7

811 66 2
                                    

💥 *💥AUREN F'ARI....* 💥💥

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
*(home of expert and perfect writers)*💡

       *SLIMZY✍🏻*
_Wattpad@slimzy33_

*SADAUKARWA:*
*HAUWA'U MU'AZU AMIR RUMA...*

                    *7*

Bilal ko parlon ya shiga bi da kallo zuciyarsa nayi masa d'ar d'ar...tabbas nan gidan amininsa ne da yazo jiya kuma ya tabbata jiddah matar Abdallah amininsa ce suke tarayya, yanayin ta ya nunar masa akwai wani abu dayake damunta,yarinya ce tausayi take bashi sosai kamar jiddah kamata yayi ace tasamu miji meji da ita da soyayya da kulawa,samun mace zukekiya a wanan zamanin kamar jiddah sai an tona sanan a kamalarta ya nuna cewar zatayi hakuri... gashi cikin yan kwanaki ya saba da ita yana matukar sonta soyayyarta a jinin jikinsa take yawo matar amininsa tun suna yara,....tunani yakeyi har ta iso da flask ta ajiye a gabansa da plate da lemo ta dire masa a gaba ta zauna ta zuba tagumi tana kallonsa ko kifta ido batayi,..ayyanawa take ina ma Abdallah irin halin bilal garesa?da bata fada son wani ba alhalin tana da miji dikda bata gama gasgata soyayyar da takeji tana neman kamuwa da ita ba ta yaya bilal...a jikinsa yaji tamkar ana kallonsa hkn yasa ya dago manyan idonsa ya dora akanta amma bata sani ba,shiru yayi na dan wani lokaci kafin ya nisa "my lil princess meyake damunki naganki tamkar kina cikin damuwa menene akwai wani abu da kike bukata ne?...ina su ummahnki?naga gidan kamar ke kadai"...ya jero mata wadanan tambayoyin a tare kafin ya tsareta da ido yana so yasan amsar da zata basa,girgiza kai tayi ta sunkuyar da kai tana kokarin boye kwallar dake shirin kubuce mata "ummah na basa nan sunyi tafiya sun tafi dubai sai wani lokaci zasu dawo"ta sharo masa karya...yadda tayi maganar muryarta na rawa yasa ya danyi murmushin gefen fuska yasan karya ta sharo masa,dago ido tayi ta kallesa ko ya gano karya tayi masa sarai ya lura da hakan sai kawai ya kauda zarginta da bude flask din dake gabansa,tururin dankali da kamshin plantain ya gauraye parlorn,jan numfashi yayi ya sauke yana kallonta yana murmushi "waya sanar dake cewar banyi breakfast ba na fito?"ya kashe mata ido,girgiza kai tayi tanajin wani shock a jikinta....wani irin yammmm takeji saboda matsananciyar shaawar dake addabarta a wanan lokacin..."ko baa fadamun ba nasan yaayah na dan gayu ne ai nasan baya breakfast da wuri"...ido ya zura mata yadda bakinta ke rawa tamkar mai zazzabi,hannu yasa ya dauki dankalin guda daya ya kai bakinta...ido ta sa masa batare da ta amsa ba bugun zuciyarta ya tsananta nan da nan fuskarsa ta juye mata zuwa fuskar mijinta Abdallah...lumshe ido tayi ta bude sai taga bilal ne gabanta wasu zafafan hawaye suka zubo mata...kafeta yayi da ido yanajin tausayinta na ratsa zuciyarsa..ya tabbatar Abdallah ne ya bata mata rai in haka ne meyasa shi bazai lallasheta ba yadda zata soshi ta shaku da soyayyarsa har bazata iya rabuwa dashi ba?. hannunsa yasa ya dangwalo hawayenta yakai bakinsa ya lashe,idanuwanta sunyi jajir take kallonsa ya mika mata dankalin "oya let's eat together"yayi maganar da tsare gida ..ga mamakinsa yaga ta buda baki yasa mata ta shiga taunawa a hankali ...shima ya dako yasa a bakinsa a haka yake bata yana ci har suka cinye a tare dik cikin damuwa jiddah take,dik motsinta a idonsa takeyi,remote ta dauka ta canja tashar zuwa zee world ana wani film na soyayya...flask din ta dauka ta mike cikin tafiyarta mai daukan hankali tafiya take mazaunanta suna motsawa...hannu yasa ya shafa kansa ya hura iska...idanuwansa sunyi jajir saboda yadda yakejin kaunarta na fuzgarsa...

  Tana tsaye gaban sink tana kokarin wanke kwanuka hawaye kawai ke zuba a idanuwanta....sammm zuciyarta batayi mata dadi na kawo namiji da tayi gidan aurenta amma batada option,she needs to be happy always,babu farin ciki a gidan Abdallah ina ma bashi ta aura ba?da bata nemawa kanta zunubi ba gashi kiri kiri zuciyarta ta kasa mata adalci ta kamu da soyayyar wanin mijinta... innahlillahi wa innah ilaihi rajiun....hawaye ke gudu a fuskarta...tsaye yayi jinta shiru yasa ya biyo ta...har ya karaso dab da ita batasani ba saida yakai hannunsa fuskarta yana share mata hawaye "kina boyemun damuwarki my lil princess...na tabbatar kinada damuwa yasa na shigo rayuwarki don in zame miki haske me haska duhun da kike ciki,meyasa kike kuka?digar hawayenki tamkar digar dalma nakeji a cikin zuciyata...inajin radadi da zugi idan har naganki cikin wanan halin...haba jiddah"yayi maganar a sanyaye ..gabanta kw faduwa cikin kitchen ya biyota?kallonsa takeyi idonta jajir ta girgiza kai "muje parlorn kaji?"cikin dasasshiyar murya tayi maganar jikinta na karkarwa...mika hannu yayi ya ruko hannunta ha fuzgota ta fada jikinsa ya kankameta....rawa jikinta ya somayi wani irin abu ke fuzgarta idan ta kara minti biyar a kirjinsa zata iya suma,saidai rukon da yayi mata bazata iya fuzgewa ba...kallon yadda take hawaye yake nan da nan idonsa suka cicciko da hawaye "kinaso inyi hawaye ko?bazan iya jure ganin kyakkyawa kamarki cikin wanan halin ba"fashe masa tayi da kuka saboda yadda takeji a jikinta shaawarta na kara karuwa musamman tsintar kanta da tayi a kirjin wani namiji ba mijinta ba....ta yaya zata cigaba da aikata hakan da aurenta?kukanta ya karo....pink lips dinta yake kallo da suke attracting dinsa ji yake tamkar ya hadesu ya tsotse su,soyayyar matar abokinsa kullim karuwa take cikin zuciyarsa...ina ma ace shine ya mallaketa?da taga soyayya...ganin tana kici kicin kwacewa yasa ya hura mata iska a fuska "is ok zan sakeki amma sai kinyimun alkawari hawayen nan zasu k'afe kuma bazasu sake zuba ba"...kallonsa take yadda yaka mata magana cikin sigar lallashi ina ma ace mijinta ne yake mata wanan tarairayar? runtse ido tayi ta budesu ta kwantar da kai a kafadarsa....mamaki ne ya lullubesa yasa hannunsa ta baya yana shafa bayanta a hankali wani irin abu takeji kamar tafiyar tsutsa da tayi saurin janye jikinta tana murmushi,shima murmushin yakeyi ya dage mata gira..."muyi wanke wanken a tare ko?"daga masa kai tayi alamar eh sai kawai ya nannade hannun shirt dinsa ya karaso tabisa da kallo sosan wanke wanken ya dauka yana yi ta tsaya gefensa "kawo inyi banaso kasha wahala"

AUREN FARI....Where stories live. Discover now