40

1.5K 77 10
                                    

*💥💥AUREN FARI...💥💥*

               *SLIMZY✍🏼*
          _Wattpad@slimzy33_

*SADAUKAR WA:*
*HAUWAU MU'AZU AMIR RUMA...*

INA MASOYANA📢📢📢 MASOYA LITTAFIN *AUREN* *FARI* GA RANARKU DON NUNAMIN TSANTSAR KAUNA, KUYI RUGUNTSIMI MU HADU A LITTAFIN *RAMIN MUGUNTA.....*  AKAN FARASHI MAI SAUKI 200 KACAL YANZUN HAKA *RAMIN* *MUGUNTA* YA FITA....HADE SUKE DA *RAMUWAR* *GAYYA* DAGA MARUBUCIYAR ZAMANI FEEDHOM....MASU BUKATAR SIYEN TAGWAYE BIYU ZASU BIYA 300
TA WANAN ACCOUNT DIN
👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
2255398727
Zenith Bank
Amina jibril
Shedar biya tun tunbi wanan number 07042277401

LAST PAGE...THIS PAGE IS DEDICATED TO *ANTY KHADIJA*  A.K.A *INNAH WURO*  ILUSM🥰❤️

                      *40*

Babu inda baya rawa jikin ramlah,gumi ne yake karyo mata kamar an kwara mata ruwa,....wani kallo Abdallah ke watsa mata cike da tsana idanuwansa sunyi jajir ya ma rasa abinda zaice jinsa yake tamkar mutum mutumi,gashi recording din be gama ba ya cigaba da yi amma gaba daya bashi da sauran common sense a jikinsa.....cikin karsashi ya kira sunanta "Ramlah"gabanta ya yanke ya fadi saboda yadda ya kira sunanta,dagowa tayi ta kallesa tayi saurin sunkuyar da kai cikinta na kara murdawa kamar ta saki fitsari....."Ramlah meye jiddah tayi miki haka da kikaci amanarta a matsayinta na aminiyarki a matsayinta na yar uwa data daukeki metayi miki haka Ramlah ko ince meye mukayi miki?"ya zabura ya mike yana takowa cikin daga murya yake maganar,itako ramlah ji take kamar ta kwasa a guje batada bakim magana,har ya tako gabanta ya tsaya...jira kawai takeyi taji saukar duka...."Ramlah na dade da yin bincike akan cewar dik ranan da bilal zaizo gidan nan wajen jiddah kema kina zuwa, tun daga ranar nasa ko kwanto a cikin zuciyata nasan kinada masaniya kuma kinada hannu,dalilin da yasa bance miki komiba banida kwakkwarar hujjar da zan turkeki akan hakan,yau saiga muryarki baro baro kina cewa bilal zaki tona mishi asiri ta hanyar turamin video dinsa yana taba nonon matata"...jikinta na rawa ta shiga girgiza kai "Abdall....ah dan allah kayi hakuri wallahi sharrin shedan ne da sharrin zucuya....da soyayy....ar"ai bata karasa ba ya zabga mata mari ya shiga nunata da yatsa yana karkada kai cike da fushi "karki kuskura ki kira shedan kice sharrinsa ne don ke kanki ma shedaniyar kanki ce da kanki Ramlah....kinyi amfani da zuwa inda take kinci amanarta kin cutar da ita Ramlah"ya fuzgota ya kai mata duka a fuska tayi saurin durkushewa a kasa Abdallah ya shiga dukanta ta ko ina ko gani bayayi ganin hakan yasa ya saketa yaje jikin kofa ya rufe kofar  ya nufi daki,

Cikin tashin hankali jiddah ya yunkura tana ganin jiri ga rashin karfi tunda suka soma ta kanta takeyi dan amai takeyi sosai har ya fito da gajeran wando da belt a hannunsa ya shiga kaiwa ramlah ta ko ina tana ihun ceto,

Mai gadi kuwa daga nesa yake jiyo ihu kamar ana duka sai tayi tunanin makota ne jin ihun yaki karewa yasa ya mike ya nufo cikin gidan yana kokarin murda kofar yaji Abdallah na fadin "kin cucemu ramlah kin shiga tsakanin mata da miji,kin shiga tsakanin aminai kin farraka ahalinmu kika shigo cikin mu dik saboda aminiyarki"....rike baki baba mai gadi yayi a fili yace "kwai ya fashe kenan....tou Allah ya kyauta"ya juya cikin sauri ya nufi gate din gidan inda ake horn,

Motar bilal ce ta shigo ta haske harabar cikin gidan,yana jiyo ihun ramlah ya shafa sajensa sanan ya kashe motar ya fito shida afee ne yana sanye da kananan kaya riga shirt da blue din wando tana sanye da tsadaddiyar jallabiya baka ta yane kanta,

Zaro ido afee tayi "yaya bee kanaji fa ihu nakeji cikin gidan nan kamar ihun anty ramly"

Tana kokarin bude motar a guje ta nufi kofar shiko bilal cikin takun kasaita yake takowa ya karaso wajen da afee take tsaye tana murda kofa taki buduwa ta koma jikin window tana bubbuga window din amma shiru.....cikin tashin hankali take salati "innahlillahi wa innah ilaihi rajiun"

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Oct 31, 2020 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

AUREN FARI....Where stories live. Discover now