34

774 75 13
                                    

*💥💥AUREN FARI...💥💥*

               *SLIMZY✍🏼*
          _Wattpad@slimzy33_

*SADAUKAR WA:*
*HAUWAU MU'AZU AMIR RUMA...*

                      *34*

Bilal ne ke kiran nata a waya cikin sauri ta dau wayar ta dauka cikin wani irin yanayi murya a sanyaye,"hello Iqbal"

"Hello habeebty,gani a kofar gida mun iso"ya datse wayar,tabi wayar da kallo haka kawai ta tsinci kanta cikin matsananciyar faduwar gaba, ta dade tsaye sanan ta juya ta tsaya gaban dressing mirror tana kallon kanta,yau kadai tadan rame ta fada hoda ta dauka ta kara shafawa ta gyara fuskarta sosai ta dauki sirrin kwalliyarta, wato kwalli ta zizara a kyawawan idanuwanta wadanda suka kara kyau ita kanta kallon yadda idanuwanta sukai kyau takeyi,tabbas maman afee takwararta tayi gaskiya da tace sirrin kwalliyar mace shine kwalli ko baki kwalliya ba kika shafa kwalli a idonki zaki fito ras kamar yadda ake cewa idan babu gishiri a miya babu miya to haka kwalliya take tafiya da kwalli,babu mamaki abbahn afee kullim yake kara sonta....juyawa tayi ta bude drawer ta zari gyalenta baki ta rufe jikinta ta feshe jikinta da turare ta fito,yadda take tafiyar kadai zakasan jiddah batada karsashi,

"Saina dawo ummah,bilal ne yazo, Dan Allah idan bakon abbah ya fito ki sanarwa da abbah bukatar bilal nason ganin nasa inyaso inya bukaci shigowa sai inzo inji ko kunyi maganar"

Jinjina Mata kai ummah tayi Tana kallom jiddah cike da tausayawa "insha allahu zan sanar masa sai ki shigo da bilal din"

  "Tou ummah sai na dawo"ta juya ta fice

Ummah ta kada kai "Allah sarki,jiddah tana bani tausayi Allah yayi miki zabin alheri ya cika miki burinki"ummah tace a fili,

Su abidah suka hada baki"Ameen"

A waje kuwa jiddah tun kafin ta karaso su zuhura suka taryeta dikda yaune rana ta farko da suka soma ganinta,cike da faraa ta rungumesu kamar tasan su "Antyn mu barka da fitowa tun tuni muke waje mun kosa ki fito muganki yaya bee kullum cikin kodaki yake"

Fadada faraarta tayi ta juya ga bilak cikin wasa tai masa wata yar harara mai cike da kissa da soyayya wadda saida yaji numfashinsa kamar zai dauke don ba karamin kyau tayi ba "wato zama kakeyi kana tsara kannena ko?gashi sunzo basuga hakan ba dan ni ban wani hadu ba"

"Injiwa anty?wallahi kin hadu kamar balarabiya,da ace da rana mukazo ma bazamu tafi ba sai munyi hoto dake"zuhur da rufaida suka hada baki,

Itadai jiddah kada kai kawai tayi cike da farin ciki sai lokacin ta dubi sashen da zainab ke tsaye gefen bilal na hagu ta kafeta da ido,zaro ido zainab tayi "ahhhhh mutuniyas afuwan ashe tare dake ake wayyooo my sweet aminiya zo muyi oyoyo mana"tana kokarin karasawa wajenta,

Juya baya zainab tayi cikin sigar wasa take daga hannu "ni kyaleni bayan kin mance dani kin shareni ni ai nayi fushi"

Murmushi jiddah tayi ta hade hannayenta "am soo sorry my dearest sister nayi laifi na tuba bari insa gwiwata a kasa"jiddah ta Shiga kokarin gurfanawa da sauri bilal ya dakatar da ita "ah ah ta hakura ai kanwata ce na ari bakinta naci mata albasa zo muje habeebty akwai maganar da zamuyi"

Kiftawa zee ido bilal yayi tai dariyar karfin hali "wato nasa masoyiyarka wahala ka maza kace ka amshi laifin hmmm laila majnun aje ayi soyayya "

Can gefe suka tsaya da Bilal ya tsareta da ido cikin wani yanayi mai cike da shaukin soyayya yake jifanta da wanan kallon,hakan yasa tadan zumburo baki cike da shagwaba kamar wata baby "iqbal...ni ka dainamun wanan kallon idan kanamun inajin wani abu fa?"

Kashe mata ido yayi "sure?kina loosing control ne?soyayya ce habeebty,...well amma yanayin naki gaba daya is not normal ba yadda kike kamar koda yaushe ba akwai wani abu ne?"

AUREN FARI....Место, где живут истории. Откройте их для себя