39

917 68 5
                                        

*💥💥AUREN FARI...💥💥*

*SLIMZY✍🏼*
_Wattpad@slimzy33_

*SADAUKAR WA:*
*HAUWAU MU'AZU AMIR RUMA...*

INA MASOYANA📢📢📢 MASOYA LITTAFIN *AUREN* *FARI* GA RANARKU DON NUNAMIN TSANTSAR KAUNA, KUYI RUGUNTSIMI MU HADU A LITTAFIN *RAMIN MUGUNTA.....* AKAN FARASHI MAI SAUKI 200 KACAL YANZUN HAKA *RAMIN* *MUGUNTA* YA FITA....HADE SUKE DA *RAMUWAR* *GAYYA* DAGA MARUBUCIYAR ZAMANI FEEDHOM....MASU BUKATAR SIYEN TAGWAYE BIYU ZASU BIYA 300
TA WANAN ACCOUNT DIN
👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
2255398727
Zenith Bank
Amina jibril
Shedar biya tun tunbi wanan number 07042277401

*39*
Tsaye jiddah tayi a kusa da gadon da Abdallah yake kwance,ya sakalo hannunsa ya rukota yana murza hannunta,wata harara ta watsa masa cike da fushi tace "au kiran da kayimun kenan?kaje can dakin be isheka ba kenan yanzun kazo nan nika tabani to sakanni"ta fuzge hannunta tana murmuguda masa baki, murmushin kasaita yayi ya lashe lebensa, wani kallo yake bin ta dashi cike da so da kauna "kishi ko?baby nasan kinada kishi nima kaddara ce tasa nayi auren amma ai kin isheni"

Idonta ne yayi kwalkwal kishi ya taso mata ta dubesa kamar zatace wani abu ta kauda kai cikin sauri ya fuzgota ta fada jikinsa ya rungumeta sosai yana shafa kanta,hawaye ne ya gangaro a idonta "ki daina kuka baby kinji?me kikeso?ni kikeso kike kishi na?'bata tankasa ba ta maida kanta gefe juyo da fuskarta yayi suna fuskantar juna yayi mata light kiss a lips dinta "am sorry sweetheart kaddara ce ta riga fata dani dake inda badan hakan ba babu abinda zaisa wani ya shigo rayuwarmu"

"Nika kyaleni nasaka abinci a kitchen kuma kaga munada baki"tayi maganar tana turo baki cike da shagwaba,

Riketa yayi sosai yana kallon dan karamin bakinta "meye amfanin yan matan dake cikin gidan nan?su duba miki abincin mana"yana gama magana ya hade bakinsu waje daya ya kankameta yana kissing....

Ramlah parlor ta fito ta nemi waje ta zauna gabaki daya hankalinta na can wani waje kallo daya zakai mata ka hango tsantsar damuwa da tashin hankali a cikin idanuwanta...

Hira yan matan sukeyi a parlor dukkansu cikin hirar suke lallashin afee akan maganar auren yaya bilal wadda dakyar ta kwantar da hankalinta...

"Nikam wai anty jiddah tafiya tayi ta barmu ta tafi wajen mijinta?"abida tace tana kallon su,da sauri Ramla ta kalli sashen dakin jiddah ta juyo ta bata fuska,

Tabe baki ayshah tayi ta watsawa ramlah harara sanan ta juyo tayi wata shewa "aikam suna can itada mijinta suna soyewa,dan nikam tun shigarsu daki itada ya Abdallah har yanzun bata fito ba"

Kallon juna sukayi sanan suka kyalkyale da dariya...

A tare suka fito jiddah tana murtsike ido Abdallah yakai mata cakulkuli ta goce tana kyalkyala dariya,haka kawai ya tsinci kansa cike da nishadi....

Yar dariya rumaisa tayi a fakaice tace "love birds"ta gimtse baki gani wani kallo da Abdallah yayi mata "ke ina wasa dake ne?".. girgiza kai rumaisa tayi tana gimtse baki dukkansu dariya suke son yi,

Kallon ramlah Abdallah yayi "ki shirya muje dake gaida bilal zamu kai masa abinci"yace yayi gaba yabi bayan jiddah zuwa kitchen.
Kallo tabisu dashi daga ita har shi dukkansu rigunansu a yamutse suke,wani mugun takaici ne ya taso ya tokare mata wuya kamar zatayi kuka ta mike fuuuu ta nufi daki cike da bakim ciki ,bama zanje ba me zanjeyi gidan su bilal kuma?tabdijan ai idan naje gaida bilal nakai kaina wato ma su shirya kenan?nashiga uku....

Tana kwashe abinci a flask yana tsaye bayanta ya harde hannuwansa yana kallonta cike da shaawa da soyayya dirin ya da kyawun sura irin tata yake bi da kallo,ji tayi kamar ana kallonta yasa ta juyo suna hada ido ya kashe mata ido ta zumburo baki gaba tana hararsa..."kaje ka tube kayan jikinka ka shirya kafin muci abinci dasu abidah nima in shirya muje"

AUREN FARI....Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang