*💥💥AUREN FARI...💥💥*
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
*(home of expert and perfect writers)*💡*SLIMZY✍🏻*
_Wattpad@slimzy33_*SADAUKARWA:*
*HAUWA'U MUA'ZU AMIR RUMA...**13*
Fuskarta sharkaf da hawaye ta fito daga bedroom idanuwanta sun kankance saboda tsananin kishin dake taso mata ji takeyi kamar ta shake masa wuya,tsaye tayi akansa hawaye na sauka a idonta kamar ruwa,shiko Abdallah abinda ke gabansa ya cigaba dayi ko kallonta beyi ba,"Abdallah,ashe cin amanata kakeyi a waje bansani ba?kana can waje kaida matan banza"
Da sauri ya dago kai ya watsa mata wata harara ,a haukace jiddah ta cigaba da magana "Allah ya isa tsakanina dakai tunda gani gaka a cikin gida amma babu abinda nake tsinana maka babu abinda kakemun saidai munzauna kamar hoto ashe akwai wadda take gamsar dakai karuwarka"....
Wani irin kallo ya watsa mata zuciyarsa na tafarfasa bayason abinda zaisa ya aikata abinda zaizo yana danasani daga baya,so far dik wanan maganganun da takeyi kishi ne,amma ai kishi ba hauka bane "kada kisake hadani da kalmar karuwa"
"Karya akaayi?ba karuwar bace?inba karuwa bace meyasa zata kiraka a waya kana tare da iyalinka?ko abinda kukeyi a waje be isheta bane take kiranka tayi kewarka?"
Zuwa wanan lokacin jikin Abdallah ya soma rawa zuciya kawai ke taso masa kalaman jiddah da take jifansa dashi tamkar Tana watsa masa rushin wuta,mikewa yayi tsaye yana nunata da dan yatsa "Ina gargadinki da ki iya bakinki idan ba haka ba"
"Idan ba haka ba me?mezakayimun ?ai nasan komi dik abinda kakeyi a tafin hannuna kakeyinsa Abdallah kuma Allah ya isa tsakanina dakai sai allah yasaka mun mugu azzalumi,saidai ka barni da shaawarka kamar zata kasheni bakada lokacina sai na matan banza"
A zuciye Abdallah ya shararawa jiddah mari biyu masu kyau gefe da gefen fuskarta wadanda saida taga giftawar taurari a idanuwanta,lokaci daya kunnuwanta sukayi dummmmm tamkar an zuba mata ruwa cikinsu....cakkkk tunaninta ya tsaya tana kallonsa ruwan hawaye kuwa sai ambaliya sukeyi daga idannuwanta hannuwanta biyu na dafe a kumatunta..."ka..mar.."bata karasa ba cikin kakkasar murya ya soma magana "an mareki jiddah...ke wacece da bazan mareki ba matukar bazaki fasa hadani da kalmar karuwa ba da matan banza ba a waje bazan fasa marinki ba saboda ni ba mazinaci bane,wawuya jahila wadda kishi ke kokarin jefata a halaka,kishinki na banza da bakisan yadda zakiyi ki janyo hankalin mijinki ba?ita wadda kike jifana da kalmar karuwa da ita a yanzun kokarin kusanta kanta dani take yayinda ke kike kokarin nisanta kanki dani,bakida hakuri kullum complain ke kenan kece akewa laifi ke baki laifi,idan bani da lokacinki ko bana kulawa dake ke bakisan kissar da zaki kusanta kanki danib"..cikin daga murya yake maganar muryarsa na amsawa a parlorn,jiddah kuwa ta kafesa da ido bugun zuciyarta na karuwa ji take kamar zata hadiyi zuciya ta mutu,
Taku daya biyu yayi ya juyo ya cigaba da magana "bakisan,kiganni cikin damuwa ko bacin rai kiyi kokarin faranta mun ba,bakisan ki jure kiyi hakuri da halayyat mijinki ba kiyi kokari wajen janyo hankalinsa gareki,mahaukaciya dabba ...tou kisani wanan abun da kikayi kin taka mataki na farko da zan auro mace in kawota cikin gidan nan koda banida niyyar hakan,domin a yanzun zuciyata tafara mun kokwanto akan tsantsar biyayyar da karuwar waje take nuna mun ke kuwa kina nan kina girman kai....kin kasa tarairayar mijinki,inaji a jikina a wanan tafiyar tabbas zan kusanto da ita gareni saboda ta cancanta,tasan farin cikina,tasan bacin raina tasan damuwata,dik wani mood nawa tasani jiddah....uwa uba tana hakuri da halayyata kullum burinta be wuce ta samu abinda zataja hankalina dashi ba dik yadda na kaiga rashin sakar mata fuska kuwa....mace mafi kusanci dake tasan mijinki fiye da ke"....ya watsa mata wani kallo mai cike da takaici sanan ya juya ya sunkuci laptop dinsa da wayoyinsa ya nufi bedroom dinsa kansa na sara masa saboda takaici,
YOU ARE READING
AUREN FARI....
General Fictionwayace miki ana bawa namiji dama?babu abinda yake canja namiji sai ikon allah idan kince zaki iya canja Abdallah to kin yaudari kanki mazaasu hali irin na Abdallah wadanda basu da lokacin matansu saina aikinsu daban suke basa taba canjawa don haka k...