*💥💥AUREN FARI...💥💥*
*SLIMZY✍🏼*
_Wattpad@slimzy33_*SADAUKAR WA:*
*HAUWAU MU'AZU AMIR RUMA...*KINA INA📢 *MOM* *SAEED* ...WANAN SHAFIN SADAUKARWA NE A GAREKI KE KADAI TAWAN...SLIMZY NAYI MIKI KAUNA TA HAKIKA🥰❤️
*33*
Cike da tsoro da tsananin kaduwa jiddah ta motsa bakinta kanta a kasa tace "gani Abbah"
"Jiddah....dama jira nakeyi indawo garin inji ko kinada manema aurenki?...yanzun dai su waye ke sonki kuma su waye ke zuwa neman aurenki? inajinki fadamun"
Cikin jiddah saida ya kad'a,ta kara sunkuyar da kai muryarta na rawa cike da kunya cikin sanyin murya tace "Abbah, Bilal ne yake sona sai Abdallah da ya dawo da niyyar aurena a karo na biyu amma ni bilal nakeso shine nakeso in aura"ta karasa maganar muryarta na rawa jikinta na cigaba da tsuma cike da tsoro,
"Jiddah waye bilal?wani irin so yake miki haka da kika zabesa a matsayin mijin aurenki?sanan wace irin halayya garesa da kikai saurin amincewa dashi koko dama can kedashi kundade kuna son juna ne?"abbah ya kafeta da ido,
Tambayar abbah yasa gumi ke karyowa jiddah ta sunkuyar da kai ba tare da ta bashi ansa ba tsawon minti daya batace komiba batada niyyar magana,ummah ce tayi mata magana cikin kosawa da son jiddah ta amsa tambayar ta abbah "ya zakiyi shiru?abbanki ke miki tambaya kinyi shiru ko bakida amsar tambayar tasa ne?"ummah ta tambayeta cikin wani yanayi,Girgiza kai jiddah tayi "inada amsa ummah"
"Tou muna saurarenki"
Dago ido tayi ta kalli yaya ibrahim taga yayi tagumi ya tsareta da ido ta sunkuyar da kai"abbah bamu dade dashi ba,nasanshi lokacin ina gidan Abdallah ne abbah,bilal ya bani gudunmawa a rayuwata ta hanyar samamun farin ciki lokacin da nake cikin kunci a gidan Abdallah,bilal shine yake bani lokacinsa wajen kawar mun da damuwa gudu gada in fada cikin wani hali"sai hawaye ya subucewa jiddah ya soma zuba a idonta sharrr sharr...
Gyaran murya abbah yayi sanan yace"ba kuka nasaki kiyimun ba inaso insamu kwararan hujjoji ne wanda zasusa kiso bilal aminin mijinki kiji kinada interest na aurensa bayan kinsan alaka mai girma dake tsakaninsa da tsohon mijinki,...jiddah bilal be baki gudun mawa ba a rayuwarki sai gudunmawar bata miki suna da yasoyi a zahirin gaskiya"
Da sauri jiddah ta dago manyan idanuwanta da suke cike da hawaye tana kallon abbah ta kasa magana,..
Jinjina mata kai abbah yayi "kwarai dagaske,don jamaa tuni sun dade da jin abinda ya fito dake daga gidan miji kinga kenan ya tabbata cewar da saninki kikai alaka da aminin mijinki da aurenki meye makomarku duka ku biyu?kun taka sharia sanan kunbi son zuciya kun Shiga hakkin aure wanda akan hakan kadai Allah sai ya muku hisabi da tsohon mijinki koda kuwa shine yake shiga hakkinki sai kema kika dauki hakkinsa wajen tarayya da waninsa,wanin ma amininsa ....jiddah bari kiji infada miki kema kinada laifi babba kuma kin dau hakkin Abdallah koda yanada laifi laifinki ya take nasa"
"Abbah....abbah... Bilal fa"
"Bilal mene?shi bilal din ya taba samun Abdallah ya yi masa nasiha akan abubuwan da yakeyi miki?meyasa be sanar dake cewar shi aminin mijinki ne ba idan har dagaske kaunarki yakeyi bazai taba yin soyayya dake da auren wani akanki ba dan haka ki shiga hankalinki ke roki allah gafara sanan ki roki yafiyar mijinki kuma wallahi ko auren bilal kikayi abinda kukai bazai bari ku zauna lafiya ba hakkinsa ne zai bibiyeki....kuma ina kara tuna miki ni din nan da kike ganina kinajin dadi kina ganina da lafiya mijinki shine ya ceto rayuwata ya bani kodarsa amma idanuwanki ya rufe neman kasheshi kikeyi da bakin ciki"..
Cikin Kuka jiddah tace "Abbah dik naji amma ni wallahi banason Abdallah ni bilal nakeso idan ban auri bilal ba mutuwa zaiyi banyi masa adalci ba abba,ka taimakeni kada kace in koma gidan Abdallah bazan koma inyi rayuwa da Ramlah aminiyata ba..."
DU LIEST GERADE
AUREN FARI....
Aktuelle Literaturwayace miki ana bawa namiji dama?babu abinda yake canja namiji sai ikon allah idan kince zaki iya canja Abdallah to kin yaudari kanki mazaasu hali irin na Abdallah wadanda basu da lokacin matansu saina aikinsu daban suke basa taba canjawa don haka k...