2

1.6K 77 1
                                    

💥 *💥AUREN FA'RI....* 💥💥

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
*(home of expert and perfect writers)*

       *SLIMZY✍🏻*
_Wattpad@slimzy33_

*SADAUKARWA:*
*HAUWA'U MU'AZU AMIR RUMA...*

*HAPPY BIRTHDAY TO YOU MY MENTOR....BILLY GALADANCI... ILYSM*🎂❤💋

                    *2*

Shiru Ramlah tayi tana kallon jiddah cike da tausayawa,hawaye ne suka soma zubowa a fuskarta shaffff shaffff hakan yasa jiddah ta kara narkewa da kaunar kawartata aminiyarta....zuciyarta a karaye tace "banida kamarki kibar kukan nan ramlah ki fadamun mafita kawai abinda zai fusheni nake bukata,ina bukatar taimako banida wanda zai bani shawara kaf duniyar nan daya wuceki domin na yarda dake"tasa hannu ta goge hawayenta,runtse ido ramla tayi bugun zuciyarta ya tsananta tabbas kukan farin ciki takeyi a zahiri amma a bad'ini kuwa tanayi ne don jiddah ta kara gasgata irin yadda ta damu da ita, katse mata tunani jiddah tayi "come on ina saurarenki kawata"

"Hakika kina bukatar taimako da shawara,saidai ke kin kasance bame son social life bace,kawai dai kinada ilimin ne amma rayuwa irinta wayayyu baki fiye sonsu ba jiddah,kuma rayuwar nan matukar kanason farin ciki to dole ka cire duhun Kai ka waye kamar yadda sauran mata sukeyi wadanda mazajensu basu fiye basu lokacinsu ba"gaban jiddah ne ya fadi me ramlah ke nufi wato tabi maza da aurenta ko yaya?...kallon da ramlah keyi ma jiddah take ta karanci inda jiddah ke hasasowa,hmmmm bazan doraki a hanya yanzun ba bazan taba fito miki a mutum ba saidai a hankali zaki hau hanyar da kanki,dukkansu shiru sukayi,kafin daga bisani ramlah ta nisa"nasan inda tunaninki yaje,sammm bana miki fatan wanan kazantacciyar rayuwar da sauran matan aure sukeyi na huld'a da wasu mazajen da ba nasu ba dikda mazan keda laifi 70%wasu kuma matan ne masu son abun duniya da kwadayi"ajiyar zuciya jiddah ta sauke"har naji Dadi kawata wallahi har gabana ya fadi da naji kin ambaci wayewa da social life,yanzun fito dani haske don kinsani a duhu kin kuma bani a dukunkune"...murmushin nasara ramla tayi "kinada babbar waya ta kece raini ai kin wuce bacin rai,kawata daurewa zakiyi kisa kanki rayuwar chat kina fira da kawayenki da abokan arziki suna debe miki kewa,akwai abubuwan da waya ke debe maka kewa dasu a wanan hanyar kake gogewa ka waye ka koyi abubuwa da dama,sanan koda yaushe kina kunshe kanki a daki kamar wata kura,kuma sunan kin iya mota amma ko nan da can baki fita balle kiga gari ki hadu da sababbin mutane kiyi rayuwa kamar ko wace mace me yanci, Abdallah bazai taba hanaki dan zuwa supermarket shan ice cream ba saboda bashida lokacin da zai kaiki balle kuyi soyayya sai kikai kanki ki zauna kisha iska kiyi hotuna kema kiga gari haba kawata kina matukar bani mamaki"...ajiyar zuciya jiddah ta sauke,tayi shiru tana tunani tabbas maganganun da ramlah ta fada gaskiya ne amma idan taje shan ice cream bazata had'u da maza ba kuwa?....tou idan kin hadu dasu ai sai kinbasu fuska ke kawai kinje kiyi nishadi ne"wata zuciyar ta bata amsa,take tasamu natsuwa da shawarar da zuciyarta ta bata...

  Ruko hannun ramlah tayi "hakika banida kamarki kawata kinkawo shawara sosai hakan zanyi da yawan kallace kallacen nan da nakeyi na films kala kala ai gara in rinka shiga duniyar gizo ance har koyon rayuwar aure akeyi"

"Kwarai dagaske kawata"ramlah tayi maganar cike da gamsuwa.....

********
  Gab da kiran magriba ramlah ta fito rike da hannun jiddah wadda ta fito raka ta,hangosa yasa bugun zucuyar ramlah ya tsananta adduarta Allah yasa ko allah ya kiyaye hanya yayi mata taji muryarsa kafin ta tafi amma da alama waya yakeyi har suka karaso dabbb dashi zasu wuce...jiddah ta ruke hannunta alamar su tsaya,"naga sweet na waya bari kuyi sallama ko?"

  "Kikasan lokacin da zai gama wayar?kibari kawai ma hadu next time"...

   Shi kuwa waya ya cigaba da yi "haba man kaiko abun kunya ace tunda nayi aure shekara daya har yanzun baka zo gidana ba yanzun kacemun zakazo amma kana fad'amun kila wa kala meye haka zanyi fushi kuma itama zatayi fushi zan zugata dik ranar da kazo taki baka ko ruwa"....kallon side din dasu jiddah suke yayi ya sakar mata wani murmushi da wani irin kallo mai narkar da zuciya, tsuke fuska jiddah tayi dikda yadda kallon ya saukar mata da kasala amma haushinsa tajeji,ita kuwa ramlah tamkar ta saki fitsari taji saboda yadda kallon ya tafi da tunaninta jijiyoyin jikinta dik suka saki.....washe baki yayi hakoransa suka bayyana kafin daga bisani ya kashe wayar "dama yana dariya?"ramlah ke tambayar kanta,maganar jiddah ta katse ta "sweet ramlah tazo har zata tafi ko gaisawa bakuyi ba balle kace mata wani abu to zata wuce"...

AUREN FARI....Where stories live. Discover now