BABI NA TALATIN DA HUDU

829 47 1
                                        


*RUBUTACCIYAR KADDARA*

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
( *home of expert and perfect writers)*💡

*SOPHIE GALADANCHI* ✍🏼

34

Jikinsa yayi matukar sanyi, ya gama saka ransa da ciki ne ajikinta, wani murmushin yak'e kawai yakeyi yana rike da hannunta lokacin data farka ana mata karin ruwa.

"Ya akayi sauro ya sameki haka yaita ciza duk da farar fatar nan"?
Ta juyar da kanta kawai tanajin yadda jikinta yayi wani iri, bata taba yin zazzafan zazzabi irin wannan ba.

Takardar dake hannunsa yasake kallo yace " wata rana zan karbi irin wannan mai dauke da positive insha Allah " tana jinshi tayi shuru ta shareshi, babu dadewa Anty tazo tareda Halima, ya durkusa yana gaida anty ta amsa tana kallon Safiyyah data rufe ido kamar mai bacci.

Ya kalli halima yace "sannu kekam, da jaririn kika fito? Ai dakun zauna a gida dan yanzu ruwan ya kusa karewa zamu wuce gida" tunani Anty kawai takeyi har bata San lokacin data tambaya ba tace "meye yake damunta"? Deen yadan kalleta yana mamaki bai yi zaton zata tambayeshi ba yace " malaria ce kawai kuma zazzabin ya sauka" a boye ta sauke ajiyar zuciya sannan ta nemi kujera ta zauna tana ci gaba da tunani.

Shirin zuwa ziyara jega suke Muhammad yace lallai shi bazai yadda ba daga tayi arba'in zata dawo shiyasa zasu tafi yanzu, lokacin da suka isa mutanen sunyi murnan ganinsu kwana daya sukayi suka kamo hanyar dawowa, Deen daya daukosu sai ya biyo ta kauyen su Anty dasu, sosai Safiyyah taji dadi sai dai babu sabo tsakaninsu da mutanen garin, sai dai ma Hafsa kanwar anty wadda ake shirin aurenta babu dadewa.

Inna tana son tambayar anty amma tana jin kunya dakyar ta iya tambyar suna lafiya Safiyyah tace "suna nan lafiya lau muma daga jega muke shine muka biyo tanan anty tana can sokoto jikinta yayi nauyi ne" karshen maganar yasa ta kasa amsawa amma har kasar zuciyarta taji dadi.

Shirin komawa Halima tayi anty dai taga yarinya ba dangin uwa a kusa dole gyaran nan itace zata yishi, dakanta ta shiga makotansu wurin wata mata duk da dai ta girmeta saboda yayanta ma sun girmi Safiyyah har an aurar dasu, matar tana ganinta taji dadi sosai ta zauna tana cewa "Hajiya dakan ki kika shigo haka da wannan nauyin" tayi murmushi kawai tana gyara zamanta bayan sun gaisa Anty ta daure tace "kinsan Halima ta kusa arba'in shine nazo inji ko zan turo miki ita ne ko zaki aiko da sakon.." Ta kasa Karasawa matar mai suna ramatu tayi dariya tace "karki damu ba sai kin turo ta ba insha Allahu anjima zan shigo dakaina" Anty tayi murmushi kawai ta mike tana mata sallama.

Tana shigowa gidan ta samu Muhammad da Deen a harabar gidan, farin cikin dake fuskokin Safiyyah da Halima ya nuna mata suna cikin nishadi, gaisawa tayi dasu Deen anan Safiyyah ta nuna mata sababbin motocinsu iri daya bakake masu kyau, Addua tayi musu ta shiga gida.

Anan Deen da Safiyyah suka bar Halima suna magana da Muhammad.

"Yan mata bazaki je dandana motar ba" sai da ta kalleshi tace "ban iya ba ai dan samari" ya riko hannunta yace "muje ki biyani sannan na koya miki" ta zaro ido waje tana cewa "kai na gaji yau sau uku fa kenan, kabari muci abinci mana" yadda tayiwa fuskarta ya bashi dariya yace "to shikenan amma sai randa kika biya zan fara koya miki" tabi hanyar kitchen tana cewa "eh nadai ji".

Yau asabar dan haka Deen da Safiyyah baccinsu suke har karfe goma, acikin bacci Deen yaji ana buga kofar part dinsu, tsaki yayi sannan ya mike ya saka jallabiyarsa ya fita, muryar Halima yaji tana magana awaya yayi saurin budewa yana kallonta, ta sauke wayar daga kunnenta tana cewa " kuda kuke nan gidan bakuji anty ta haihu bane kunshige kamar babu ku a gidan Yaya" ya zaro ido yana cewa "yaushe"? Ta juya tana cewa "yau da safen nan fa inaji ko Abba bai sani ba dan kamar baya gidan" shima juyawa yayi ya koma cikin gida saboda ya tashi Safiyyah, azaune ya sameta da hula a hannunta tana shirin sawa yace "tashi kije part din anty kigani Halima tace ta haihu" mikewa tayi tabi hanyar fita yayi saurin jawo hannunta yana kallon rigar jikinta har pant dinta ana hangowa yace, "malama ki saka hijabi da zani ko" sai a lokacin hankalinta ya dawo jikinta, cikin sauri ta daura zanin tasa hijab ta fita.

A Palo ta samesu zaune anty tana dauke da dayan ta shayar dashi taga kuma halima dauke da daya, ta zare ido tana murmushi Halima ta daga yatsunta biyu sama tana cewa "twins duka maza" da sauri ta karasa kusa da halima ta karbi dayan tana murmushi, fari tas dashi gashin kansa kamar ya hade da gira, rahmatu ta fito daga dakin tana cewa "Hajiya bari naje gida zuwa anjima zan dawo amma dan Allah ki kwanta ki huta" ta gyada mata kai kawai.

Tana fita Abba na shigowa, a bangaren Hajiya ya kwana. Yana tashi kuma yafita jana'izar baban abokinsa da ya rasu cikin dare, daga can ya tsaya wurin gaisuwa shine fa yana can Deen ya kira shi.

Jikinsa har rawa yake ya karbi na hannun Safiyyah yaje kusada Anty ya zauna, yayi mamaki sosai, bata fara zuwa awo ba saida cikin yayi wata bakwai tasan yan biyu ne ko bata sani ba.

A bangaren anty kuwa ta sani amma bata taba fadaba, tunda batada matsalar komai.

Wani Abu ya daki zuciyar Safiyyah tana kallon yadda Abba yake daukar yaran yana ajiyewa, fuskarsa dauke da farin ciki, daga baya kuma sai ya soma Kiran waya yana sanarwa yan uwa da abokannan arziki, tayi kokarin maida hawayenta, Allah sarki  ita duk wayannan gatan ko daya bata samu ba, ta tabbatar Anty tafi yin farin ciki da wannan haihuwar akan ta ta, ta kuma fi kwanciyar hankali da nuna wayannan yaran a duniya ta kuma ce ga ubansu, amma ita har yanzu zataji kunya da nauyin cewa itace ta haifeta balle ace ga ubanta ma tayi duk wannan tunanin azuciyarta.

Halima ta rike hannunta sosai saboda tasan me take tunani tace "matar yaya naga kinyi kiba" wani guntun murmushi tayi ta mike tana cewa "bari naje ko baki ban wanke ba" daga haka ta fita daga part din anty tabi bayan ta da kallo idonta suka Cika da ruwan hawaye.

RUBUTACCIYAR K'ADDARAStories to obsess over. Discover now