*💥💥AUREN FARI...💥💥*
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
*(home of expert and perfect writers)*💡*SLIMZY✍🏻*
_Wattpad@slimzy33_*SADAUKARWA:*
*HAUWA'U MUA'ZU AMIR RUMA...*
*10*
"Barka da zuwa yayah Abdallah...ina yini"rumaisa ke gaida Abdallah a d'arare ta mike meenah kuwa hankalinta na kan waya bata ko dubi inda suke ba rumaisa na satar kallon ramlah tana kokarin ficewa daga parlorn ya dakatar da ita "rumaisa "
"Naam yaya"ta juyo ta sunkuyar da kai,"Dan Allah kai ramlah toilet tayi fitsari shi ya biyo da ita nan"
Kokarin zama yakeyi,ummah ce ta fito sanye da Atanfa dinkin bubu tayi mata kyau da farin glass a idonta "nakejin murya kamar ta Abdallah..."ta karaso
Da sauri Ramlah ta tsugunna ta zube "ina yini ummah...barka da yamma"
Sosai ummah ke kallonta Tana kokarin gano inda tasan fuskarta "barka dai lafiya lau, kamar kawar jiddah ko? wadda ta amshi plate a hannuna ko?"..jinjinawa ummah kai ramlah tayi cike da ladabi "nice ummah"ta mike tabi rumaisa dake biye da ita.
"Abdallah daga ina Haka kaida kawar matarka,kai yarinyar nan akwai ladabi wallahi naji Dadin nunamin mutunci da tayi ranan da sukazo sabanin waccen matsiyaciyar"
Cije lebe Abdallah yayi yana jin zafin zagin da ummah tayiwa jiddah "umm a wajen aikinmu tasamu aiki yanzun ma zan sauketa in biyo nan tacemun tana jin fitsari shine muka biyo"
Shigowar su Ramlah yasa ya mike "sai muje koh?"
Jakarta ta bude kanta a kasa ta ciro wata farar jaka,mai kyaun gaske turarruka uku ta fiddo "gashi rumaisa,keda meenah da afee"
"Laaaa harda hidima haka anty ramlah mungode sosai"rumaisa tasa hannu ta karba,meenah ta yunkura daga kwancen ta danyi murmushi "mungode Anty"jinjina kai tayi batare da tace komi ba Tana kokarin fita ummah tace "ki gaida ummanki"
Dan durkusawa tayi ta amsa da "zataji"... Abdallah kuwa tuni yayi gaba abinsa tabi bayansa....
"Ummah kinga turaren nan fa tsada ne dashi ta bamu,daga biyowa fitsari?"
"Kila nata ne dai ta siya ta bamu kyauta"rumaisa tayi maganar Tana kallon ummah....jinjina musu kai tayi ummah ta zauna tana fuskantar Tv.
Minti minti yakan ja numfashi yana driving samm bayason yadda ummansa ta tsani jiddah bashida yadda zaiyi gashi kaf kannensa sun hade kai da mahaifiyarsa,afnan ce kadai keson jiddah gashi jiddar ba wani abu tayi musu ba tsabar tsana ce.... mamaki ne ya lullube Abdallah yadda ramlah ta ciro turare ta bawa kannensa,me hakan ke nufi?ko tayi hakan ne don ta samawa jiddah muhalli a zukatan kannensa da ummahn sa tunda kawarta ce?..tunani yake kala kala har sukazo junction dinsu ramlah yayi parking "su rumaisa sun gode da turare fa"yayi maganar kansa na kallon titi ko inda take be kalla ba,
Ajiyar zuciya tayi "kannena ne,ummah kuma uwace a gareni sanan jiddah Aminiya ta ce"jinjina mata kai yayi ya kunna motar yaja abunsa...Ita jiddah meyasa batayi tunanin yi musu da kanta ba,saidai ta saka kawarta ta nema Mata muhalli a zukatan zuriar sa?da alama ummah taji dadin kyautar da ramlah tayi musu harda su rumaisan ma...kada kai yayi ya cije lebe,ya sauke ajiyar zuciya... Ramlah tanada son kyautatawa mutane gashi bata fushi,inama haka jiddarsa take?kullum sai son soyayya amma batasan yadda zata ja raayinsa ba,ko batasan cewar mace tana canja mijinta bane?....tunanin da yakeyi kenan har ya shigo cikin street dinsu shiru babu kowa haka ya iso gate din gidan ya shiga horn...da sauri mai gadi ya bude masa ya shige....

YOU ARE READING
AUREN FARI....
General Fictionwayace miki ana bawa namiji dama?babu abinda yake canja namiji sai ikon allah idan kince zaki iya canja Abdallah to kin yaudari kanki mazaasu hali irin na Abdallah wadanda basu da lokacin matansu saina aikinsu daban suke basa taba canjawa don haka k...