*RUBUTACCIYAR KADDARA*
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
( *home of expert and perfect writers)*💡
*SOPHIE GALADANCHI* ✍🏼
(3)
Dole ta dage wurin wannan sana'ar da ta zama madogara a garesu, so take ta takarta abinda ta tare suje kasuwa da Safiyyah ta siyo mata abubuwan da tafi bukata a matsayinta na wacce ta soma zama budurwa cikakkiya, amma ta wani gefen tana ganin rashin amfanin wannan sana'ar, har yanzu babu abunda ta tara sai bakar wahala da kwana cikin zulumi dare da rana, yanzu ma gashi wata fitinar na neman bullowa.
"Allah Kaine gatana, Allah kayimin sassauci" ta fada tana share hawayen da suka zubo daga idonta.
Shiri take da sauri-sauri tanaso kafin su iso ta samu dalilin fito da indo daga gida, tana shirin fitowa ta hango ta fitowarta kenan daga gida zata siyo musu ruwa, itama cikin sauri take tafiya saboda yunwa takeji gashi yau ta samu damar yi musu tuwo sun kwana biyu basuci tuwon ba, saboda yanzu Safiyyah tana tsayawa lesson a makaranta sai karfe biyar take dawowa daga ta shigo gida ta sauya uniform zuwa islamiyya koda zata dawo ana sallar magrib, yama hakance ta faru shiyasa ta fito da kanta ta siyo musu ruwa dama kuma bata so yarinyar tana fita bayan sallar magrib saboda yanayin unguwar.
Komawa magajiya tayi cikin gida ta tsaya daga gefen kofa tana hango indo , kiran wayar Wanda suka gama shirya kullinsu dashi tayi, yana dagawa tace "zaka iya matsowa kusa gatanan ta fito sai dai Kuyi a hankali unguwar nan akwai wuta kuma ga mutane suna yawo, zaku ganta da hijab kalar ruwan toka fara ce ba sosai ba kuma tanada tsagun fulani daga gefen bakinta, doguwa ce kuma bata da jiki" daga haka ta katse wayar taja gefe ta tsaya tana kallon yadda indo ke zuba sauri, tana kuma fatan samun sa'arta wannan karon.
Indo kuwa yau da take sauri saita ga nisan wurin kamar ya karu,fitilar mota ta haske mata ido sai tadan matsa gefe tana kare fuskarta da hannunta, a hankali motar ta wuce ta bata damu ba ta ci gaba da tafiya, sai ji tayi anyi wuf da ita kamar tayi baya-baya zata fadi amma sai taji ta a zaune, a firgice ta soma fadin " nnalillahi wa inna ilaihirraji'un", fadi take tana nanatawa, su uku ne mazan duk sun rufe fuskarsu da bakin kyalle babu Wanda ya kulata acikinsu ta kalli na kusa da ita tace, "Ku dubi girman Allah dan darajar Annabi da alqur'ani Ku tausaya min, wallahi banida komai banida kowa ni kadai ce sai yata guda d'aya, kuma marainiya ce".
Shuru babu Wanda ko yayi alamar yaji abinda take cewa, sai ta sake maimaitawa " wallahi marainiya, batasan kowa ba sai ni, bata da mai bata abinci dan Allah Kuyi hakuri Ku maidani gida" har lokacin babu wanda ya kulata, ta saki kuka mai cin rai, tafiyar Minti goma ta kaisu wannan tsararren gidan, ganin an bude musu gate sun shiga ya kara tayar Mata da hankali, ta kara sautin kukanta.
A kafada wani daga cikinsu ya dorata ya shigarda ita gidan, kai tsaye dakin dake hannun dama ya wuce da ita yana zuwa ya bude kofar ya ajiyeta tsakiyar dakin, babu wuta duhu ne sai ji tayi an rufe kofar hadi da murda key alamar dai an garkameta.
Kuka take yi har muryarta ta dashe, ba tunanin halinda take ciki take ba tunanin halinda Safiyyah take ciki shine ya addabi zuciyarta, ko tana can tana nemanta ko kuma tana jiran ta dawo daga siyan ruwan ne.
Safiyyah kuwa har Saida ta gaji da jiran Antyn ta ta fara cin tuwon saboda yunwa rabonta da abinci tun safe da tayi breakfast a makaranta, koda aka tashi taje siyan awara aljihun wandonta Ashe ya zare daga ciki kudin sun fadi, cin abincin take a hankali tayi loma biyar sai a ta shida wani tunanin yazo kanta da sauri ta mike ta zari hijabinta ta fita, tsayawa tayi ta kalli gabanta, gefenta na dama da hagu, bata hango wata mace mai kamada mamanta ba, da sauri ta shiga gidansu magajiya, ta same su a zazzaune tsakar gida kowa na harkar gabansa.
A wulakance wata daga cikinsu ta kalleta tace "lafiya dai".
Muryarta na rawa alamar kuka yana daf da zuwa tace " Anty nake nema ko ta shigo nan?".
"Dalla fita can ki nemi uwar taki bata nan munafuka kawai".
Da sauri ta juya ta fita tana kuka, shagon da suke siyan ruwan ta nufa tana tambayarshi ko ummanta tazo shagon yace " a'a bata zo ba gaskiya".
Hannu ta Dora akai ta kara sakin kuka tana cewa "na shiga uku".
Har titi Saida ta kai amma bataga alamar indo ba, ta dawo gida ta zauna bakin kofa tana kuka mai taba zuciya cikin kukan take magana kamar wata zautacciya " Anty ina kika shiga, daga sunan siyan ruwa sai ki bata? Idan kin tafi kin barni dawa zan zauna, dan Allah Anty ki dawo bazan iya rayuwa idan babu ke ba, ke kadai na sani" ta ci gaba da kuka tana kallon tabarmar da suka zauna da kwanon tuwon dake kai.
Bangaren indo kuwa tayi kukan da bata taba yin irinsa ba, takai awa daya zaune a kasan tiles taji alamar taba kofar, zubawa kofar ido tayi dukda bata ganin ko tafin hannunta, bude kofar yayi ya shigo, as usual da waya a hannunsa yana dannawa, ya maida kofar ya rufe, hasken wayar yayi kasa sosai saboda haka ba sosai take ganin fuskarshi ba, a hankali ya iso kusa da ita ya bita kasan ya zauna bayan ya saka wayarsa key ya ajiyeta kan gado.
Mikewa tsaye tayi tana nanata Kalmar shahada ta gano abinda yake nufi sai yanzu ta gano dalilin daukota, ZINA! Zuciyarta ta ambata jikinta ya dauki rawa sannan ta fara magana cikin kuka "dan Allah ka tausaya min, kada ka zama silar rugujewar rayuwata, shin anya kana tunanin wannan zata fishsheka? , bansan ka ba, banyi maka komai ba, da girmana bazan lallata rayuwata ba dan Allah ka barni na koma gida, banida komai da kake bukata ni talaka ce banida komai banida kowa".
Karamin tsaki yayi sannan ya dafe kansa a hankali kamar da kansa kadai yake magana yace " sai da na fada mata Bana son kuka".
Mikewa kawai yayi yana daukar wayar sa dake ringing ya kama hanyar fita, A hankali ta soma magana, ganin kamar jikinsa yayi sanyi tace " baka dace da wannan muguwar dabi'ar ba da Allah yai hani da ita, wannan kazamiyar rayuwa ce, kuma a zahiri kai mai tsafta ne, idan har kayimin alfarmar kare mutunci na nikuma nayi maka alkawarin yi maka adduar shiriya akoda yaushe, Allah ya shirye ya rabaka da shaidan".
Yanajin tayi shuru ya bude kofa ya fita har kasan zuciyarsa ya amsa da ameen amma iya labbansa ya tsaya, dakinsa ya shige ya fada kan gado yana kuka kamar wani karamin yaro, kuka ya zame masa tamkar abinci da abinsha.
Ganin kofar a bude yasa ta fito da sauri duk da duhu sai dan haske kadan dake lekowa ta window tana Fita waje ta samu Samuel a tsaye yace "Hajiya kizo a maida ke". Sai da tadan yi tunani kadan sannan ta juya ta shiga motar.
Karo tayi da Safiyyah bakin kofa da sauri Safiyyah ta tashi tsayuwar ta rungume uwarta tana kuka tana cewa " Anty kin bani tsoro, nayi ta yawon nemanki amma banganki ba".
Hawayen ya zubo daga idonta itama tace "kiyi hakuri bazan kara yi miki haka ba wani uzurin ne ya tasa Dana fita amma kiyi hakuri zo muje kici abincin".
Dakyar da lallashi tasamu Safiyyah tayi bacci ita kuma ai bacci bai ganta ba a zaune ta kwana tana tunani.
Magajiya ce a tsaye sai faman jera tsaki take tana cizon yatsa, taso wannan Abu ya faru dan ba karamin samu zasuyi ba, bata kuma yi tunanin saboda indo taki Deen zai maida ita ba ganin shi ya ganta da idonsa.
Ajiyar zuciya ta sauke tana murmushi a hankali tace " Aisha indo! Idan kin San wata bakisan wata ba wallahi".
Waya ta dauko ganin sha biyu tayi na rana ta danna kiran Deen, saida ta katse sannan yakirata.
" nace idan babu damuwa akwai wata yarinya, y'ace a wurin wacce nakai maka jiya Kuma babu inda diyar ta baro uwar, suna masifar kama har tafiyarsu iri daya, nasan za kayi murna domin yarinyar budurwa ce zabuwa hul a Leda kai zaka fara shan romonta bayan haka kuma ina da tabbacin duk yadda kake cewa baka son wacce aka taba kai maka to wannan yarinyar sai ka dawo mata".
Saida yaja iska da bakinsa sannan yace "ina fatan zantukan ki duka su kasance gaskiya wannan itace dama ta karshe".
Saida ta danyi shuru sannan tace " to amma ina bukatar dan lokaci domin su saki jikinsu naga alamar kamar akwai sauran tsoro a tare dasu".
"Yadda kike so" haka kawai yace ya kashe wayarsa, ya shiga yin aikin dake gabansa yana faman Jan iska ta baki lokaci zuwa lokaci".
Murmushin nannna mugunta tayi tana kallon wayar dake hannunta "yau jumu'a ken..."
*Safiyyah Galadanchi ke muku fatan Alkhairi*
YOU ARE READING
RUBUTACCIYAR K'ADDARA
FanfictionLABARIN UWA DA Y'AR TA WANDA YAKE CIKE DA TAUSAYI DA AL'AJABI, KUYI KUTSE A CIKI DOMIN GANIN ABINDA YAKE FARUWA.
