BABI NA BAKWAI

829 63 2
                                    

*RUBUTACCIYAR KADDARA*

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
( *home of expert and perfect writers)*💡

*SOPHIE GALADANCHI* ✍🏼

_Assalamu alaikum, ina mik'a sakon gaisuwa da godiya ga masoyana masu karanta wannan novel ina kuka rokonku akan duk wanda yake son novel dinnan daga farko ya nema tun yanzu, banida tabbacin zan kula idan anyi min magana PC saboda yawan sakonni ko kuma a groups, nasan da yawa daga cikin masu karatu sunfi so sai anyi nisa a novel ko kuma an kammala sannan su fara nema dan su karanta to ina Baku shawarar akan tun yanzu da yake farko Ku fara Tarawa kuna ajiyewa dan karkuyi nema ba a kulaku ba kuga kamar anyi wulakanci, nagode._

(7)

Komai nasu sai da ta had'a wanda zai dauku sannan ta yi shirin zuwa gidansu huraira.

Cikin ikon Allah ta gane gidan, sai tayi tsaye tana kallon gidan tana tunani kamar tasan gidan, a zuciyarta tace "gidajen nan dama na masu kudi sai ka ringa ganin kamar duk iri daya ne" Numfashi ta sauke sannan ta shiga bubbuga gate din gidan Malam buba yana zaune yajiyo ana kwankwasa ya taso da sauri ya bude, kallo daya yayi mata ya gane maman safiyyah ce saboda kamar da suke, matsawa yayi ya bata hanya yana cewa "bisimillah ki shiga mana".

Shiga tayi sannan ta juyo suka gaisa tace " da tambaya zanyi ince ko nan ne gidan huraira maman fadimatu?" Sai da ya Washe bakinsa dake cike da goro sannan yace "Nan ne ai ina ganin ki na gane ki, ko ba maman safiyyah bace?" Murmushi kawai tayi sannan ya mata jagora zuwa cikin gidan.

Safiyyah da fadimatu na zaune sunyi shuru kamar masu zaman makoki saboda rashin sabo sai kuma akayi Sa'a dukansu ba masu surutu bane.

Sallar da suka yi ne yasa safiyyah dagowa bayan ta amsa, cike da murna taje ta rungume indo tana kukan murna, raba jikinsu indo tayi ta tsaya tana kallon yadda safiyyah ta rame, itama din kallonta take yadda duk tayi kamar wata mai ciwo.

Huraira tace "Safiyyah kya bari ai maman taki ta zauna ko" murmushi tayi ta nufi tabarmar da suke zaune tana rike da hannun Indo.

Zama sukayi suka gaisa cike da mutunci aka kawo mata abinci da ruwa, kamar ko sunsan yunwa take ji sai dai kadan taci, ta kalli safiyyah tace " Safiyyah lokaci yayi da zamu bar wannan gidan, idan sun aikata wannan mummunar abun agare mu mun samu Allah ya kwace mu watarana zasu iya yin fiye da haka duk da bamu cire rai daga rahamar Allah ba da kariyar sa amma yakamata mu tashi tsaye"

Safiyyah ta kalleta muryarta na rawa tace "to Anty ina zamu koma?"

Indo tayi kasa da murya tace "shine abinda nake tunani safiyyah, na duba ko dubu goma banida su, bansan kowa ba balle na ranto kudi sannan kuma idan ma Na ranto kudi ko aikin kwasar kaya ba karamin Abu bane sannan banida wata Sana'a kuma".

Kuka safiyya ta fashe dashi tana ganin tonuwar asirinsu, tambayoyi ne kunshe a bakinta amma tana tsoron furtasu, saboda ta gwada sau biyu amma dukansu basu sha da dadi ba, dan haka tayi shuru tana kallon Indo.

Indo ta goge hawayen idonta sannan tace " kiyi hakuri safiyyah nasan me kike tunani, yanzu ina tunanin komawa gida ne, can kadai ne nake tunanin munada mafaka, sai dai ina jin kunyar rokon baban Fadimatu akan ki zauna anan Kafin naje gidan na dawo"

Safiyyah ta sa bayan hannunta tana goge hawayen da suka sake zubowa daga idonta sannan tace "to Anty kije dani mana" .

Zaro ido Indo tayi tace "ba zai yuwu ba safiyya sai dai har ni na fasa zuwan amma babu halin zuwa dake tunda kinga na Dade banje ba, shiga ki kiramin maman fadimatu" mike safiyyah tayi jikinta a sanyaye, tana tunanin dalilin dayasa Anty bata son zuwa da ita gida.

Dakin ta shiga da sallama ta fadawa maman fadimatu kiran da indo ke mata, tare suka fito huraira tana dariya tace "maman safiyyah badai tafiya zaki yi ba tun yanzu?"

Safiya itama dariyar tayi tace "ina hanya dai isha Allahu, sai dai wata alfarma da nake so na sake nema a wurin Ku karo na biyu" zama maman fadimatu tayi tana kallon indo tace "Allah yasa bai fi karfinmu ba".

" matsala ce ta kowane gefe maman fadimatu, gidan nan bamuda hakki dashi, Wacce muke zaune a karkashinta gidan ta ne kuma ta mutu ta barmu, koda babu matsalar barazana da ake mana da rayuwarmu dole ne watarana zamu bar musu gidansu, ba sai na miki dalla-dalla ba kinsan yadda gidan yake, to shawarar dai ita Barin gidan yafi zama kwanciyar hankali a garemu sai dai ba anan gizo yake saka ba, ni ba yar nan garin bace, nan din Dana zauna bana hulda da kowa inba margayiya ba sai mutanenta, nayi tunanin kama haya amma banida wannan zarafin saboda ko nan gidan da nake sana'ar wanki da guga nakeyi, shine na yanke shawarar zan je gida in dawo kuma bazan tafi da Safiyyah ba saboda wani dalili, alfarmar anan shine Ku dubi girman Allah zan sake Barin Safiya anan kafin naje idan na daidaita komai zan dawo".

Shuru maman fadimatu tayi sannan tace "to maman safiyyah bari inje In fadawa baban fadimatu sai in ji ta bakinsa".

Murmushi indo tayi gabanta na faduwa, tanajin tsoro kada suki aminta, da kuwa ta shiga uku.

Malam Buba ya jinjina lamarin yayi shuru yana ci gaba da sauraren huraira tana cewa " Ni tsorona ma naga daga gidan karuwai fa suke kar mu kwashi wata cutar" kallon da ya mata ne yasa tasha jinin jikinta tayi shuru yace "ki fada mata Na amince Allah ya dawo da ita lafiya, kina magana kamar bake kike cewa a taimaki yarinyar nan ba, to ki dauki kanki ki dara a mizanin da suke yanzu idan kece ya zakiji?"

Ajiyar zuciya ta sauke tace "Allah ya dawo da ita lafiya"
Ya amsa da ameen yana kara radio a kunnensa, juyawa huraira tayi ta koma cikin gidan yabi bayan ta da kallo yana kissima abubuwa da yawa aransa.

Jin sun amince ya sa Indo yin murna sosai tayita jera musu godiya, acikin kudinta ta Ciro dubu daya ta basu tace su kara dakyar huraira ta amsa sannan sukayi sallama, bayan ta fada musu zata dawo kafin ta wuce, ta kalli safiyyah tace "to sai na dawo kinji kuma dan Allah ki kama kanki" gyada kai safiyyah tayi dan bata son yin magana kukan da take rikewa ya fito.

Tana fitowa malam Buba ya mike yana cewa "ai naji sakonki nace kinfi haka a wurinmu ai, fatan mu dai Allah ya kara karewa ya kuma dawo dake lafiya, sai yaushe ne tafiyar ma?"

"Ban saka rana ba tukunna sai na shirya, yanzu dai zan tafi can gidan insha Allahu zan dawo".

" to Allah ya kaimu sai kin dawo".

Ya fada yana bude mata kofa ta fita yabita da kallo.

Bangaren Deen kuwa har mamakin sauyawarsa yake saboda bashida lokacin zama gidan ma sannan baya bukatar ganin lambar magajiya ma awayarsa kwata-kwata baya jin wani Abu da yayi kamada son mace a kusa dashi kamar yadda yake ji a da.


*Safiyyah Galadanchi ke muku fatan Alkhairi*

RUBUTACCIYAR K'ADDARAWhere stories live. Discover now