*RUBUTACCIYAR KADDARA*
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
( *home of expert and perfect writers)*💡*SOPHIE GALADANCHI* ✍🏼
30
Halima taso ta kwana gidan saboda Safiyyah, amma tasan Muhammad hauka ma take yi tace zata kwana saboda bazai yadda ba, jikinta yayi sanyi, bata san abinda zai faruba gobe, duk iya kokarinta wurin lallashin safiyya ta kasa hanata kukan, babu yadda ta iya dole ta baro ta tana kukan.
Bangaren Deen kuwa dakyar yaja kafarsa ya shiga mota ya tafi amma ya kasa Isa gida, zama yayi cikin motar gefen hanya yana jin kunyar kansa, haka tabon zina yake? Ya tuba irin tuban da Allah yake so amma gashi laifin na bibiyarshi, yana jin kunyar kowa na gidan ma, tun farko me ya kaishi? Kamar wani Mara hankali saboda kaddara wadda take rubutacciya ta afkawa kanwarsa bai Isa ya zama dalilin da zai dulmiyar dashi cikin karuwanci ba.
Kansa yana ciwo ya wuce gida. Malam buba na gaidashi bai damu daya amsa ba ya shiga gida.
Kowa haka yayi bacci agidan cikin bacin rai har gari ya waye, amarya fuskarta duk tayi wani irin, event dinda zasuyi ranar ma ji tayi ya fita ranta, "to wama ya sani ko an fasa auren tunda mijin bazai iya hakuri a kaita ba seyabi yayan mutane da laluba" ta fada tana dauko kaya daga wardrobe.
Abbah tunda sassafe yayi tsinke police station y'an sanda biyu ya dauka daga nan suka wuce unguwarsu magajiya, tun bayan barinta gidan yasa aka bi bayanta, bai yadda da haka kawai tazo ta tarwatsa masa gida ba ta kunyata shi a idon duniya dole sai ya bibiyeta.
Magajiya tana zaune ta jiyo sallama, tana murna tasan customers ne sai sukayi mata bayanin kansu, ta kuma shaida Abba, tun a wurin cikinta ya duri ruwa amma ta dake, saida suka sakata gaba taje ta nuna gidan lubabatu, zuciyarta ta shiga bugawa, waya sani ko ta mayar da yaron wurin uwarsa? Ganin babu wasa a taredasu yasa ta nuna gidansu, koda sukaje lubabatu na zaune ta Cancada kwalliya zata talla kasuwa da bokitin alalanta da awara, tana ganinsu ta mike da sauri tana zare ido.
Da ido magajiya tayi mata alamar karta bada su, ta bude baki tace "ki dauko yaro mana amaidashi gidan ubansa kin tsaya raba ido" sai da ta dan daburce sannan tace "yana gidan iya hari bari na karbo shi" dan sandan ya daka mata tsawa yace "karku maida mu mahaukata ki wuce muje station" gaba tayi da sauri tana waigen awaranta, bata taba yin case da yan sanda ba lallai yau ta debo ruwan dafa kanta.
Suna zuwa police station Abba dama ya musu bayani yayi tafiyarshi, koda ya koma gida part din Anty ya shiga ya samu su mommy a Palo ya zauna suka gaisa sannan suka shiga zancen abinda ya faru Abba yace.
"Yaron nan babu yadda banyi ba ya dawo nan yaki, ni yanzu mataki daya Na dauka, tunda abinda ya zabawa rayuwarsa kenan to lallai sedai ya zauna nan tare damu, wancen gidan saidai a sayar dashi kokuma yajira har lokacin da yayi hankali sannan ya dauki iyalinshi ya koma can" Momy ta gyara zamanta tana cewa "to Allah yasa ya daina hakan kuma ya zama alkhairi, nima nemanshi nake in masa fada kuma ko jiya danayi magana dasu Hajiya larai sunyi complain akan Deen tun randa abin nan ya faru ya dauke kafa kuma ba'a haka jira nake hankali ya kwanta kafin mu wuce Kaduna sai Na ci masa mutunci" Abba ya sauke numfashi yana cewa "ni bansan da haka ba saboda abubuwa da sukayi yawa Nima nan badan yaga Safiyyah ba da Bana ganinshi sai bayan sati ko fiye, Allah dai ya shiryar mana dasu" ta amsa da ameen.
Abba bai yiwa kowa zancen magajiya ba Anty ma bata nemeshi ba duk da tajiyo muryarsa daya shiga bangarenta. Ita takanta takeyi shiyasa Dan yau ko yawun bakinta bata son hadiyewa.
Safiyyah ma a daki ta wuni Dan ko yan bikin bata son gani, gaba daya auren ya fita ranta.
Washe gari Abba shirinsa yayi Na zuwa daurin aure, sannan ya daga wayarsa ya kira deen bai dauka ba sai ya kira abubakar yaji idan suna tare amma sai yace rabonsa dashi tun jiya da safe.
Abubakar da shima ya gama shirinsa bayan gama waya da Abba sai ya wuce kai tsaye gidan Deen, abin mamaki ya sameshi yana zaune Babu alamar shiri atare dashi.
"Wane irin Abu be wannan? Zuwa yanzu ya kamata ace duk wani shiri ja gama yinshi Dan Allah karka bata min rai, Abba yakiraka kaki dagawa akan wane dalili?" Tsaki Deen yayi yace "da wanne kakeso naji, kana tunanin safiyyah da Anty zasu yadda da wannan auren bayan Sharrin da magajiya tagama yimin? Na yadda khaidin mata yafi Na shedan abubakar, karara nake hango tsanata a idon Safiyyah, meya kamata nayi ban saniba, ta rusa duk shirin Dana gama yi Allah shine shaidata akan tuban danayi kuma shine shaidata akan irin soyayyar Danakewa Safiyyah amma cikin lokaci kalilan makirar mace ta rusa min komai" abubakar ya dafa kafadarshi yace "hakuri zakayi, Safiyyah kanwarka ce kuma matarka insha Allahu, ka godewa Allah da kunyar tun anan duniya ne kajita ba sai a gaban Allah ba, yau ranar murna ce awurinka Dan haka ka tashi shirya mu tafi lokaci na tafiya" yana dafe da kansa tsawon mintuna goma sannan ya shiga toilet.
Shikansa yasan yayi matukar kyau cikin farar shadda, lallai zai nuna godiyarsa ga mahalicci sannan zai nunawa Safiyyah godiya ta musamman.
Acikin kyakkyawar motarsa suka je,mutane sun hallara shi kadai ake jira, babu dadewa aka daura auren, yana zaune ya sauke ajiyar zuciya ya runtse idonsa.
Daga wurin daurin auren gida suka dawo dama a masallaci aka daura, koda suka ido angyara cikin gidan da table da kujeru hard a canopies, wannan shiri da akayi shi ya tayarwa Safiyyah da hankali, a tunaninta an fasa auren ne, sai taga sabanin haka, tana zaune da kayan da bai kamata amarya ta zauna da irinsu ba. Kuka tasa a dakin Halima ta zauna kallonta.
Dakyar ta tursasata ta sauya kaya dan saida ta nuna mata bacin ranta sosai, babu dadewa dayin haka Deen ya iso da abokanshi cikin gidan, Momy ta shiga dakinta tace "Halima jeki rakata suyi hoto da angon ko Dan tarihi" Halima ta amsa da to ita ko hawaye take kokarin rikewa saboda haushin deen da take ji kunshe cikin zuciyarta.
_Kuyi hakuri kunsan duniyar ta rikice kwana biyu banyiba, yau danayi niyya ciwon kai ya hana nayi dayawa_

YOU ARE READING
RUBUTACCIYAR K'ADDARA
FanfictionLABARIN UWA DA Y'AR TA WANDA YAKE CIKE DA TAUSAYI DA AL'AJABI, KUYI KUTSE A CIKI DOMIN GANIN ABINDA YAKE FARUWA.