*💥💥AUREN FARI...💥💥*
*SLIMZY✍🏼*
_Wattpad@slimzy33_*SADAUKAR WA:*
*HAUWAU MU'AZU AMIR RUMA...*INA MASOYANA📢📢📢 MASOYA LITTAFIN *AUREN* *FARI* GA RANARKU DON NUNAMIN TSANTSAR KAUNA, KUYI RUGUNTSIMI MU HADU A LITTAFIN *RAMIN MUGUNTA.....* AKAN FARASHI MAI SAUKI 200 KACAL YANZUN HAKA *RAMIN* *MUGUNTA* YA FITA....HADE SUKE DA *RAMUWAR* *GAYYA* DAGA MARUBUCIYAR ZAMANI FEEDHOM....MASU BUKATAR SIYEN TAGWAYE BIYU ZASU BIYA 300
TA WANAN ACCOUNT DIN
👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
2255398727
Zenith Bank
Amina jibril
Shedar biya tun tunbi wanan number 07042277401*36*
A kofar gidan bilal yayi parking ya dubi zainab dake faman satar kallonsa yace "muje ko?"Karkada kai tayi alamar bazata fito daga motar ba ta kauda kanta gefe batare da tayi magana ba,gwauron numfashi ya ja "ki fito daga motar nace ko?kince zakiyi sallama da ita ko?"
"Ehh idan ta fito kun gama sai infito mugaisa"...daura fuska yayi yana mata wani kallo "kina batamun lokaci ki fito nace"ya juya ya bude motar ,tura baki tayi ta bude motar ta fito ta rufe ta jingina hade da harde hannuwanta biyu tana jifnsa da wani kallo yana rike da wayarsa,
Tsaki yaja "ina neman wayarta ma Bata shiga,ko batada carji ne?...gashi kuma unguwar ko ina da wuta"ya karasa maganar a slow,
Kallon zainab yayi a fakaice ya dan daura fuska kadan "ko zaki shiga kiyi mata magana munzo?"Kafin ta bashi amsa Yaya ibrahim ya karyo kwana yana waya da alama daga wani waje yake amma baa mota ba,...yana hada ido da bilal yaji tsammm wani iri cikin jikinsa gashi Bilal din ya rigada ya gansa,hakan yasa ya dakata ganin bilal din ya tahi,mikawa ya ibrahim hannu yayi cike da ladabi "assalamu alaikum...yaya ibrahim barka da warhaka ina yini"
"Barka dai,lafiya lau alhamdulillahi ,ya mutanen gidan?"
"Lafiya lau"ya amsa yana sosa keya ganin ya ibrahim ya tsaya yana kallonsa "amm yaya tun dazun nazo bana samun wayar jiddah inata kiranta"
Shiru yaya ibrahim yayi yana kallon bilal kusan second ashirin,bilak dago Kai yayi yana kara duban yaya ibrahim,ganin kallon da yakeyi masa yasa gabansa ya fadi cike da rudani bakinsa na rawa yace "yayah...lafiya dai ko?kowani abu ya samu jiddar ne?"ya jehowa yaya ibrahim tambaya a jere,
Gyaran murya yayi "ammm...bilal gaskiya dai tsakani da allah zan fada maka banso sanar da kai ba amma zan sanar da kai yanzun Allah yasa ka fahimceni,ka fahimcemu Baki daya"
Wata irin faduwar gaba da tsoro ne suka cikasa suka bayyana karara a fuskarsa, Allah yasa jiddah ba mutuwa tayi ba,adduar da ta fado masa kenan be kawo komiba ya daure yace "yaya meya faru ne?ka sanar dani kada ka boyemun"Jimm kadan ya Ibrahim yayi yana jinjina kalmar abakinsa kafim yace ",tou....jiddah da mahaifin mu ya daura mata aure batare da shawara da ita ba,maana dai ta koma gidan mijinta",
Wata irin walkiya ce ta gifta a idon bilal take yaga duhu ya kewayesa jiri ne ke dibarsa yana neman faduwa kasa ya ibrahim ya rukosa yana kiran sunan sa "bilal... Bilal ka dawo hayyacinka kada ka fadi wani mummunan abu ya sameka a wajen nan"rukon da yayi masa yasa ya tsaya amma dikda haka kafafuwansa rawa sukeyi masa karrr karrr karrr yakai hannunsa ya dafe kansa da yaji kamar ansara masa adda a tsakiyar kai...da kyar ya motsa bakimsa batare da kaji abinda yace ba ya furta "innahlillahi wa innah ilaihi rajiun allahumma ajjirni fi musibati waklufni khairan minha"....dakyar yake hada kalmomin a harshensa da yayi masa nauyi,zuciyarsa kuwa bugun da takeyi kadai zai baka tsoro da tashin hakali shi kansa yaya ibrahim saida ya tsorata cikin rawar jiki ya kira zainab daje tsaye tana hangosu ta taho cikim sauri,
Kallom bilal take tana zaro ido "yaya bee....yaya meya sameka meyafaru?mekayi masa"ta kalli ibrahim tanayi masa tambaya,
Ya ibrahim kasa amsa mata yayi sai cewa yayi "kin iya mota?"ya tambayeta jikinsa na rawa,
YOU ARE READING
AUREN FARI....
General Fictionwayace miki ana bawa namiji dama?babu abinda yake canja namiji sai ikon allah idan kince zaki iya canja Abdallah to kin yaudari kanki mazaasu hali irin na Abdallah wadanda basu da lokacin matansu saina aikinsu daban suke basa taba canjawa don haka k...