*💥💥AUREN FARI...💥💥*
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
*(home of expert and perfect writers)*💡*SLIMZY✍🏻*
_Wattpad@slimzy33_*SADAUKARWA:*
*HAUWA'U MUA'ZU AMIR RUMA...**Inawa daukacin masoyana makaranta littafaina da na haske writers gabaki daya Barka da sallah Allah ya maimaita mana...SLIMZY✍🏻*
*9*
Tafe suna yana kallon sashen ta yana jin kansa cikin wani irin nishadi da bai taba jinsa ba,kallon mirror din motarsa yayi da sauri ya sake kallo abinda idonsa yake gane masa ne yakeso ya tabbatar shin wanan Abdallah ne yake biye dasu ko yaya?kara kallon mirror din yayi wanan karon waya yake latsawa daga bayansu sakamakon wutar traffic da ta tsaida motoci a junction sin ministry of education kaduna....wayarsa ce tayi kara tana ajiye yayi saurin dauka ganin tana kallon inda wayar ke vibration Abdallah ne ke kiransa, shin kodai ya gansu ne?wani irin bugu zuciyarsa tayi yana kallon call din kafin ya furzar da iskar bakinsa cike da kwarin gwiwa "hello man ya ne?"
"Lafiya lau,na biyoka inason ganinka muyi magana but na hangi kamar kanatare da budurwarka dikda ban kalli fuskarta ba dai na juya please ka sameni a gida kawai muyi magana"
Wani gumi ne ya karyowa bilal ya sauke ajiyar zuciya"owk"ya datse wayar ya kalli jiddah da ta kafesa da ido,sosai take kallonsa gabanta ke faduwa domin tana jiyo sautin murya kamar ta mijinta Abdallah,shin Abdallah yasan bilal ne?...da sauri zuciyarta ta kaudar mata da tunanin Abdallah bazai taba sanin bilal ba,ajiyar zuciya ta sauke ya dubeta ya Kai hannunsa ya shafi gefen fuskarta ta lumshe masa ido sosai take shagala da kallonsa bata gajiya da kallon nasa,
Lallai yau sunyi narrow escape yau da abdallah ya gansa da matarsa jiddah a matsayinsa na amininsa to yace masa mene? akwai kunya sosai saidai babu wani abu da zaiji face damar samun mallakar auren jiddah...shin meyasa ma be gansu ba ayita ta kare?....
Ko wannensu tunani suke har suka iso crystal garden inda kasantuwar ranar aiki ce babu mutane dayawa tsurarun mutanene yawancin su ma masu aure ne.....parking motarsa yayi ya ruko hannunta "let's go"
"Amma dai bazamu dade ba ko?"tayi maganar muryarta na rawa tana kallon kwayar idonsa,gyada mata kai yayi yadan matse hannunta kafin ya sake ta suka fito a tare....
********
Kamshin turarensa ne ya sanar mata da dawowarsa da sauri ta kalli hanyar shigowa bata gama gyara zamanta ba ya shigo,shagala tayi da kallonsa yana tafe yana latsa waya "barka da zuwa sir Abdallah....har ka dawo?sannu ka gaji ko?"Kallonta yayi,ji wanan waye yace mata shi ya gaji?mtsww yadan ja tsaki "na dawo"ya amsa a takaice yayi gaba ta bi sa da kallo,jakarta ta janyo ta bude turaruka guda uku ne ciki ta ciro tayi murmushi for rumaisa,afee da meenah nasan zasu so shi amma ta yaya zataje gidan mahaifiyar Abdallah domin kamun kafa?...murmushi tayi dabarar da ta fado masa...
Lumshe ido Abdallah yayi kyakkyawar fuskar jiddah ce ta hasko masa a daren jiya lokacin da take tambayarsa me kiran nasa, Yana missing din matarsa yanason kasancewa da ita amma samm aikinsa baya basa wanan damar,shiba mutum bane meson yawan nanikewa mace salom ta rainasa amma tabbas yau ya tanadar mata tarairaya ta musamman....
*******
Dan zukan lemo yayi ya dire cup din yana facing dinta...gabaki daya yanayinta ya canja sammm yana lura da akwai abinda take bukata saidai besan ko meye shi dinba "yadai my lilly?"ya dage mata gira, sunkuyar da kai tayi tana girgiza kai bugun zuciyarta na karuwa,"My lilly....."ya kira sunanta cikin wata irin kasalalliyar murya "hakika na shiga wani yanayi a ta dalilinki....na tsunduma kaina cikin wani harkalla da bazan iya fita ba sai ke"da sauri ta dago kai tana kallonsa idonta cike da tsoro,kada kai yayi "nasan kina mamakin meye ne wanan harkallar,...harkallar bata wuce soyayyarki ba da taimun dirar mikiya batare da ta shawarci zuciyata ba,hakika soyayya bataimun adalci ba... kanwa ta na daukeki amma at the end na kamu da matsananciyar kaunarki"cikin wata iriyar murya mai kama da rada yake maganar,.... innahlillahi wa innah ilaihi... ta furta a zuciyarta cike da tsoro tabbas na yaudareka da na kasa fada maka nidin matar aurece ga waninka,saidai dagani har kai zuciyoyin mu basuyi mana adalci ba....inajin sonka a can kasan zuciyata,saidai soyayyar mijina itace ke yawo a jijiyoyin jikina....kulawarka da nuna tausayawa da nake gani a kwayar idona sune suka shagaltar dani na mance da igiyar aure uku da suke daure a kaina....ta shagala cikin kogin tubani tabo lallausan hannunta yayi ya langabar da kai kamar zaiyi kuka yanajin zuciyarsa na kara azalzalarsa "kinyi shiru jiddah... kiyi magana kimun alkawari bazaki taba iya rabuwa dani ba...kimun alkawari komi runtsi dik wuya a nan gaba bazaki barni ba koda wani mummunan lamari ya faru a rayuwarmu zaki amince da aurena idan nazo miki dashi?"..kallonsa take maganganunsa na barazanar tarwatsa mata kwakwalwar kai,to kodai yasan cewar tana da aurene yakeso tayi masa alkawari koda mummuna lamari ya faru bazasu rabu ba?wani mummunan lamari ne ya wuce wanda mijinta yasan tana mu'amala da wani da har zasu shiga wani hali?...me kalaman bilal ke nufi ne?gumi ne ke karyo mata jikinta yayi sanyi kasa motsi tayi saidai bazata mance da halarci da bilal yayi mata ba na gayyato farin ciki cikin rayuwarta, tsintar kanta tayi tana magana "nayi maka alkawari bilal....komi runtsi bazan taba rabuwa da kai ba saboba ina matukar...."sai kuma tayi shiru muryarta ta kama rawa "ki karasa mana jiddah ki fadamun kina matukar mene?please mana love ki fadamin kinji hakan zaisa in kwana cikin farin ciki da murna"girgiza kai tayi tana murmushi ta dubi agogon dake makale a hannunta laasar ta kusa..."inaso in koma please nace zaka saukeni a wani gida"gyada mata kai yayi yana kallon dan bakinta...i cant wait na amsheki a hannun wacen wawan ya furta a ransa mikewa yayi ya mika mata hannu babu musu ta dora hannunta akan nasa ya dagota suna dariya...sosai mutanen wajen ke kallonsu wani mutumi nesa dasu kadan ya kashe musu hoto a waya....

YOU ARE READING
AUREN FARI....
General Fictionwayace miki ana bawa namiji dama?babu abinda yake canja namiji sai ikon allah idan kince zaki iya canja Abdallah to kin yaudari kanki mazaasu hali irin na Abdallah wadanda basu da lokacin matansu saina aikinsu daban suke basa taba canjawa don haka k...