*RUBUTACCIYAR KADDARA*
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
( *home of expert and perfect writers)*💡
*SOPHIE GALADANCHI* ✍🏼
(19)
Wallahi ji yake kamar yanada damar da zai dauki yarinyar nan, yaje ya nunawa danginsa ita, bayan shekaru dayawa daya shafe yana Neman su, sai gashi ya gansu a saukake kuma baya tunanin koda sau daya Aisha da iyayenta zasu wulakantashi.
Rasa abin cewa yayi sai kallon Safiyyah yake, ita kanta ta tsargu da irin kallon da yake mata da magana a bakinta amma rashin sanin sunan da zata kira shi da shi yasa dole tayi shuru, mintuna kadan ya katse shurun da cewa "a ina kuka zauna"? Idonta na kallon kasa tace "a sokoto" yayi murmushi yana cewa "kenan kinyi makarantar boko"? Ta dago da hannunta da yatsu biyu tana cewa "ina SS2 yanzu, munzo salla inna da Baffa sun hanamu komawa" wayarsa ya Ciro daga aljihu yana cewa "Su Baffa sun kyauta min, da sun barku kun koma wata kila da banganku ba, na shafe shekaru goma sha biyu ina yawon kauyen nan ba tare da na gaji ba saboda kawai inji ina Aisha ta tafi da abinda ke cikinta, ni nasan nayiwa Aisha laifi ina fatan zata yi hakuri ta yafemin" Safiyyah tace "Anty bata dogon fushi, nima idan nayi mata laifi daga Na bata hakuri shikenan ta daina fushi dani" ya sauke ajiyar zuciya dan ya fara tunanin Safiyyah bata san abinda ya faru ba, ya riko hannunta yana cewa "zoki zauna ga takarda ki rubuta min duk abinda kike so zan kawo miki gobe, sannan kuma ki rubuta min lambar wayarki" cikin idonsa ta kalla tace "bana bukatar komai kuma kaga mu bamuda waya fa ko anty bata taba rike waya ba" bude mota yayi ya dauko wata wayar ya mika mata bayan ya cire layi daya daga cikin biyun dake kan wayar yace "karbi wannan, wayata ce da layina aciki babu Wanda yake da layin sai mutane kadan ba a yawan kirana da shi" ta kalli wayar babbace sosai bata taba ganin irinta ba ta matsa baya tana cewa "Anty bazata yadda ba bazan amsa ba" sai yaji babu dadi, yarinyar bata san kowa ba sai anty, hannunta yaja suka koma cikin gidan sai da yayi sallama sannan aka bashi izini ya shiga, kallon indo yayi yace "Safiyyah ke kadai ta sani, ki fada mata duk abinda zanyi bazan cutar da ita ba, idan na bata Abu ko nace tayi kar tayi min musu" kallon da tayiwa Safiyyah yasa ta dan fahimci magana take sannan tace "Abbanki ne kiyi abinda yake so indai ba ya sabawa addinin mu bane" gyada mata kai Safiyyah tayi shikuma ya ajiye mata wayar sannan ya mike yace "yamma tayi zamu tafi, Safiyyah ki ajiye wayar kusa dake zan kira kinji zamuyi magana" tana murmushi tace to, ya Shafa kanta yana mikewa tsaye sai kuma ya sake sunkuyawa gaban Safiyyah yace "ga wannan kafin na dawo gobe" ya fita da sauri yana yiwa su Baffa sallama.
Mukhtar dake tsaye jikin mota ya kalleshi yace "amma wallahi ka cuceni, yazaka barni iskan kauye na hurani haka tun safe, kaga mutane sekace kaga zinari" ya fada yana tsaki kadan cike da jin haushi, Abdullahi ya kalleshi bayan ya zauna cikin motar yace "sunfi min duk duniyar nan da abinda yake cikinta, kai inbanda su yan nan ne kana tunanin zasu daga min kafa bayan abinda nayi musu? Y'arsu nayiwa mummunan tabo Wanda bazai taba goguwa ba, duk halin da suka shiga ta dalilin abinda na aikata inada nawa kason aciki, da ban gansu na roki yafiyarsu ba na tabbata hakkinsu kadai Seya hanani kwanciyar kabari, mukhtar ni babu abinda zanyi daya wuce na kwana na wuni nakuma kare rayuwata ina yiwa Allah godiya, ko yayane ina ganinsu a matsayin haske ga rayuwata".
Shuru mukhtar yayi yana nazarin kalaman da Abdullahi ya fada.
Har suka iso babu Wanda yayi magana, sallar magrib suka tsaya a masallaci sukayi sannan sukaje banki mukhtar dama abinda ya fito dashi kenan, Abdullahi kuwa bukatar hakan ta taso masa ne lokacin da yaje kauyensu indo.
Sai da ya sauke mukhtar gida sukayi sallama shikuma ya kama hanyar gidansa.
Bayan sallar ishai suna zaune a dakin da suke kwana safiyyah ta kalli indo tana murmushi tace "Anty wai ya akayi aurenku ya rabu da babana"? Wani dummm indo taji kanta yayi ta dago tana kallon Safiyyah ta kasa cewa komai, ta kasa sauraren shawarar da zuciyarta take bata amma kuma ya zama dole ta bayyana ko yaushe ne dole Safiyyah zata ji ta hanyar data zo duniya, musamman da suke zaune wannan kauyen su suka san komai, tunaninta ya katse jin Safiyyah ta sake maimaita tambayar.
A hankali ta kalli safiyya tace " ba ayi aurenmu bama balle mu rabu, bada aure aka samu cikin ki ba" da sauri Safiyyah taja baya tana sake kallon indo, kamar ta fahimta kamar kuma bata gane me anty take nufi ba.
"Safiyyah zuwanki duniya kaddara ce rubutacciya, ba son zuciya yasaka cikin ki shiga jikina batareda an daura min aure ba, banida yadda zanyi, banso haka ba Safiyyah, abinda yasa ban fada miki ba saboda bukatar hakan bata taso ba, yanzu kuma lokaci ne daya kamata ki sani saboda boye miki ba Abu bane da zai fiddamu har ke, ko yaushe ne ko yayane dole watarana kiji" Safiyyah ta fashe da kuka ta zauna kasa tana cewa "Anty yanzu ni shegiya ce? Innalillahi wainna ilaihirraji'un, Ya Allah ka dauki rai..." Kafin ta karasa inna ta rufe mata baki tana girgiza mata kai "karki sabo Safiyyah, kinsan babu wanda zai tsallake abinda Allah ya kaddara masa, dukanmu nan har abban naki babu Wanda yaso faruwar abinda ya faru, bakida laifin komai, bakida banbanci da Wanda aka Haifa ta hanyar aure, duka musulmi daya ne a wurin Allah sai Wanda yafi wani tsoron Allah kiyi hakuri kar wannan yayi sanadin lalacewar rayuwarki, ki godewa Allah ki tabbatar da kina cikin gata bazaki gane hakan ba sai kinje gidan marayu dayawan su basu san iyayensu ba kuma har su koma ga Allah bazasu san waye uwar su waye ubansu ba, Allah yayi miki ni'ima da kika san iyayenki kuma kika rayu tare dasu" tana gama fadar haka ta fita daga dakin, indo taci gaba da kallon Safiyyah da yanda take kuka, aranta tace "gara kiyi kukan tun yanzu".
Har washe gari da safe Safiyyah bata saki ranta ba, abinci ma taki ci kuma har lokacin indo bata lallashe ta ba.
Suna zaune shuru Abdullahi yayi sallama ya shigo dakin, tun da yaga fuskokinsu yasan akwai matsala sai ya matsa kusa da Safiyyah ya dago fuskarta yana kallon yadda tayi ja sosai idonta duk sun kumbura yayi ya zaro ido waje yana cewa " meya faru" Safiyyah tayi shuru sai yaji indo tace
"Kuka take saboda taji ita wacece" ta sauke ajiyar zuciya sannan taci gaba da cewa "nima akwai lokacin da nayi kuka kamar haka, ina ganin kamar bazan kuma rayuwa mai dadiba, nida aka kutsa kai cikin rayuwata aka tarwatsamin ita, shekaruna talatin a duniya amma har yanzu ni budurwa ce, akwai abinda yafi wannan ciwo, nayi kuka wuni da kwana, duk lokacin Dana kalli cikin jikina sanadinshi nabar gaban iyayena, ban fara jin sassauci a zuciyata ba saida na haifeki, lokacin da banida kowa sai ke, har yanzu bansan sunan rayuwata ba Safiyyah ki godewa Allah".
Shuru Abdullahi yayi saboda bashida abin cewa, abinda yake yiwa gudu kenan, zuwan irin wannan ranar uwa da ya suna kuka a gabanshi ta dalilin shi kuma.
Juyawa sukayi a tare suna kallon yaran dake shigowa da kaya.
_kuyi hakuri da wannan pls kuma ga post cikin dare duk banso haka ba aradu_
YOU ARE READING
RUBUTACCIYAR K'ADDARA
FanficLABARIN UWA DA Y'AR TA WANDA YAKE CIKE DA TAUSAYI DA AL'AJABI, KUYI KUTSE A CIKI DOMIN GANIN ABINDA YAKE FARUWA.
