiti.
Washe gari tanata jira taga ya fita taga yaci gaba da baccinsa har takwas da rabi gashi karfe Tara zasu fita. "Bazaka fita bane yau"? Ya gyara kwanciyarsa yace " eh asibitin zamuje tare kin shirya ne?" Ta zaro ido waje aranta tace waya fada masa?
Dole ta shirya suka fita tare bayan sun dauki Halima, a hanya ya tsiri masifa yana cewa "Ku bakuda hankali mutum Na Neman Abu ana tsammanin yasamu amma ku k'i fada mai, surprise din banza" suka yi shuru kawai suna kallonsa.
Suna zazzaune kowa da abinda yake sak'awa aransa kafin abasu result.
Lokacin da aka basu result din har mutumin dake lab din saida ya samu kyautar kudi awurin Deen.
YOU ARE READING
RUBUTACCIYAR K'ADDARA
FanfictionLABARIN UWA DA Y'AR TA WANDA YAKE CIKE DA TAUSAYI DA AL'AJABI, KUYI KUTSE A CIKI DOMIN GANIN ABINDA YAKE FARUWA.
