4

872 67 0
                                    

💥 *💥AUREN F'ARI....* 💥💥

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
*(home of expert and perfect writers)*💡

       *SLIMZY✍🏻*
_Wattpad@slimzy33_

*SADAUKARWA:*
*HAUWA'U MU'AZU AMIR RUMA...*

                    *4*

Zaune take a parlor tana cin dankali soyayye da kwai gefenta cup din tea ne da take kurba minti minti..hannunta rike da wayarta,murmushi ne makale a fuskarta tana karanta sakon bilal....

  Yaye labulen shigowa tayi bakinta dauke da sallama suna hada ido ramlah tayi mata hararar Wasa,"wato baki ma ko shirya ba ko?inata sauri don nasan halinki bakida hakuri ko kadan jiddah amma sainazo na tarar dake zaune kina breakfast"

Murnushi jiddah tayi "kaina bisa wuya....rigima.com karaso mana kin tsaya daga nan kin soma zazzagawa haba tawan"

Karasowa tayi tana bin jiddah da kallo,kayan baccin dake jikinta yasa wani kishi ya yunkuro mata,tabe baki tayi tana kokarin zama tace "wato tun tuni kinata soyayya da Abdallah ko kayan baccin ma baa cireba,gashi ansa riga yar jan raayi"kallon kanta jiddah tayi sanan ta tuntsire da dariya "meye kuma riga yar jan raayi?sabon sunan riga kenan"

Murmushin k'eta ramlah tayi "ehh gashi kinja raayin Abdallah,wayasani ma ko aiki ya kasa zuwa?"

  Zaro ido jiddah tayi "hmmm ashe zaa maimaita yakin biyafara,matukar Abdallah beje aiki ba...tou bari kiji ban tari numfashinki ba jiya saida ya gama tsotsemun baki ya kunnamin network ya sakeni ya haye gado na da sunan yim aiki,niko kinsan halin nawa nan da nan na hau na soma masifa karshe ya fice Niko na janyo wayata na cigaba da chat dina,hmmm bari kiji jiya kadai shawararki taimun amfani don nasha hirata nakai har daya na dare ina abuna yana can yana tsiyarsa....amma kinsan wani abu wallahi hankalina na wajen mijina ina son Abdallah bansan wani irinso nake masa ba"tayi maganar a slow cike da damuwa hawaye ya gangaro mata...

Wani dadi ne ya lullube ramlah bakinta ya kasa rufuwa,abinda takeson ji kenan burinta kawai kada jiddah ta rabi Abdallah da sunan jan raayinsa..."kawata ai nafada miki wallahi zakiji dadin chat zakuma ki hadu da mutane da dama da zasu debe miki kewa"...

  Mikewa jiddah tayi tana fadin "naga amfanin hakan kawata bari in wanke hannu in watsa ruwa ba wani makeup zanyi ba kawai mu kama hanya"...tayi gaba ramlah tabi ta da wani irin kallo da murmushin keta....ta dawo ta wuceta tayi hanyar bedroom

  Ramlah kamar jira taketi ta ciro wayarta a jaka nan da nan tayi dialing number bilal....

  Shirin breakfast yakeyi ganin bega jiddah online ba ya ajiye wayar yaci abinci...sai kiran ramlah ya shigo hannu ya kai ya dauki wayar...murmushi yayi Ramlah manya a tunaninta bansan jiddah ba ..hmmm jiddah ni ya kamata insameta ba Abdallah ba, recieving ya danna ya kara wayar a kunnensa cike da katsaita yace "umm hmmm ina jinki"

  Bata damu da yadda yayi maganar ba "nace yayah bilal ko zakasamemu wajen shan icecream na cikin gari?,inaso kayiwa kawata surprise ta ganka amma banaso tasan nina fada maka ka samemu kaga zaka kara ganinta....ko?wallahi cikin damuwa take ka taimakawa kawata ina matukar sonta".... tunda ta soma maganar ya dire spoon din hannunsa,jimmm yayi yana tunani jin shiru yasa ta daga wayar daga hannunta ta kalla taga tana tafiya ta kara a kunneta "hello ya bilal"

"Ina jinki ramly,bari mugani idan kun isa just tex me"

  Wani farin ciki ne ya lullubeta,tamkar ta taka rawa takeji....

  Shiko yana dire wayar tagumi ya rafka, tunanin yadda zai fuskanceta yakeyi,gashi awwanni da basu wuce ashirin da hudu ba kadai ya saba da ita,ya lura tanada shagwaba tanada son attention....uwa uba tanason hira yadda take replying massage dinsa jiya daddare kadai ke daure masa kai tambayar kansa ya shigayi "ina Abdallah a wanan daren matarsa ke chat"?

AUREN FARI....Where stories live. Discover now