*💥💥AUREN FARI...💥💥*
*SLIMZY✍🏼*
_Wattpad@slimzy33_*SADAUKAR WA:*
*HAUWAU MU'AZU AMIR RUMA...*INA MASOYANA📢📢📢 MASOYA LITTAFIN *AUREN* *FARI* GA RANARKU DON NUNAMIN TSANTSAR KAUNA, KUYI RUGUNTSIMI MU HADU A LITTAFIN *RAMIN MUGUNTA.....* AKAN FARASHI MAI SAUKI 200 KACAL YANZUN HAKA *RAMIN* *MUGUNTA* YA FITA....HADE SUKE DA *RAMUWAR* *GAYYA* DAGA MARUBUCIYAR ZAMANI FEEDHOM....MASU BUKATAR SIYEN TAGWAYE BIYU ZASU BIYA 300
TA WANAN ACCOUNT DIN
👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
2255398727
Zenith Bank
Amina jibril
Shedar biya tun tunbi wanan number 07042277401*38*
Ruko hannun jiddah yayi tana biye dashi suka shiga ciki,bin ko ina da kallo takeyi gabanta na cigaba da faduwa ji takeyi kamar ana buga mata guduma a kirji haka suka kutsa kai babban parlorn gidan a tare,
Suna zaune parlor kamar anyi mutuwa suna breakfast suka shigo da sallama,kallon kallo akeyi momy ce kebin su da kallo cike da mamaki kwayar idanuwanta k'arara ya bayyana tsantsar mamaki kallon Abdallah takeyi tayi shiru,shi kansa kunya da nauyin momy yasa ya tsugunna "momy ina kwana,barka da safiya antashi lafiya?"
Kallo zuhura kebin su dashi ta mike ta nufi dakin da bilal yake momy ta tsaidata "daka ta dawo ki zauna"
Dakyar jiddah ta hadiyi wani miyau mai kaurin gaske sanan tace cikin sarkewar murya "momy ina kwana"
"Lafiya lau surukata ku shigo nan mana Abdallah ya ka tsaya a nan kana d'ari d'ari kamar ba gidanku ba"mikewa yayi ya karasa ya nemi waje ya zauna jiddah ta zauna,
"Ga dakin da yake ciki can bema ko ci abincu ba muma saboda bamu samu bacci jiya ba yasa muka dan natsu muke breakfast"
Kallon jiddah Abdallah yayi "tashi muje ciki"da sauri ta kallesa ya gyada mata kai babu karsashi ta mike haka kawai gabanta ya tsananta faduwa....
Kwance yake yana kallon kofa a zahiri amma a bad'ini ba kofar yake kallo ba yayi nisa cikin duniyar tunani suka turo kofa a tare suka shigo,
Kallom kallo suke tsaye sukayi batare da sun karaso inda yake ba,kafin kace me jiddah ta saka kuka tana kallon bilal ta juya da nufin fita Abdallah ya ruko hannunta yana takowa har gaban gadonsu,
Dakyar bilal ya motsa baki yace cikin jin ciwo "ina ganin mutane biyu a gabana a zahiri amma nasan ba gaskiya bane mafarki ne"
Kuka Abdallah ya fashe dashi"ba mafarki kakeyi ba man,nine Abdallah ne nine nida jiddah mukazo bilal.....haba man ka tashi kadaina ciwo kaji ka warke ka taimakeni matukar kanaso in sakar maka jiddah zanyi maka sadaukarwa"ya karasa ya dago Bilal cikin zafin nama ya rungumesa duka su biyun hawaye sukeyi,
Momy ce ta turo kofar ganinsu cikin wanan yanayin yasa ta tsaya daga kofa tana kallonsu tana murmushi...hawaye na sauka a kwayar idanuwanta..."babu wanda ya isa ya raba hanta da jini,bilal kaida Abdallah sai allah...."tasa gefen rigarta ta share kwallar sake zubowa a idonta,
Abdallah d'ago fuskar bilal yayi tayi jajir bakinsa yayi jajir dik ya fashe"am soo sorry friend nine nasaka ka cikin wanan halin ba kowa ba sanadiyyata kuka fada halin da kuka fada man...kayafe mun ina kaunarka a matsayin d'an uwana kaidin jinin jikina ne"yana maganar jikinsa yana rawa,
Dakyar bilal ya motsa ya d'ago hannunsa da babu alamar karfi ya shiga sharewa Abdallah kwallar dake zubowa a idanuwansa "is ok...i will be fine man"ya gyada masa kai suka kara rungume juna....
Tafa hannu jiddah takeyi a tsaye kuka take tausayinsu ne ya kamata jikinta har rawa yakeyi wani iri takeji a jikinta... tsigar jikinta ke tashi saboda yanayin data gansu ciki,
YOU ARE READING
AUREN FARI....
General Fictionwayace miki ana bawa namiji dama?babu abinda yake canja namiji sai ikon allah idan kince zaki iya canja Abdallah to kin yaudari kanki mazaasu hali irin na Abdallah wadanda basu da lokacin matansu saina aikinsu daban suke basa taba canjawa don haka k...