*RUBUTACCIYAR KADDARA**HASKE WRITERS ASSOCIATION*
( *home of expert and perfect writers)*💡*SOPHIE GALADANCHI* ✍🏼
(18)
Washe gari da safe inna ta lallaba Safiyyah akan ta yadda ta koma gida, suma din ba dadewa zasu yi ba, danne kukan dake zuwa mata tayi sannan ta amsa mata amma tana tunanin yadda zatayi rayuwa a kauyen batare da anty ba.
Baffa gidado daya zo shine ya koma da Safiyyah, bayan sun isa yace ta debo kayanta tabi hafsatu can gidan haulatu, sai a lokacin taji sanyi dama tana tunanin yadda zata rayu da yan gefen Baffa salihun nan.
Taji dadin zama a gidan dan mijin haula baida matsala, ita kanta haulatun tana janta ajiki danta lura batada sakewa kamar bata saba shiga mutane ba.Satinsu daya aka sallamesu, hannun nata da sauki sai dai taci gaba da shan magani.
"Haba mukhtar! Kana hauka ne? Abinda na shafe shekara da shekaru ina nema? Zaka gani baka gaya min ba sai yanzu da ake zancen sati biyu" ya fada yana buga teburin dake gabansa.
"Calm down mana ranka ya dade, wadda nace maka na gani fa bazai yuwu ace indo bace, she's very young indo ta girma yanzu ko yayane zamu ga ta zama babbar mace, wancen lokacin fa karka manta karamar yarinya ce ko kai yanzu ka kara girma da shekaru akan da can".
Mukhtar din ya fada yana kallon mutumin da suke magana dashi.Mikewa yayi yana cewa "banga zama ba shima bai ganni ba, asibitin nan dole zaka kaini, inaji wannan daka gani itace ajiyata Dana bawa indo bazan taba samun kwanciyar hankali ba sai randa na gansu, sune farin ciki na" murmushi mukhtar yayi yabi bayansa suka tafi asibitin, sai dai sun samu an sallamesu tun kwana shida da suka wuce, shi kansa mukhtar din baiyi tunanin an sallamesu ba, dan yaso suyi sallama ya sake basu hakuri akan abinda ya faru.
Bayan fitowarsu Abdullahi bai wani bata lokaci ba ya kama hanyar kauyensu indo, har tsikar jikinsa yake ji tana tashi, yakai shekara uku rabon daya biyo hanyar nan, yanzu kuma da yazo bayan ya gama cire rai da samun abinda yake nema, sai yake jin yanada kwarin gwiwa wani gefe Na zuciyarsa na nashi tabbacin sake ganin indo da kuma farin cikinsa daya kwallafa rai akai.
Mukhtar kuwa kallonsa kawai yake yadda duk ya katse musu abubuwa masu muhimmanci ya kama hanyar kauyen nan, shi kanshi yanada abubuwan da zaiyi wani satin za'ayi auren yar shi, shi ake jira yaje ya bada kudin gadajenta aje a karbo.
Duk da shekara ukun da yayi bai zo ba hakan bai hanashi gano gidan su indo ba, lokacin daya tsaya kofar gidan sai yaji bugun zuciyarsa na karuwa, tsayawa sukayi kofar gidan sukayi sallama, Baffa salihu shi ya amsa ya fito yana dibarsu yana zubarwa, amma basu damu ba dan ba wannan ne karo na farko da suka samu tarba irin wannan daga gareshi ba.
Abdullahi ya riko hannun wani yaro dake wasa yace "dan Allah zo kashiga gidan nan kayi min sallama da Baffa Gidado, kafin yaron ya shiga cikin gidan Baffa gidado ya fito a lokacin kuwa har Baffa salihu ya Cika rigarsa da iska.
Baffa gidado ya kallesu cike da mamaki mikawa Abdullahi hannu yayi suka gaisa sannan ya kalli mukhtar yana cewa, " Allah sarki ai Aishatu ma taji sauki sosai hannun ma tana motsa shi Allah ya takaita mana wahala" mamaki ne ya kama mukhtar jin wai aishan ce ma ya kade, kenan wannan yarinyar itace yar da ta Haifa? Wata zuciayar tace kila dai kanwar ta ce, murmushi yayi yace "muna yiwa Allah godiya".
Abdullahi ya kalli Baffa Gidado yace "Baffa ashe Aisha ta dawo shine baka neme ni ba"? Baffa yayi murmushi yana cewa "Kayi hakuri Abdullahi banida layinka, bayan tafiyarka wancen lokacin wayata ta fadi a wurin kiwo ban sani ba, kuma tun daga lokacin ban sake rike waya ba" wani sanyi yaji yana ratsa zuciyarsa ya rike hannun Baffa sosai yana cewa "zan iya ganinta yanzu"? Shuru kadan Baffa yayi sannan yace "babu matsala Abdullahi bisimillah" ya fada yana shiga gidan, bayansa suka bi, a tsakar gida suka ja birki suka jira Baffa Gidado ya musu iso har cikin dakin sannan ya fito ya basu wuri, kallo daya indo tayi musu bata wani kalle su ba amma dai ta gano Wanda ya kadeta ne yazo, Abdullahi ya tsaya yana kallonta daga bakin kofar, Aisha bata girma, yarinyar dake gefenta ya kalla sai yaga kamar Aishan, sallama ya sake yi sai a lokacin ta dago ta kalleshi, wani irin faduwa gabanta yayi tayi saurin dauke idonta, yaushe zata manta da wannan fuskar? Idonta ta sauke kan Safiyyah dake dama mata fura, Safiyyah ta dago da murmushi a fuskarta sai taga Antynta na hawaye, da sauri ta ajiye kwaryar gefenta ta matsa kusa da ita tana cewa "sannu Anty, ko na kira Baffa asamo mota muje asibiti" girgiza mata kai indo tayi tana goge hawayen fuskarta.
Abdullahi ya zauna kusa da mukhtar yana kallon Aisha a hankali yace "Aisha dan Allah kiyi hakuri, nasan ganina ne yasaka ki kuka, amma yanzu kiyi shuru dai, ya hannun naki"? Kallon su Safiyyah tayi su duka sannan ta tsayar da kallonta kan Abdullahi, shikam hankalinsa yana kan indo yanaso ya tambayeta ko labarin cikin da tabar gida dashi, jingina bayan ta tayi da bangon dakin ta kalleshi sannan ta kalli Safiyyah, kamar ya gano yaren sai ya kalli Safiyyah yayi shuru, mukhtar kam tunda ya mata yajiki ya fita, Safiyyah ta sake kallonsu, ita dai bayan wancen daya kade anty bata san sunada alaka da wani a sokoto ba, kuma wannan mutumin san baiyi kamada mutanen kauyen nan ba, sai ta kalli Abdullahi ta gaidashi, ya amsa yana kallonta sosai, ganin kallon yayi yawa yasa ta sake matsawa kusa da indo a hankali tace " Anty waye wannan? Bansan shi ba" a hankali indo tace "Babanki ne" a tare Safiyyah da Abdullahi suka kalli juna, shi yaji wani irin farin ciki yayinda Safiyyah taji kamar anfada mata wani Abu Wanda yake Tayar da hankali.
Awa biyu kenan da zuwansa office ya kasa yin komai, tunanin Safiyyah ya tsaya masa a rai, ko ubanwa ma yace suje gida salla? Ajiyar zuciya ya sauke yace "duk ruwan da aka sheka jiya saida nayi wankan dare saboda yarinyar nan, hmm na tausaya mata ranar da duk muka yi karo" file din gaban sa ya bude sai kuma ya rufe yace "bari naje wurin wancen dan rainin hankalin" ya fada yana mikewa tsaye.
Abubakar saida yayi dariya sosai yace "kaifa wallahi mayen mata ne? Kajira ka gani zasu dawo bana ji sun tafi kenan" shuru Deen yayi yana adduar Allah yasa su dawo din.
Gidansu ya nufa sai ya samu kawayen Halima sunzo suna rabon sweet din engagement dinta da aka kawo, yaji dadin ganin yadda ta saki jikinta suna ta nishadi da kawayenta, zama yayi kan kujera ya dauki biscuit din purebliss na chocolate yana ci yace "yar gidan Abba ankusa samun abinda akeso ko" dariya sukayi su duka ya mike da biscuit din a hannunsa yana cewa "to auren dai ba yanzu ba sai bayan shekara biyu" dariya suka kuma yi yabarsu nan sunata tsokanarta.
Kallon indo yayi yace "Aisha da gaske ashe kin Haifa min abinda yake cikinki"? Gyada masa kanta kawai tayi dan nauyi bakinta ya mata, kusa da Safiyyah ya matsa ya riko hannunta sai kuma ya saki hannunta ya kalli gabas yayi sujjada yana yiwa Allah godiya, kota yaya yasamu wannan yarinyar dole zaiyiwa Allah godiya yasan ya tafka kuskure amma Allah mai jin rokon bayinsa ne, idan Aisha ta yafe masa sai ci gaba da rokon gafara daga wurin Allah har ya koma gareshi.
Ganin yadda Yake murna yabawa indo mamaki, Sam batayi tunanin zai karbi Safiyyah ba, kallon indo yayi yana cewa "Aisha in banyi gaggawa ba kibani ita na tafi da ita dan Allah, nayi alkawarin dawo da ita gobe" Safiyyah ta zaro ido waje sai kuma ta koma ta zauna tana cewa "ni bazan bika ba, ka tafi gobe ka dawo, anty batada lafiya idan na bika ba zan iya bacci ba" bai yi mamaki ba dan shima yasan yayi gajen hakuri, murmushi yayi yace "to zo muje muyi sirri"
Yadda yayi maganar yana dariya yasa tayi murmushi ta kalli indo, sanin darajar mahaifi yasa indo itama tayi murmushi tana cewa "ki tafi mana", yana rike da hannunta har suka je wurin mota.
_kuyi hakuri pls kwana biyu kunji shuru ai kunsan dalili amma zamu ci gaba daga nan insha Allahu nagode.
![](https://img.wattpad.com/cover/210952048-288-k453654.jpg)
YOU ARE READING
RUBUTACCIYAR K'ADDARA
FanficLABARIN UWA DA Y'AR TA WANDA YAKE CIKE DA TAUSAYI DA AL'AJABI, KUYI KUTSE A CIKI DOMIN GANIN ABINDA YAKE FARUWA.