*RUBUTACCIYAR KADDARA**HASKE WRITERS ASSOCIATION*
( *home of expert and perfect writers)*💡*SOPHIE GALADANCHI* ✍🏼
29
Bai fahimci abinda magajiya take nufi ba sai ya tsaya yana kallonta yayinda zuciyar Safiyyah ta shiga tsalle kamar zata faso kirjinta, dan matsawa baya tayi Tana ci gaba da kallon yadda wadda aka kira da lubabatu ke kokarin mikawa Deeni yaron hannunta, shikuma yana ja da baya yace "wannan wace irin hauka ce? Ku gaggauta barin gidan nan kafin na saka a wulakanta ku" dogon tsaki lubabatu taja tana cewa "zamu bar gidan amma ba zamu daga da koda taku daya ne da wannan yaron ba, ga danka nan ka rike ko ka yar nagama nawa rainon".
Baba mai gadi ya shiga bangaren Anty da sauri kafin a kira masa Anty duk ya kagu, bai tsaya gaisheta ba yace "da matsala awaje, wasu ne suka zo mata suna ta yi mana hayaniya" Anty ta runtse idonta sosai Dan gaba days ji take bata son yin magana da kowa.
Fita tayi bayan ta saka mayafi, tsayawa tayi kallon matan dake faman tada jijiyoyin wuya, abinda suke fada ne ya kara tayar mata da hankali ba ganin magajiya ba.
"Baka Isa ba, kace ba danka bane, bayan duk yan Matan daka gama lalacewa dasu, nice nake kaimaka kuma lubabatu tana daga cikinsu, daga kanka bata sake kula kowane namiji ba, yarinyar dake gabanta shaida ce ita da uwarta, dalilin daya sanya ka kawo su gidanka kenan, haba Deen duk abinda akayi maka kai kaja, ban fada maka ranar na nan zuwa ba? Kai mai wayo ko? Ka hade uwa da ya kana Mora" zuwan Anty gurin yasa magajiya yin saurin zuwa kusa da ita tana cewa "ga wata shaida na samu Deeni mahaifiyar Safiyyah indo gatanan, tana cikin Matan Dana kai maka, daga baya kuka hada kai kuka zalunce ni"
Da sauri Anty ta daga kai ta kalli Deen yana danna waya, kokarin kiran Abba yake yanaso ya turo masa lambar commissioner of police, a take kwakwalwarta ta haska mata tsayuwarsa kofar dakin da aka kaita ranar yana danna waya, ta zaro ido tana Nuna shi bakinta yana rawa ta kasa furta koda kalma daya.
Shigowa gidan Abba yayi zai dauki Abu Dan motarsa ma a waje ya barta.
Zuwa yayi kusa dasu ya soma tambayar lafiya, magajiya ta kalleshi tana cewa "yawwa dattijo gara da kazo, nice magajiyar gidan karuwan dake gangare, wannan matar shekara da shekaru muna tare" ta fada tana Nuna indo sannan taci gaba da cewa "to wannan bawan Allah dama ni ina hadashi da mata sai ranar yaga wannan matar yace yana so in kai masa, na hada shi da ita kuma na hada shi da yarta daganan ban sake jin labarinsu ba, gashi yasa na dauki wasu maza aiki ba a biyasu ba yadaina daukar wayata karshe seda na siyar da filina na biya su, ya hada uwar da diyar yana mora, ina zaune saiga wannan baiwar Allah lubabatu marainiya ce na taba kai masa ita tazo ta kawo min kukanta da yaro Ashe tun lokacin ya kunsa mata ciki, gashi ta haife yaro abinda zasuci yana musu wahala shine na kawo ta yanzu Dan nayi bincike na gano nanne gidansu, daga zuwana naga yarinyar nan a taredashi daga baya saiga uwarta, ranka ya dade indo da kake gani ba karamar karuwa bace, ta saba da maza kuma naga alamar ciki ajikinta Dan haka kasancewarka babban mutum a garin nan yakamata kayi bincike kafin ka aminta dashi"Anty ta kalleshi tana son ganin yanayinsa, ko zai kareta amma sai ganin tayi idonsa sunyi ja sosai, ya kalli magajiya yace "yanzu kuyi hakuri Ku tafi gobe da safe sai Ku dawo" murmushin mugunta magajiya tayi ta kalli lubabatu tana cewa "dauko bawan Allahn nan mutafi gashinan duk hakori ya karar dashi".
Batareda tayi magana ba ta dauki yaron suka fita.
Anty ta kalli Abba tana cewa "da bakinka kake cewa wannan muguwar matar ta dawo gobe? Ka yadda da abinda ta fada ne ko me"? Ya sauke ajiyar zuciya yana cewa " ba a gane irin wannan gaskiyar sai anyi bincike" ya fada yana mata wani irin kallo, batayi magana ba kawai ta koma cikin gida, Jakarta kawai ta dauka ta fito, Safiyyah dake tsaye a wurin tana kuka sosai ta biyo bayan ta tana kiran sunanta cike da hasala ta juyo ta kalleta tace "ki tsaya nan, a wurina nan ne gidan ubanki, idan ya tabbatar miki da bai yadda dake ba sai kiyi yadda kika ga dama" ta bude kofar gate din gidan da sauri zata fita Abba dake tsaye gefe yace "Aisha kin san Allah ki koma cikin gida, idan kika sa kafarki kika fita ba tare da yadda ta ba ban yafe ba" yasan zata fita ta bar masa gidan shiyasa ya dawo waje ya tsaya, ba saboda ita yakeso yayi bincike ba, yasan Deeni da dabiar bin mata kafin wannan lokacin shiyasa yakeso yayi bincike bayaso ya tauyewa waccen matar hakkinta.
Tunda suka gama dramarsu suka fita Deeni yake tsaye wurin, ya rasa kasa yake ko sama, tashin hankalin da bai taba tunani ba, Allah ya gani yayi tuba irin tuban da bazai taba komawa irin wannan sabon Allah ba, shiyasa yake so yayi aure Dan ya kare mutuncinsa amma yanzu magajiya ta rusa komai.
Kawayen Safiyyah sallama suka yi mata suka bar gidan da kananun maganganu a bakinsu irinna mata.
A bakin kofar suka tsaya Anty tana bakin cikin hanata tafiyar da yayi, ita kuma Safiyyah tana kukan abinda ya faru, Abba yazo ya nunawa Safiyyah kofar shiga gida ta juya tana tafiya kamar kazar da kwai ya fashewa aciki, tana tafiya ta hadu da Halima tana murza ido, duk abinda ya faru bata sani ba bacci takeyi, dakinsu direct Safiyyah ta wuce, babu abinda yafi kona mata rai irin yadda Deen ya kasa raba Kansa da Zina, haba! Zina a wurin son rai ne, baka nemi mata ka rasa ba komai Kanada shi amma ya tsaya bata rayuwar yayan mutane.
Sai da Abba yayiwa Anty Jan ido ta dawo cikin gida da matsanancin ciwon kai, momy ce tayi ta bata magana har ta Dan saki ranta tana jiran gobe tayi ayita ta takare.
Hajiya duk abinda ya faru a kan idonta amma bata yi kokarin shiga sabgar ba, abin dadi ma ya mata, wato Abba shi mai mata, ita dai addua take Allah yasa bai debo musu cutar zamani ba tunda ashe ma karuwa ya auro.
Daga gidan bai tsaya ko ina ba sai gidan abubakar koda yaje baya nan, sai yayi zamansa a mota, gaba daya rayuwarsa baya jin dadinta, bai taba tunanin fuskantar irin wannan ranar ba.
Duk irin lallashin da Halima tayiwa Safiyyah bata ji ba har Halima ta soma jin haushinta ta fara yi mata fada tana cewa " ke wai bakijin lallashi ne sai kace Baki San halin Yaya ba tun farko, inhar kina sonshi ki masa addua mana"
Cikin kuka Safiyyah tace "kin kuwa San yadda nake ji? Ni ba a haifeni ta hanyar aure ba, Wanda zai rufamin asiri ya aureni mazinaci sannan ana sheganta Dan dake cikin Anty tun kafin yazo duniya, haba! Kukan nan shi kadai ne mafita a gareni, magajiya ta cucemu mun dade muna shan wahalarta, dole nayi kuka Yaya halima" tausayinta ya kama halima ta rungumeta kawai tana bubbuga bayanta, jikinta har ya soma yin zafi fuskarta ta kumbura sosai.
_SAFIYYAH GALADANCHI KE MUKU FATAN ALKHAIRI*
YOU ARE READING
RUBUTACCIYAR K'ADDARA
FanfictionLABARIN UWA DA Y'AR TA WANDA YAKE CIKE DA TAUSAYI DA AL'AJABI, KUYI KUTSE A CIKI DOMIN GANIN ABINDA YAKE FARUWA.