*RUBUTACCIYAR KADDARA*
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
( *home of expert and perfect writers)*💡*SOPHIE GALADANCHI* ✍🏼
33
Babu dadewa Halima ta tashi daga baccin da take, Deen ya matsa kusa da ita sosai ya rike hannunta yana mata sannu yace "kinji yadda mata suke ji ko? Haka mamanmu taji lokacin da zata haifeki, haka naji lokacin Dana kalli yaron nan, Allah ya albarkaci rayuwarsa ya baki lafiya" murmushi tayi ta kara rike hannunsa ta kalli Safiyyah dake dauke da babyn tace "haka wata rana kanwata zata haifa mana taji yadda anty taji" yayi dariya yacewa Safiyyah "kawo mata babynta ta gani kin kama kin rike mata" hararar wasa tai masa tace "idan naga dama bazan bata ba zan tafi dashi" yayi dariya yace "to ki gwada mana, da yau naga yadda Muhammad zai Cika min gida da motocin yan sanda har takalmin gidan sai an deba" sukayi dariya har Abba, Anty kam dama bata Cika yin fara'a ba musamman da cikin nan sai ta kawar da kanta kawai.
Kallon Abba tayi tana cewa "zasu sallame su ne yau"? Abba yace " eh takardar da Muhammad yaje karba kenan" ta sauke ajiyar zuciya tana cewa "Allah yasa dai subarmu mutafi gida ba sai sun mana wani k'ak'ale-k'ak'ale ba, wallahi bacci nakeji ga yunwa ma kuma tuwo nakeso" Abba ya tashi tsaye yana cewa "Deeni ku taho daga baya zan wuce idan da akwai wani Abu bayan tafiyarmu muyi magana a waya" Deen ya kada masa kai kawai saboda ya shagala da kallon yaron dayake matukar kama da Halima.
Anty ta kalli Safiyyah tayi magana da yarensu tace "ni na tafi bana jin dadi ina so na kwanta" Safiyyah tace "to Anty Allah ya kara lafiya" da yaren nasu" har zasu fita sai ga Hajiya ta shigo tana bata rai ta kalli Abba tace "banyi tunanin rashin muhimmancin nawa yakai ga halima ta sauka banjiba sai a bakin shanun talla, amma ai ita yar gwal din tare kuka zo saida aka sakota a gaba"
Abba ya kalleta yayi murmushi yaje kusa da ita yayi magana k'asa-k'asa yace "haba uwar gida, banfa san kin fita ba dan baki fadamin ba naje bangarenki kuma bakyanan nakira wayarki bansamu kin daga ba saboda kina fushi dani, yakike so inyi"?
Anty ta kawar da kanta daga kallonsu tana dan matsawa baya saboda bata kaunar turaren Hajiya.
Hajiya kuwa shuru tayi batada abin cewa matsawa tayi bata ko kalli inda Deen da safiyya ba, Deen dama bai wani damu da ita ba albarkacin Abba take ci.Abba yace "Hajiya mu mun wuce" ta tabe Baki tana cewa "ku jirani mu tafi tare hamza dama ya kawo dama Maman suhaila tadaukeni ban fita da mota ba" daga nesa taga yaron tace "Allah ya raya" Safiyyah kawai ta amsa mata tabi bayan su Abba.
Anty ta bata rai tana tunanin da gangan anty tace zata bisu saboda tasan bata son warin turarenta.Suna zuwa anty ta bude gaba ta zauna, Hajiya bata damu ba ta shiga baya, tunda suka zauna anty ta kasa hadiye yawu zuciyarta sai tashi take dakyar taga sun Isa gida.
Bayan fitarsu Abba Deen ya kalli Safiyyah yace "meyasa anty take juya harshe wani lokacin idan zata miki" ta kalle shi da gefen ido tace "tana jin kunyarku ne saboda bata son wani ya mata maganar cikin dake jikinta, shine ta fadamin zasu wuce saboda bata jin dadi" Deen yayi dariya kadan yace "to ai mu son cikin muke ma, kema yanzu banki ace kinada shi ba" shuru tayi bata tanka masa ba saboda ita gaba daya bata son taji zancen abinda ya shafi aure koshi kanshi idan suka kwana daki daya sai ta Dade bata saki jiki dashi ba da safe.
Halima tace "Allah ya kawo yayana da ranar bansan kalar murnar da zanyi ba" Safiyyah ta sake yin kasa dakai, Deen ya mike yana cewa "Ameen, bari na dubo Muhammad" ya fita Halima ta maida dubanta ga Safiyyah tace "kanwata naga kinyi fresh kodai kin harbu" Safiyyah ta dafe kirji tace "kin manta daga ranar bamu sake yin komai ba fa" Halima ta kwashe da dariya tace "hauka kenan, badai yayan nawa ba, kuma ai ko sau daya ne ba mamaki kiganki da cikin" tayi saurin yi kasa dakanta tace "dan Allah Yaya halima mubar maganar nan" halima zatayi magana Muhammad ya shigo yana cewa "idan zaki iya tashi mu tafi dan nacewa su Anty zaliha muna hanyar zuwa gida su sameki a can" saida ta dafa Safiyyah sannan ta tashi zaune tana yamutsa fuska, basuda wasu kaya dayawa suka tafi Deen ya kalli Safiyyah yace "ki bisu kuje gida, zanje duba wani Abu tareda abubakar sai dai na dawo bada dadewa ba".
Suna shiga gidan sai Safiyyah tayi bangaren Hajiya Halima tayi saurin riko hannunta tana cewa yarinya hauka kike yi wallahi bazan zauna wurin Hajiya ba" har zatayi magana Halima tayi gaba ta barta dole tabi bayanta.
Koda suka suka shiga suka samu Abba ya tsaya bayan anty yana jera mata sannu, Safiyyah ta kalli yadda ko tsayuwa anty ta kasa ta hadiye wasu yawu idonta ya Cika da hawaye Abba yace "wallahi tunda muka dawo take yunkurin amai amma yaki fitowa saboda ba komai a cikinta" Safiyyah ta goge hawayen da suka zubo ta kalli anty tace "Abba ku zamuje asibiti ne ya girgiza mata kai yace "Dr na zuwa yanzu yace zai kara mata kira Deeni dai a waya kice masa yayi kiran Hajiya inna daga jega idan babu damuwa larai tazo gobe saboda kula da halima" ta gyada masa kai tana kallon Anty dake kokarin raba jikinta Dana Abba.
A Palo suka yada Zango yan barka daga gidan su Muhammad na zuwa duba halima da babyn ta, anty dai tana daki tana baccin wahala. Sai goman dare Deen ya shigo sai mintsinin Safiyyah yake ta tashi su wuce tayi kamar bata jinsa, saida yaga banayi bane kawai sai ji tayi ya sunkuceta ta zaro ido tana kallonta shikuma ya dauke ido daga kanta sai part dinsu ya ajiyeta bayan ya rufe kofa ya soma Neman abinda yake kwadayi, ai daga nan bai sake jin bakinta ba sai washe gari da sassafe karfe bakwai ta fito ta shiga part din anty, sai da ta shiga dakin da Halima take taga Halima da anty sun kura mata ido, sai a lokacin ta tuno abinda ya faru jiya anty ta kawar da kanta tana cewa "zo ki karbi yaron nan zanje na kwanta ne" dakyar ta karbe shi ta zauna tana zare ido.
Anty na fita halima tayi dari ya tace "su safiyyah matar babban Yaya, wallahi kibar kaiwa dare inba haka ba watarana anan zai...." Ta kanne mata ido daya, kunya takamata sai kawai ta soma hawaye tana cewa "ni bazan ma koma ba ai sai an gama suna" tabe baki halima tayi tana cewa "aiko wata rana zakiga abin kunya dan yayana baya wasa kin sani"
Shuru kawai tayi tana goge hawayen idonta, ita kadai tasan wahalar da take sha jintake kamar ta kulle kayanta a zani ta gudu.
Saida aka kwana biyu sannan larai tazo daga jega, sosai take kulawa dasu halima tareda anty taji dadin zama tare dasu.
Yanzu lamarin Deeni ya habbaka har da rana sai ya dawo daga wurin aiki dasunan cin abinci ya nuna mata kauna.
Bayan anyi suna da kwana biyu zazzabi ya kayar da ita bata iya cin komai se fama da koren amai. Hankalin Deen duk ya tashi kullum dare a tsaye yake kwana saboda zafin jikinta daga karshe dai dole ya kwasheta suka wuce asibiti dan yaga Abu na Neman fin karfinsa.
Duk yadda aka cewa anty Safiyyah na ciwo bata yadda taje duba ta ba dan tagama yadda cikine aiko data shiga uku, Ita ciki y'a ciki wannan abin kunya.
Daga karshe sai da tayi hawaye dataji Abba na waya da Deen yana fada masa suna asibiti.
Lokacin dayaji dalilin hawayenta ya saki baki kawai yana kallon ikon Allah.
YOU ARE READING
RUBUTACCIYAR K'ADDARA
FanfictionLABARIN UWA DA Y'AR TA WANDA YAKE CIKE DA TAUSAYI DA AL'AJABI, KUYI KUTSE A CIKI DOMIN GANIN ABINDA YAKE FARUWA.