*RUBUTACCIYAR KADDARA*
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
( *home of expert and perfect writers)*💡*SOPHIE GALADANCHI* ✍🏼
*I just want to use this opportunity to say something important which ina tunanin may be zai b'ata ran wasu, naga ana son a lakabawa marubuta wayanda basu da aure sharri, wata tana cewa budurwa zata koyar da matar aure yadda zata zauna da mijinta saboda rainin wayo, na tabbatar akwai budurwar da tafi wata matar auren Hankali da sanin yakamata, nidai zuwa yanzu banga buduwar da ta rubuta novel na batsa ba, saboda haka ina rokonku da kuma Baku shawara, idan kin karanta novel, kiyi kokari ki tsinta abinda kika San alkhairi ne kuma daidai ne ki ajiye shirme, wasu dayawa basuda jigon labari sai na iskanci babu abinda kuma zaki samu sai zunubin da za'a raba muku keda wadda ta rubuta, duk Wanda yayi dai dai yasani Wanda yayi sabanin haka ya sani. Nagode.
25
Mamakin duniya ya ishi Abba, ya rasa Inda Hajiya ke zuwa, duk acikin Abubuwan da takeyi yana kyaleta baya lamuntar yawo haka kawai kullum cikin yawo sai kace kudi, wayarta ya kira saida tayi ringing tana katsewa har sau biyu a na uku ta daga yace "kina ina"? Kamar a gabanta yake tace "ina gidanmu" karamin tsaki yayi yace "ki dawo yanzu kuma wallahi kika sake fita bada izinina ba zakiga other side of me Wanda baki sani ba" yana gama fadar haka ya kashe wayarsa ya kwashi kayansa ya koma part din indo, ko yunwar da yake ji kadai ta isheshi.
Lokacin daya shiga ya same ta tagama girki tana zaune k'asan carpet tana ci yana, sallama yayi ta amsa ya karasa shigowa palon, tuwon ya burge shi bai tsaya wasa ba ya wanko hannunshi ya zauna ya soma ci.
Duk da bata karasa sakewa dashi ba haka taci gaba daci har suka cinye ta kalle shi tace "A karo ne"? Da kai ya amsa mata, ta dauki plate din ta shiga dashi kitchen babu dadewa ta fito ta ajiye mai ita har ta wanke hannunta, ya kalleta yace "ina zakije kuma"? Tana kallon kofar dakin da su Safiyyah suke tace "nakoshi, yaran can zan tada suci abinci ga kayansu dake can gidan ma basu gama kwasowa ba" sai da yakai loma ya hadiya sannan yace "idan kin fito kisame ni adaki zamuyi magana" da to ta amsa masa sannan ta nufi dakin.
Sai da ta gama kare musu kallo, Ashe da rabon Safiyyah zata yi kiba duk wannan kashin wuyan ya cike, zuwa tayi kusa dasu ta kira sunansu, Halima ce ta fara mikewa ita dama baccinta bai yi nauyi ba.
"Ku tashi kuci abinci tundazu kunata bacci" indo ta fada Tana kallon Halima, kafin ta fita Halima ta tada Safiyyah sannan suka koma palo zasuci abincin.
Indo kuwa dakin Abba ta shiga da sallama, ya gama cin abincin yana zaune shuru ya kalleta yana cewa "da ba Dan karna katsewa Safiyyah karatu ba dana aurar da ita" dariya kadan tayi tace "hakan ma ba matsala bane tunda ta isa Auren" shima dariyar yayi yace "dagaske nakeyi, wannan nuruddeen jiya yazo min da maganarta"
"To Allah ya sanya alkhairi"
Ya kwanta yana cewa "Ameen, Deeni d'ana ne, kuma ina so yayi aure, naji dadin daya nuna son Safiyyah saboda ina tunanin wurin samun miji za a yimata gori kasancewar mafi yawa daga cikin mutane sun San ban taba haihuwa ba, Bana shaidar Deeni amma abinda zahiri yanuna dashi zanyi amfani, ina fatan Allah ya kara shirya mana zuri'a, yace gobe insha Allahu zai shigo ya gaidake, yanayin aikin kampanin nan ne sai a hankali duk shine karfin aikin" kadan tayi murmushi tace "Ameen, Allah ya kaimu, ai yaran yanzu ba a shaidarsu domin bayan idonka baka san abinda yake faruwa ba, kai dai ka bawa yaranka tarbiya ja kuma bisu da addua" ya amsa yana riko hannunta yace "zo ki fadamin sirrin kibar nan, ba yadda zanyi ba ni har yanzu babu Wanda yacemin nayi kiba" tayi dariya tana kwace hannunta tana cewa "tuwo ne, ka tashi ka koma can bangaren in bakada wurin zuwa har yanzu Hajiya tana da sauran lokaci" yamutsa fuska yayi ya kwanta bayan ya saki hannunta yace "jibi zamuje Jega, zamuje ki gaida Hajiya jiya ta kira ni tana mita ban kawo Ku ba" duk da gabanta ya fadi amma sai ta daure tana cewa "ai da gaskiyarta Allah ya kaimu" bai amsa ba Dan tunda ya koshi yaji bacci ya taso masa.Fitowa tayi ta bar masa dakin sai ta samu Halima tana ta sheka amai a palon, da Sauri ta karasa kusa da ita ta rikota tana Shafa bayanta tace "subhuhanalillahi Halima, meya sakaki amai haka" Safiyyah tayi raurin bata amsa tana cewa "tun jiya fa mama batada lafiya amai da gudawa take daga taci abinci" Anty ta kalli Safiyyah cike da takaici tana cewa "wasu irin sakarkaru ne Ku da bazaku fada ba akaita asibiti" sai da taja baya sannan tace "Anty kiyi hakuri ita tace ba komai bane wai idan tasha madara tashin zuciyar zai sauka dama Dan taci Abu me maiko ne" tsaki Anty taja ta nufi fridge sai da ta fasa kankara ta zuba a cup sannan ta zuba madara tazo tana bawa Halima abaki, awurin tayi bacci tana sauke ajiyar zuciya. Safiyyah ko ta gyara wurin.
Waya Safiyyah ta kira Deen ta fada masa ya siyo yaya Halima magani sun kare kuma yau batada lafiya, yace "ke meyake damunki"? Tayi shuru tace "mekaji"? " muryarki ta canza" tace "bakomai fa may be mura CE" ya amsa da OK ta katse kiran.
Lokacin da yazo kawo maganin Anty tana zaune kusa da Halima ya kwankwasa kofar, Safiyyah ta bude, as usual da waya a hannunsa yana dannawa, yanayin tsayuwar da yayi yasa Anty taji kamar ta sanshi, gabanta ya fadi ta sake kallonshi, wata zuciyar tace mata "ba mamaki wani wurin na taba ganinshi" ta amsa masa sallama tana murmushi.
Shi dinma daya kalleta ya sake yin dana sanin abinda ya aikata, wani gefen ya godewa da bai aikata ba, yaji dadi da Allah ya jeho su cikin rayuwarsa, maganganunsu sunyi tasiri a gareshi Dan sun karkarto dashi zuwaga hanya madaidiciya.
Ya durkusa yana gaida ita, yace "Anty sai kuka tafi lokacin babu sallama"? Tayi murmushi tace " Bamu so hakan ba muma Deeni Allah ne ya kaddaro" ya girgiza kai yana cewa "nagodewa Allah da ban wulakanta ahalina ba, danasan yan uwana ne da sai dai ni na zauna a dakin dana Baku Ku kuma Ku koma cikin gida, duk da haka naji dadi Dan nasan na taba kulawa a gefen da ta zame min alkhairi" kallon shi tayi tana jinjina irin kimarsa tace "Allah ya biya yasaka da alkhairi ya kuma albarkaci rayuwarku, Abbanku yacemin an saka ranar Halima" ya gyara zamansa yana cewa "insha Allahu, dazu ma Muhammad din ya kira ni yace za aje ganin gida, to ina so na kira momy ta Kaduna ne naji suwa zasuje" ta mike tsaye tana cewa "idan an fadi masu zuwan sai a fadamin" ta fada tana shiga kitchen.
Ya kalli Safiyyah data zauna gefe kamar babu ita a wurin ya kanne mata ido daya, tayi dariya tana cewa "bari a kawo maka ruwa, tana mikewa Anty ta fito da plate din abinci da kwalin five alive.Dagaske yana jin yunwa shiyasa bai yi gardama ya karba yana ci bayan yayi godiya.
Ranar asabar da sassafe suka shirya zuwa jega, duk da Halima tana jin jiki amma ta daure.
_ina muku fatan alkhairi_
![](https://img.wattpad.com/cover/210952048-288-k453654.jpg)
YOU ARE READING
RUBUTACCIYAR K'ADDARA
FanfictionLABARIN UWA DA Y'AR TA WANDA YAKE CIKE DA TAUSAYI DA AL'AJABI, KUYI KUTSE A CIKI DOMIN GANIN ABINDA YAKE FARUWA.