SHAFI NA TARA

785 61 6
                                    

*RUBUTACCIYAR KADDARA*

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
( *home of expert and perfect writers)*💡

*SOPHIE GALADANCHI* ✍🏼

(9)

Zuwa tayi kusa da ita ta riko hannunta tana dariya tace "Anty kin ko san tunaninki nake? Dan Allah kiyi sauri kisamo mana gida wallahi tunanin kawai nake ko kina lafiya" tana dariya itama ta kalleta tace "to ranki ya Dade ki bari mu karasa ciki mana", ta fada tana zama gefen korido din.

Huraira kuwa tanajin shigowarta tai mata Banza a daki dan haushinta take ji sai da Indo ta aika kiranta sannan ta fito fuska ba walwala, a take indo ta sha jinin jikinta ganin yau babu fuska kamar kullum.

A daddafe suka gaisa sai ga malam Buba ya karaso ya zauna yana ta Washe baki ya kalli safiyya yace " safiyyah anga mama hankali ya kwanta ko?", kunya tasa ta boye fuskarta bayan indo.

Sannan ya maida hankalinsa kan indo yace " to ya maganar tafiya gida?".
Sai da ta dan ja lokaci sannan tace "gaskiya tafiya yanzu ba mai sauki bace, na sake shawara hakanan zamu zauna a gidan kafin naga me na kama, daga baya zamuje har safiyyah din ma".

Ajiyar zuciya ya sauke kafin yace "to nidai ba shishshigi ko kaudi na miki ba amma naga gidan nan akwai daki, jiya na zauna da mai gidan nan na kuma roke shi ya amince, yace babu matsala zaku iya dawowa nan, kinga makullin dakin ma ya bani yace idan kika zo babu damuwa dan Na nuna masa yar uwata ce ke", shuru tayi tana tunani yayi saurin cewa " karki damu mai gidan nan ba shida matsala wallahi mutum ne kuma wanda yasan girman mutane kuma da alkhairi, kinga ko huraira daya ke ba fita suke ba shikuma baya zama wallahi sai su share wata biyu basu hadu ba tunda kinga a baya muke sai dai hali na ajizanci da baza a raba dan Adam da shi ba".

"Wallahi malam Buba na gode kuma insha Allahu bazan taba gajiyawa da yi maka addu'a ba, duk wanda ya dauki muhalli ya baka koda na kwana daya ne to lallai ya taimake ka, duk yawon da nake ina tunanin wurin da zamu zauna ne ga karatun safiyyah daya soma rawa yau anyi sati daya bata je ba duk dan saboda haka, Allah ya biya maka bukatunka na alkhairi ya albarkaci zuri'arka".

Ameen ya amsa yana jin dadi har cikin ransa ganin yadda take murna sannan tace " yanzu idan na koma zan karasa hada muna kayan mu dama ashirye nake da barin gidan nan" daga haka ta mike tayi musu sallama har huraira dake ta faman hura hanci, malam Buba ya mike shima ya koma bakin aikinsa a ransa yana cewa "kiyi kokari duk ladar da kika samu ki zubar da ita".

Safiyyah ma murna tayi sosai har tana bawa fadimatu labari, fadimatu kuwa tana taya ummanta kishi bata wani bawa hirar muhimmanci ba dole safiyyah tayi gum da bakinta.

Bayan isha'i indo ta nak'alci ido ya da kafa sun dauke a gidan kowa yana sha'aninsa dan haka bata wani baya lokaci ba taje ta nemo dan adaidaita sahu sukayi ciniki ya daukar mata kayanta.

Deen yana danjin hayaniya daga waje amma bai damu ba wata kila matar ce tazo amma idan zasu ringa surutu haka zai ce su rage musamman da daddare dan baya son hayaniya.

Saukar musu da kayn yayi sannan suka koma suka karasa dauko sauran ta rufe gidan sannan suka wuce tana jin kamar an cire mata kaya, daki biyu ne a BQ dinda ya basu da kitchen a gefe sai toilet ma a gefe kamar yadda su malam Buba suke, ta sallami mai adaidaita sahun sannan ta karasa shiga ciki, basu kwanta ba sai da suka gyara abinda zai gyaru a Daren sannan suka kwanta safiyyah tana jin daban, tunda ta tashi a can gidan ta taso amma yau ga shi ta baro shi har abada, tunanin da indo takeyi kenan itama har bacci ya daukesu.

Washe gari bayan azahar sun karasa gyaran gidansu komai anyi masa mazaunin sa mai kyau, suka zauna shan gari da madara sai sallamar malam Buba suka jiyo, fitowa safiyyah tayi daga dakin ta durkusa tana gaida shi ya amsa yana cewa "kirawo mamanki" yana rufe bakinsa ta fito da hijab dinta da ya kai har kasa, itama gaida shi tayi ya amsa yana nuna mata kayan abinci yace " Alhaji ne ya kawo dama duk wata yakan bamu irin wannan, to wannan karon ma yace har dake shine muka kawo miki", zaro ido tayi tana kallon kayan abincin to ita me kuma zata nema duk gatan da ake yi Allah yayi mata, tana rokon Allah ya biya wayan nan bayin nasa da mafificin alkhairi, takalminta ta sa tana cewa " malam ai bari muje muyiwa mai gidan godiya, malam Buba yayi saurin tareta yace " kwantar da hankalin ki maman safiyyah Alhajin ma ba zuwa yayi ba aike ne yayo wani can daban ya turo kinsan baya zama kwana biyu yace akwai aiki sosai a wurin aikinsu amma idan mun hadu zan masa godiya".

Cike da farin ciki tace "to babu komai Allah ya saka da alkhairi" ya amsa da ameen sannan ya juya suka tafi shida fadimatu data taimaka masa wurin kawo kayan.

Suna wucewa Safiyyah tace " mama Dan Allah in dafa taliya? Kinsan bana son gari tunda ga taliyar ansamu kuma akwai manja" murmushi tayi tace " sai kije ki dafa tunda anmiki magani da cin taliya kamar jaraba" sa fiyyah dai bata amsa ta ba, ta shiga hada risho a kitchen alhmdllh Allah ya rabata da shan gari dan bata son shi idan baiji madara sosai da gyada ba.

"Kambuuu.... Ni matar nan zata wulakanta? Inyi musu hanyar samun abin duniya amma ta kwashe kayanta rankatakaf ta bar gida babu ko sallama, wato su suka iya cin arziki ko? sun zama yan hannu ni za a nunawa barikanci, harda shi tsohon karuwin Nasu ya hada uwar da yar yana Mora, to basu san ta inda gizo yake sak'a ba, zasuga ainahin kalata wallahi" masifar datake tayi kenan yau tun da ta samu gidan a kulle tasa aka balle mata kofa wai zata wulakanta Indo saita samu babu komai na Indo da yarta a gidan sun kwashe sun bar gidan shikenan ta haukace.

Yau kam ta baci dan Deen kwana yayi tunanin inda zai sake ganin safiyyah tunaninsa ya tsaya cak akan magajiya, yanada tabbacin zatayi masa hanya sai dai ba kamar waccen hanyar ba, idan ya taso daga aiki zai nemeta awaya duk da ya san kwanakin nan ta matsa da kiransa amma baya dagawa dan gani yake kamar tana cikin masu ingizashi zuwaga Matan banza irinta.


_kuyi hakuri yayi kadan kuma gashi anyi dare, inada uzurin daya janyo hakan ne nagode_

*Safiyyah Galadanchi ke muku fatan alkhairi*

RUBUTACCIYAR K'ADDARAWhere stories live. Discover now