💥 *💥AUREN F'ARI....* 💥💥
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
*(home of expert and perfect writers)*💡*SLIMZY✍🏻*
_Wattpad@slimzy33_*SADAUKARWA:*
*HAUWA'U MU'AZU AMIR RUMA...**8*
Wani irin kallo take masa mai cike da ma'anoni kala kala,nan da nan cikin mintuna da basu wuce uku ba idanuwanta suka kankance sukai jajir yana hango yadda bugun zuciyarta keyi a kirjinta...shima wani irin kallo yakeyi mata tamkar zai hadiyeta yana son matarsa anma samm batasan yadda zata zauna dashi ba batasan yadda zata koya masa abinda takeso ba shi be saba da hakan ba amma ta kasa ganewa fitinar jiddah tayi yawa...ji yake tamkar ya rungumeta ya samu sassaucin soyayyarta dake ruruwa a zuciyarsa amma bashida yadda zaiyi....kallon da yake mata yasa ranta ya kara baci kallon agogo tayi ta maida kai ta dauki wayarta ta mike cikin fushi ta nufi dakinta fuuuuuuu....gurgiza kai yayi yaja nunfashi ya sauke....
Gado ta haye ta kwanta,sauke numfashi take a hankali a hankali ta soma samun sassaucin rad'adin da takeji a ranta,ajiyar zuciya ta sauke zuciyarta batai mata adalci ba da take raya mata kishi akan kawarta ramlah bayan tasan yadda suke ramlah bazata taba kallon Abdallah da wata manufa ba koda yake haka Allah ya halicceta da son mijinta....runtse idonta tayi bilal ne ya fado mata a rai lokacin da yake rungumarta a jikin kofar koshin da lokacin da yakai mata sumba a gefen wuyanta ..murmushi ne ya subuce mata har batasan takai hannunta ta shafo gefen wuyanta ba....nan da nan taji wani sabon shauki akan bilal wanda bata ji sa ba lokacin da yake gidan..."yayana yana son harkar turawa"tayi dariya inba bature ba waye zai rungumi kanwarsa harda kiss...mantawa tayi da wani bacin rai cikin sauri ta kunna data ta shiga laluben contact dinsa tana dubawa ta gansa online..dafe kirji tayi ta sauke ajiyar zuciya....
*******
Tana shirin kwanciya ta saka kayan bacci tana feshe jikinta da turare aka turo kofa,cikin sauri ta juya ummahta ce,fad'ada murmushinta tayi ta zauna gefen gado tana kokarin kwanciya...ummah ta karaso ta tsaya "har zaa kwanta ramlatu?""Ehh ummah...inaso in kwanta saboda gobe in tashi inyi shiri da wuri banaso ma oga ya rigani zuwa wajen aiki sanan inaso in dan soya samosa a kitchen kafin in fita shiyasa ma nayi komi daddaren nan kafin in kwanta"
"Toh... Allah ya bada saa ramlah a dai kula a kama kai sai Allah ya fito miki da mijin aure da kikeso shima yake sonki"
Kallom ummah tayi tai murnushi "ummah...kenan kedai kiyimun addua insamu cikar burina don yanzun haka akwai?"sai kuma ta rufe fuska tana dariya...itama dariyar ummah tayi tana kokarin juyawa "Allah yasa Ramlah ya cika miki burinki"
"Saida safe ummah"ta gyara kwanciya ta kwanta kunna data tayi ta duba jiddah na online...massage din jiddah ta gani kamar haka "kawata...shine kika kira mijina daddare?kikeso kisa zuciyata ta buga?kinfi kowa sanin yadda nake kishin Abdallah har yan uwansa"...wata yar dariya ramlah tayi lallai kina gab da mutuwa don saina tabbatar da na samu kan mijinki na shigo gidanki na goga dake a matsayin matarsa ta sunnah ba dadiro ba don Abdallah ba kalan namijin da zaa bi a waje bane kuma banida raayin binsa...badai bakisan yadda zaki hakuri ki koyi jan hankalin mijinki ba?ki canja sa da kanki?hmmm zan canja Abdallah dik runtsi.....
Kin mata reply ramlah tayi kawai ta kashe datar ta ma ta kwanta ta rufe idonta tana hararo kanta kwance a kirjin Abdallah...
Karfe biyu na dare suna manne a waya itada Bilal sun gagara chat din hira kawai take masa ta mance da wani mijinta "ya bila...."ta kira sunansa cikin wata irin murya.
Cikin murya mai kama da rad'a "my lilly....am serious missing u wallahi...kefa kyakkyawa ce wani ya taba fada miki hakan?"
Farrrr tayi da ido cikin duhu "babu wanda ya taba fadamun haka saikai my yaayah"tayi maganar cikin sanyin jiki...kallom kofa takeyi ko zai shigo ya lallasheta amma shiru muryar bilal ce ta bugi kunnenta "gobe kinaso mu hadu ko?tou kiyo kwalliya sosai inaso inganki cikin make up kishafa komi na adon mata kinji my baby sis?"
YOU ARE READING
AUREN FARI....
General Fictionwayace miki ana bawa namiji dama?babu abinda yake canja namiji sai ikon allah idan kince zaki iya canja Abdallah to kin yaudari kanki mazaasu hali irin na Abdallah wadanda basu da lokacin matansu saina aikinsu daban suke basa taba canjawa don haka k...