BABI NA TALATIN DA SHIDA

898 53 4
                                    

HWA

RUBUTACCIYAR KADDARA NA SAFIYYAH GALADANCHI.

36

Idan yace zai nunawa Safiyyah kalar murnar dayake, to tabbas zai aikata barna, sai da suka sauke Halima gida sannan ta zagayo tana fadawa Safiyyah magana a kunne tace "ke naga take-taken yayan nan wallahi kibi a hankali karya barar mana" Safiyyah tayi dariya tana toshe bakinta yace "munafuka wallahi innakama ki kina horewa matata kunne nidake ne" suka sake yin dariya sannan suka tafi.

Suna shiga gidan zasu dauki Aisha taga yanata zumudi ta rike shi tana rokonshi akan dan Allah karya fadawa anty dakyar ta samu ya yadda ko Abba bata so yaji harda kwallanta.

Aikam taga alamar anason cikin, baby yayi musabaha da babanshi har ya saba dashi, seda cikin yakai wata biyar yadda bazai boyu ba tazo gida gaishedasu Anty.

Anty ta kalleta tace "cikin nan watanshi nawa"? Safiyyah ta zare ido tana cewa "Ciki Anty? A ina"? Mugun kallo Anty tayi mata yasa ta saukar da kanta kasa ta wasa da wayarta Anty tace "wai yaushe zakiyi hankali? Harda Deenin kin maidashi wani iri ko" ta kasa cewa komai Anty tace "tashi kibar gidan nan" Safiyyah ta dago da sauri ta kalleta tana cewa " Anty dan Allah kiyi hakuri" tsaki Anty tayi tace "kinsan Allah sai kin bar gidan nan kijira sai randa kika San munada muhimmanci a gareku sannan ki dawo, ta mike tana hawaye ta dauki key din mota ta fito rikeda hannun Aisha, tana shirin shiga mota Abba yafito Daga bangaren hajiya, ya karaso kusa da ita ya kalleta yana cewa "lafiya dai Safiyyah ta goge hawayen idonta tana cewa "Anty ce" ya riko hannunta ba tareda yayi magana ba suka shiga gidan.

Tana daga zaune suka shigo ta harareta tana magana da fulatanci tace "meya dawo dake, ki koma inda kika fito tunda akanki aka fara yin ciki" Abba ya kalli Anty yace "ko zaginta kike da yaren ni bansaniba, amma kinsan dai yaro dole a bishi a hankali, meye ma dalilin fadan"? Anty tace "ciki ne da ita se akayi mana seya fito mugani bamukai afada mana ba" gaba daya Abba baiga abin fada acikin wannan lamarin ba yasan kunya takeji shiyasa bata fada ba ya kalleta yace "Safiyyah kibawa mamanki hakuri kuma karki sake yin haka kinji" ta gyada masa kai tana goge fuskarta da gefen mayafinta, sannan ta bawa Anty hakuri kamar yadda ya bukata, daganan shikam dama fita zaiyi ya kama gabansa itama safiyya ganin Anty na fushi zaman ba dadi yasaka tayi mata sallama ta wuce gida.

Kulawa da son duniya wannan cikin yana samu a kwana a tashi har cikin yakai lokacin haihuwa, taso ta dawo gida amma Deen ya hana dole ta zauna agida, watarana ta tashi da naquda tun safe suka je asibiti amma har dare shuru ta wahala iya wahala, ta cire rai daga rayuwa saboda azabar da takeji bata taba jin irinta ba, daga karshe ta sauka ta samu katuwar jaririyarta mai kama da ubanta sak, murna awurin su Halima ba a magana farin ciki ya lullubesu wannan ya Shafa wannan ya dauka haka aka ringa yawo da baby yayinda Safiyyah me kwance tana baccin gajiya.

Sai da ta sake kwana aka sallameta sun fito kenan zasu wuce wani wari ya tunkare sai ji sukayi ana kiran sunan safiyya koda suka tsaya magajiya ce tazo tana kuka tana rokonsu gafara "hakika na girbi abinda na shuka acikin mutanen Dana cuta kuna ciki ina Neman gafararku kafin Allah ya dauki raina, kunga ciwon daya sameni ki roka min gafarar mahaifiyarki ko zan samu sassauci" irin yadda zuciyarta ke tashi ya saka tayi saurin gyada kai tana cewa "mun yafe miki Allah ya yafe mana baki daya" daga haka tajuya Deeni kam tuni yayi nisa da babynsa a hannu Dan bayajin zai iya tsayawa kusada Inda take ma.

Suna Isa gida suka samu goggonsu ta iso daga jega, nan ta shirya tayiwa safiyya wankan azaba, inji safiyya saboda ruwan yayi masifar zafi sannan tana fitowa aka dura mata tuwo da kunu bugu da kari aka dungura mata baby ta shayar da ita, kunyar duniya ta isheta yadda take ta nuku-nuku kar aga jikinta.

Ranar suna yarinya taci suna  Fatima. Taro ya watse lafiya sai dai bayan haka Tsoho mahaifin Anty ya kama ciwo, ana gobe Safiyyah zatayi arbain Allah yayi masa cikawa. Anty tayi kuka harta gode Allah daga baya kuma ta dangana ta rungumi yan uwanta tunda itace babba.

Ana gama kwana uku Abba yace Safiyyah ta koma, bata samu tayi Dan tsarin nan ba haka aka maida ita, tana ta jin tsoron daukar wani cikin amma kuma tana basarwa.

Tana zaune tagama feeding din Fatima bayan sallar asuba ya shigo dakin yana kallonta ta janyo hijab din gefenta ta rufe jikinta tana cewa "kallon fa" yace "ba komai sonki ne yayimin yawa, na tabbar ke alkhairi ce a gareni, Safiyyah Allah yayi miki albarka, nagodewa Allah na gode miki Allah ya barmu tare ya raya mana Fatima" ta kalleshi tana cewa "duk Wanda yasoni a yadda nake to nikuma banida babban masoyin daya wuceshi, na tabbar da baka sona koda ni yar uwarka ce zaka gujeni amma kuma ka soni a haka, naji dadi kuma bazan taba daina yi maka Addua ba, bazan duba laifin da kayi na kika ba, kaddara ce tana kan kowa kuma Alhamdulillahi tunda ka gane gaskiya ka dawo kan hanya" ya rungumeta  yana jin wani sanyi na ratsa zuciyarshi.

Bangaren Anty ma komai sai hamdala lafiya lau take zama da Abba da kuma Hajiya kullum yana yi mata godiya da Sanya mata albarka itama kuma tana yi masa yadda yake mata, ba kowane namiji ne zaiyiwa wata ciki ya aureta ya rike abinda ta haifa ba harma yayi zama na amana da iya bugu da kari kuma yaringa tarairayarta yana nuna mata soyayya.

Bayan wasu shekaru na leka gidan  Deen da driver da yara su hudu maza biyu mata biyu babbar itace Aishan Halima sai Fatima da kannenta usman da Aliyu ta turasu mota tana cewa "Aisha kicewa Anty sati zakuyi, Fatima idan Anty tace Ku dawo kusaka ihu kunji" duk suka amsa da to ta koma cikin gida tana dariya Deen yace "ance miki tsofaffi basa soyayya ne tace " aisu basuda yara yanzu se subarmu muma muci kuruciyarmu.

Ya janyota yana murmushi ta zauna kan kafarsa nikuma nayo waje.



ALHAMDULILLAHI.
ANAN NAKAWO KARSHEN LITTAFIN RUBUTACCIYAR KADDARA, INA FATAN ZAKU BIYONI MASOYANA ACIKIN SABON LITTAFINA TANA KASA TANA DABO

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Jun 15, 2020 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

RUBUTACCIYAR K'ADDARAWhere stories live. Discover now