1

4.4K 164 2
                                    

💥 *💥AUREN FA'RI....* 💥💥

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
*(home of expert and perfect writers)*💡

       *SLIMZY✍🏻*
_Wattpad@slimzy33_

*SADAUKARWA:*
*HAUWA'U MU'AZU AMIR RUMA...*

  _kamar yadda nayi alk'awari gareku masoyana masoya_ _littafaina bayan_ *IZZA TA* _zanzo muku da sabon labari a kyauta to Alhamdulillahi alk'awari_ _ya cika👌🏼_ *SLIMZY CE* ✍🏻

                  *1*

Fararen kujeru da d'an karamin centre table me kmr stool shine a gabansu a harabar gidan da laptop Me dan girma akan centre table din me kama da stool,gabaki daya fuskarsa babu walwala ko kadan babu alamar faraa,hira take zuba masa amma sam hankalinsa baya kanta be ma san tanayi ba hannuwansa kawai ke motsi wajen danna keys din laptop dinsa da alama,aiki yakeyi mai muhimmanci,...."sweet kasan ko ummah da naje gida cewa tayi wai nayi kyau abuna saidai nad'an rame kodai ciki gareni..."ta karasa maganar cike da nishadi ko kallonta beyi ba ya cigaba da abinda yakeyi,zuwa yanzun zuciyarta ta soma harzuka ta soma tafarfasa,wani kululun bakin ciki ne ya taso ya tokare mata wuya,kallon jikinta tayi suturar dake jikinta da yadda take zuba kamshi amma sammm beko bin ta kanta,har yaushene zata soma burgesa?har yaushene zata iya jan hankalin mijinta?..tsaki tayi cikin zuciyarta,nan da nan idonta ya canja kala ta hadiyi wani miyau da ya bushe a bakinta saboda bacin rai,niyyar mikewa tayi tabar wajen ta koma parlor tayi kallo amma bazata taba barin wajen ba saita amayar masa da abinda ke cikinta dikda indai irin wadanan maganganun ne sun saba....

  "Sweetttttt....wai nikam bakaji ina magana ina baka labari ba?ka shareni sai zuba nakeyi kamar an kwance kura?"a fusace tayi maganar.

Bece komi ba ya cigaba da typing dinsa,kara fusata tayi zatayi magana a karo na biyu,ganin bakinsa na motsi yasa ta dakata Tana dubansa cike da bacin rai,dakyar ya motsa labbabsa "inace magana kikeyi?...kuma kunne keji?umm?ai ina jinki"ya maida kai cikin ko in kula ya cigaba da typing dinsa.

"Ehh magana nakeyi,amma nikadai nakeyi ai sunan mijina yana gefe na ne amma sammm hankalinsa baya wajena yana can wani waje daban"ta d'an hararesa cike da kosawa,

Murmushin gefen fuska yayi "jiddah kenan....tou aidai kina ganin aiki nakeyi ko?kuma bazan bar aikina in tsaya sauraren shirmen labarinki ba,kuma dai ai kunne na yana sauraronki ko?inace dama kunne keji?"

Kara k'uluwa jiddah tayi ta mike tsaye ta rike kwankwaso cike da takaici,wai miji kakewa hira yana cewa kunne keji kamar wata sauna haka ya maidata,"nasan aiki kakeyi ai , Amma naga nan ba office bane kuma yau ai sunday ne ba ranar aiki ba ,ta yaya ina bukatar lokacinka kai baka da nawa?yai da ya zama sunday zamu kasance tare da juna kana manne da computer kamar wani bature?"dariya ma ta basa jiddah ta saba irin wadanan rigingimun ta kasa gane cewar bazai iya ajiye aikinsa ya tsaya shirmen banza ba,dole ne ya nemi abinda zai gina rayuwarsa da ta yaransa,sanan da aikinsa ta gansa amma kullum saita yab'a masa maganganu marasa dadi akan aikinsa ya kamata ace ta saba tunda dai tasan ai Yana sonta bawai baya sonta bane.....saida ya kwashi minti biyu tana tsaye tana jira ko zai ruko hannunta ya zaunar da ita alamar ban hakuri,amma shiru ta cire rai hakan yasa kwalla ta cicciko a idonta,dago kyawawan idanuwansa yayi ya saukesu akanta memakon yayi magana girgiza kai yayi hade da dan murmushi ya maida kansa ya cigaba da abinda yake.....juyawa tayi ta ruga sashensu hawaye na bin fuskarta a yuje tahau matakalar da zata sada ta da babbar kofar patlorn su ta bude kofar da karfi ta rufo ta....yana hangenta ya girgiza kai yana murmushi,jiddah rikici itadai a zauna ayi soyayya ayi hira shine muradinta.....ya kai hannu ya dauki lemo ya kurba ya ajiye cup din sanan ya maida kansa ya cigaba da abinda yakeyi.....

  Zama tayi a parlor ta rike kanta hawaye na gudu a fuskarta,har yaushe ne zaisan muhimmancinta?har yaushene zai dauketa da muhimmanci kamar yadda ya dauki aikinsa?mijinta fari cikinta wanda dik lokacin da take tare dashi tana tsintar kanta cikin farin ciki da nishadi mara misaltuwa amma basa cikakken minti biyar batare da farin cikin nan ya juye zuwa bakin ciki ba,hakan na faruwa ne saboda yanayin da kullum suke ciki na aiki da dare da rana yana kan aikin nasa kamar wani bature....cije lebe tayi tana jin wata kaunarsa a zucuyarta saidai haushin da takeji a yanzun haka yasa tana kallonsa bakim kirin.....wayarta dake jikin carji ta ciro ta dawo ta zauna,share hawayenta tayi dikda wasu ne ke kara zubowa ta daddana numbobi ta kara a kunnenta....

AUREN FARI....Where stories live. Discover now